Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Yar Sadaka Book One Complete Hausa Novel 1,262 words 0 views Progress saved
Download Book

mashkur ba yaro bane Duk inda yake Ze Iya Kula da kansa,,Kuma shikenan seya tafi cikin matsiyata masu yawo a Jeje wadanda Basu da Wani abinci Sai nono,, wallahi Bazan lamuntaba koya dawo Ko hankalin kowa ya Tashi a gidannan.. Kiyi hakuri Mummy nasan Duk inda mashkur yake Yana hanya"Koda yazo Baze shigomin gida ba Sai an kaishi hospital an Duba lafiyarsa,,nasan zuwa yanzu yaci abubuwa marasa kyau da zasu Iya taba lafiyarsa,,Kuma inaso kufara kaishi toilet Na Baya yayi wankan kafin ya shigomin Daki... Shikenan mummy za'ayi yadda kikace,,Abu daya nakeso ki kwantar da Hankalinki,,haba lateefa tayaya hankali Ze kwanta Ina zaune cikin Jin Dadi auta Yana cikin wahala kinga lateefa Idan Baze zoba kuje ku daukomin Shi Dan wallahi Na tsani Zama da wadannan mutanan,,shiyasa kikaga Ko nono Bana sha.. Ajiyar zuciya lateefah ta safke tana kallan mummy tana girgiza kai tace,,Dan Allah mummy ki rage wannan damuwan kinsani Idan daddy yaji Baze tabajin Dadi ba,,cike da fada mummy tace. To yaji man Idan yaji saime dukana zeyi,,Koshi yayi irin wannan rayuwar ne,,Amma mummy Amma me Dan ubanki,,karfa ki batamin Rai. Kiyi hakuri Mummy Naga Dai daddy Shima bafulatani ne,,kidena nuna kyamarsu a Fili Hakan Ze riqa sosamasa Rai.. Badai kema kina Bayan wadannan mutanan ba mutanan da saisu shekara Goma basuci Nama ba,,mummy kinsan nafiki tsanar Zama a irin wannan guri kawai Dai banaso kina fada agaban daddy.. Sallama Yaya yayi suka amsa nan ya Samu guri kusa da mummy ya zauna Yana gaisheta,,dauke kai mummy tayi taqi amsawa dan a ganinta basuyiwa mashkur Magana ba shiyasa be dawo ba.. Lateefah ce tayiwa Yaya sannu da zuwa nan ya amsa Yana cewa Ina mashkur yake? Yaya be dawo ba Nima tinda nazo nake zuba idansa gashi Har 4 Na yamma be qaraso ba,,Anya Ko ya taho? Eh Yana hanya dazu munyi Magana dashi yace nan da 2 hours ze Iya qarasowa.. lateefah meya Samu mummy Ko Bata da lafiya? Bansani ba,,kaida Nace kagayamasa ya dawo da wuri shine harka samu damar zuwa shibe qarasoba,,kiyi hakuri Mummy kinsan yanayin haryarsu Sai ya hau Mota biyu kafin su zo,,Nace driver zeyi daukansa yace harya kama hanya" karyane wallahi kunsan Allah Idan be dawo Yau ba Saina Saba muku a cikin gidannan.. Tinda daddy ya shigo yafara Jin hayaniya harya shigo falo ya Samesu zaune sun sa mummy tsakiya Suna Bata hakuri.. Daya Bayan daya ya riqa kallansu Yana mamakin zuwansu,,sannu da zuwa sukayi masa ya amsa tare da neman guri ya zauna Yana Kallan mummy yace.. Yanzu abinda kikeyi ya dace Kenan agaban yaranki kina zauna kina koya musu dabi'a mara kyau ta rashin sanin darajar Dan Adam,,to Wallahi kisani kowa da Kika gani da baiwar da Allah yayi masa dan haka kibi Duniya a sannu" turo baki mummy tayi ta budeshi a hankali tace,,to Ni menayi kawai Dan Nace yarona ya dawo gareni Sai ka kama fada kana fishi Dani" Ki rufemin baki,,kosu Fulanin ba Allah ya haliccesu ba,kinsan bakisan Fulani Kika auri jininsu,,Maryam a gidana Kika Zama abinda Kika Zama shine yanzu Har Kika Iya ....." Daddy kayi hakuri Kasan halin mummy tinba yanzu ba,,kasani Ko kauyensu Inna wuro batasan zuwa Har Allah yamata rasuwa,,daddy Mun girma hadda yara bazamu so ganin haka Yana faruwa a tsakaninka da mummy ba,,munsani daddy kaima ka Sani,,baku taba yin fada da mummy Sai a Kan maganar zuwa ruga lokaci gudu kaika Kadena zuwa daganan bamu sake ganin bacin ranku ba Sai yanzu da mashkur Yaja.. Kallan yaya daddy yayi yace meya dawo dakai kasar nan yanzu,,bakinsa Na rawa yace daddy Wani aiki nazo Yi,,Ke Kuma fa daddy yafada Yana nuna lateefah da cikinta ya duru ruwa harta fara karkarwa.. Ba tambayanki nayi ba,,Ina Kika Baro mijinki? Nina kirata,,Shima Sadiq Nina kirashi tinda kai bazaka Sashi ya dawo gidaba su zasu Sashi yadawo,,to ai shikenan Idan ya dawo saiki jiqashi ki yanshe Ko,,be jira amsar mummy ba ya fita a falon.. Hira suka cigaba dayi ita Dai mummy jinsu kawai take tana Kalle kalle tare da.neman ta hanyar da mashkur Ze shigo,,Har akafara Kiran Sallar magrib Basu qaraso ba haka Dai kowanne su ya daura alwala sukayi sallah,,Suna cigaba da Zaman jiransa... Tinda nijlah Taji warin Mai zuciyanta yafara Tashi nan ta fara toshe hanci tana kallan mashkur,,a hankali yake Mata Magana Yana Kallan yadda idanunta sukayi zuru zuru,, Menene Naga kina toshe baki da hanci,, Banasan warin Mai ka saukeni cikina juyawa yake tafada tana yinqurin Amai,,kafin motan ta tsaya tafara Kwara Amai a jikin mashkur Har Saida ta Bata gaban rigarsa,,be damu da Hakan ba Saima shafa bayanta ya riqayi Yana Mata sannu,,Seda ta gama me motan ya Basu ruwa a jarka suka wanke jikinsu,,nan suka cigaba da tafiya hancinta a toshe ,,karfe 7 Na dare Suka sauka a cikin garin Kano,,me napep ya tare suka Shiga nan yayi masa kwantancen gidansu kasancewar mashkur be taba Hawa nape ba,,dariya me nape yayi Yana cewa Malam haka kai bakone,,mu ba address Ake bamu ba,unguwa kawai Zaka fada Idan mukaje saika nuna gidanka,,ok kawia mashkur yace yacigaba da jera nijlah sannu,,tinda suka Hau napep bacci ya dauketa Har suka kai gidansu mashkur Bata Sani ba. Bayan ya sallami me napep ya tsaya tinanin ta yadda zefara tashinta Sai kawai ya dauketa ya kwankwasa get.. Waye ne Ze balle mana kofa qara bugawa mashkur yayi Yana cewa nine baba zoka Bude.. DA gudu baba me Gadi ya Bude kofan Yana yiwa mashkur sannu da zuwa.. Ahankali mashkur yace,,baba ga kayana Dan Allah ka temaka ashigomin dasu,,to ranka ya Dade,,nan baba yafara rufe qofan,,qaran qofa yasa nijlah Bude Ido tana Kalle kalle.. Ahankali mashkur ya safketa Yana jera Mata sannu,,Ina kayana nijlah tafada cike da sanyin kuka. Kingansu can Karki faramin halin naki,,dasauri ta dauko kullin dankwalinta ta Dora akai tana Kalle kallen gidan.. Hannunta ya kama Yana cewa 'yar kauye Sai Wani Kalle kalle kike,,lah kado kaga wannan abun da Ake nunawa,,lah kado Kalli kaza haka nijlah ta riqa fada Har suka isa qofan falon.. Da sallama mashkur ya Shiga zuciyarsa na harbawa tare da matsanancin faduwar gaba.. Mummy dake zaune tasa abinci agaba Taji sallamar mashkur,,dasauri ta dago ido Aiko tayi sa'a idanta be safka Kan Na mashkur ba saiya sauka Akan santaleliyar surukarta.. Zabura tayi ta Tashi tana nuna nijlah da yatsa bakinta yakasa magana... Aunty lateefah ce tayi qoqarin Bude baki tace mashkur Kaine haka,,ita Kuma wannan Daga ina,,Ina Zaka kaita.. Mashkur be Iya Magana ba illah zuba musu shanyenyun idanunsa dayayi Yana cigaba da tafiya,,,har Saida yakai jikin kujera Ze zauna hannunsa riqe Dana nijlah yaji muryar mummy tana Magana.. Karka fara Zama min Kan kujera ka Kuma ficemin da wannan aljanar yarinyar"waima a gidan ubanwa ka samota Sai kuma tasa kuka tana cewa. Kunga irin jajibe jajiben nasa,,ya kamomin wannan qazantar Har gida... Mashkur wacece wannan Daga ina ka daukota?? Kafin mashkur yayi Magana yaji tsincin muryar nijlah.. Sunana nijlah kawu Daga garin kankan ya daukoni Kuma ni matarsace Ko kado????????????????????? *Kuyi hakuri wayana ya Samu matsala ba lallai ku qara Jina a 'yan kwanakinan ba,,sedai kuyi fatan Allah yasa ta gyaru da wuri,,Nima ba haka naso ba,,zanyi missig zafafan comments dinku😍😍😍* *Comments & share* *momn sultan ce*✍✍✍ πŸ’˜πŸ’˜ *'YAR SADAKA..*πŸ’˜πŸ’˜ *STORY & WRITING BY...* *BY* *MOMN

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46