Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

Yar Sadaka Book One Complete Hausa Novel 1,276 words 0 views Progress saved
Download Book

Zama da ita a gida daya ba Dan haka ka zabamata inda ya dace Kuma a yanzu nakeso ka saketa saki uku. Mummy kiyi hakuri tinda bazaki Bata gurin Zama ba nizan zauna da ita a dakina,,batin saki Kuma kiyi hakuri Baz... Lafiyayyun Mari Har guda uku Yaya ya safkewa mashkur Yana nunashi da yatsa,,kayi kadan ka wulaqanta mana uwa,,wallahi sedai kabar gidannan.. Beyi Magana ba ya kama hannun nijlah dake kuka tana Kiran Sunan kaka ya Shiga dakinsa da ita,,a qasa nijlah ta zube tana birgima tana ihu,,shiko bakin gado ya zauna ya dafe kansa Yana Jin Wani irin faduwar gaba.. Cikin kuka lateefah tace,yanzu haka zamu zuba ido mashkur yayi yadda yakeso,, ba Wanda yabata amsa.. Nan mummy ta dauka waya ta Kira daddy tana kuka,tace Alhaji ka dawo gida yanzu,,tana gama fada ta katse Kiran Bata jira amsar Shiba.. Wani layin ta Kira ta miqa lateefah wayar.. Yasmeen dake kwance Kan cinyar mama tana game a waya taga Kiran mummy,,kallan mama tayi jikin Jin Kunya tace,,mama mummyn mashkur ce. Ki Daga mana cewan mama tana kasa kunne,,Yasmeen Na dauka lateefah tace .. Sunana lateefah yayar mashkur,,mummy nasan ganinki yanzu.... Wash,, typing da wahala,,mu hadu a page na gaba.. Karku manta da share. *Momn sultan ce*✍✍✍ 💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘 *STORY & WRITING BY...* *BY* *MOMN SULTAN* *DEDICATED TO.....* *MMN AMATULLAH* *SPECIAL GIFT TO...* *MOMN ANSAR* 1⃣9⃣&2⃣0⃣ Mummy kuma,,ke Yasmeen dama kina waya da mahaifiyar yaran nan" gizgiza Kai Yasmeen tayi tana kallan mama data kafeta da ido,,amsa zaki Bani,kinfi kowa Sanin bagane wannan yaran naki nake ba.. Cikin yauqi da yanga Yasmeen tace,,Allah mama bamu waya da ita" Ok!saiki gayamin ta ina mahaifiyar sa ta dauka number ki?? Mama sau dayane mashkur ya kirani da layinta shine nayi saving,,cike da rashin gamsuwa mama tace,,idan bakwa waya da ita yaya za'ayi ta kiraki??? Mama ba ita bane yayanshine,,sunanta aunty lateefah sedai da wayan mummyn ta Kira kuma tace wai mummy nasan ganina.. Mezaki Mata??? Eyyah mama Nima bansani ba,, Yasmeen ta fada tana turo Baki.. To babu inda zakije"wannan ai shirmene ki dauki qafa kije har gidansu saurayi kina magana da mahaifiyar sa,,mama Allah bantaba zuwa ba sedai jikina Yana Bani kamar akwai matsala.. Wanne irin matsala kinga Yasmeen kidena kawo tinani marasa kyau a cikin zuciyanki... Mama ba haka bane,,wallahi tin jiya gabana yake faduwa ki abinci ban iya Ciba,,gashi sai Kiran mashkur nake wayanshi kashe,,kuma Shi be Kira ba,,gashi yanzu aunty lateefah ta Kira mummy na nemana,,kinga ko da wani abu. Babu komai Insha Allahu,,karyar da murya Yasmeen tayi tana hawaye tace,,mama Dan Allah kibani dama naje wallahi bazan zauna ba.. Hmmm Yasmeen ina jiyemiki Abu Amma ke Baki gani,,akullum ina gayamiki ki rage wannan soyayyar da kikewa mashkur,,namiji fa mijin mace hudu ne.. Bata fuska Yasmeen tayi tana kallan gefe tace,,,mama kullum gadanki Baya wuci Kan mashkur,,ba aibu bane Danna nuna kulawa da tsananin soyayya gareshi,,mama mashkur Yana Sona har inaga kama Sanda yakemin ya zarta nawa"" duk da haka ki rage nidai ina gayamiki.. To mama Dan Allah naje??? Ajiyar zuciya mama ta safke tana kallan yadda Yasmeen ta narke Mata kama ance wani Abu ya Samu mashkur tace,, shikenan kije Amma sainayi waya dashi mashkur din naji daga bakinsa yakuma hadani da maman nashi.. Mama kenan,,haba mama na saikace Baki yadda da tarbiyyana ba,,mama kinsani mashkur Baya gari kuma wallahi number mamansane barima nakira saikiji da bakinki.. Number mummy Yasmeen ta Kira sedai wayan akashe Dan haka mama tace babu inda zata fita,,kuka Yasmeen tasa tana Jin wani irin yanayi a dukkan jikinta,,jitake kama qirjinta ze fashe zuciyarta ta fito gaba daya Kota huta da abinda takeji,,koya ta motsa Kota Tina sunan mashkur sai taji kama andora Mata dutse aka,,duk yadda taso hakura takasa haka tasa mama agaba tana kuka.. Yasmeen meyasa kikesan dagamin hankali,,ba Duka ba zagi amma kinsani gaba kina kuka saikace qaramar yarinya.. Mama kibari naje ko hankalina ze kwanta,,wallahi mama akwai matsala,,bantabajin irin wannan yanayin ba sai jiya zuwa yanzu,,Insha Allahu bazan wuci 1 hour ba Zan dawo.. Shikenan Yasmeen tinda haka kikeso saikije daki sani gaba kina wannan kukan ko kunya baji.. Share hawaye Yasmeen tayi tana murmushi tace,, nagode mama.. Mama bata iya bata amsa ba Sai binta da kallo tayi tana mamakin yadda Yasmeen ke nuna damuwanta agaban kowa.. Dago jajayen idanunsa yayi ya zubamata ido Yana kallan yadda take kuka tana Kiran kaka,,wani irin juyawa kanshi yake sabida halin dayake ciki ga kuka dake taba masa zuciya,,ahankali ya riqa Kiran sunanta.. Nijlah. nijlah. Nijlah.. Bata amsaba Saima qarawa kukanta sauti tayi,, ya rasa yadda zeyi da ita,,nan ya miqa hannu Yana Magana da shaqanqiyar murya,,zomana amaryar mashkur,,maqale kafata nijlah tayi ta kuma juya masa baya tana turo baki,,duk da haka ranshi be baci ba ya cigaba da kiranta Yana rarrashinta,,amma duk da haka bata iya shiru da bakinta.. Shiru yayi yana kallanta tare da tinanin ta inda zefara rarrashinta. Ahankali ya tashi Yana tafiya isa inda take kwance,,kafin ya qarasa nijlah tafara birgima tana juyi a qasa.. Haushine ya kamashi Dan haka ya daka Mata tsawa Wanda tasa hantar cikin nijlah kadawa nan take jikinta yafara karkarwa ta fada jikinsa tana safke ajiyar zuciya.. Rungumeta yayi a karo Na farko Yana shafa bayanta"kukan ya isa haka,,ko kinajin yinwa,,daga masa kai tayi tana qara shigewa jikinsa.. Labensa na qasa ya cije Yana tinanin yadda ze bullowa labarin,,sedai yayi alqawarin baze taba rabuwa da nijlah ba,sabida nijlah amanar Allah ce agurinshi... Ahankali ya Tashi da ita a jikinshi ya zauna gafen bed Yana qaremata kallo,,qara shigemasa tayi sabida karkarwa da jikinta ya dauka.. Kinaso nazaneki,,saurin girgiza masa kai tayi,,bakinta na rawa tace Dan Allah kayi hakuri.. Zan hakura amma saikin dena wannan birgiman da kike,,koni bakiga halin da nake ciki ba??? Shiru tayi,shiko ya cigaba da Magana,, nijlah indai baso kike zuciyana ta buga ba,toki dena irin wannan kukan Kina birgima a qasa saikace yarinya,,dagowa tayi tana kallansa shiko ya dage Mata gira,,wai ko bakisan kin girmaba??. Nan ma shiru tayi saida taji ya janye jikinsa anata yana qoqarin Tashi tace.. Kado yinwa nakeji" Kobata fada ba yasan dole zataji yinwa duba da rabanta da abinci nan yayi murmushi yace jeki falo ki gaya mummy.. Bakinta na karkarwa tace,,Nina qoshi" Yana niyyan Magana yaji ana buga kofan dakin,,beyi Magana ba yayi shiru Yana sauraran bugun.. Mashkur wai bakajina ina tsaye tin dazu baka bude ba" menene ya fada a hankali" mashkur ni kake tambaya menene?? Cike da qosawa yace,,haba aunty lateefah,,wai me kike nema dani,,Nabar Miki falo nan ma saikin biyoni.. Toka fito mummy na kiranka.. Ina zuwa yabata amsa a ciki,, juyawa aunty lateefah tayi tana tafiya tana tinanin abinda ya chanza mashkur yaran da ko Magana bata dameshiba.. Mummy yace Yana zuwa.. Tinda Yasmeen ta hau titi take gudu kama zata Tashi sama,,ba ita ta rahe gudun motan ba har saida ta shigo layin gidansu mashkur,,Yana zuwa tayi horn get man ya bude mata,,bata iya daidaita parking ba ta fito tana sauri zuciyanta da halbawa da sauri da sauri harta isa kofan falon,,a bude yake Dan haka tayi sallama tana jiran a amsa Mata" Yaya ne ya iya amsawa Yana kallan kofan,,a hankali Yasmeen ta shiga falon kanta a qasa tana mejin kunya.. Qasan kafet ta

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46