Skip to content

Chapter 19

Chapter 19

Yar Sadaka Book One Complete Hausa Novel 1,279 words 0 views Progress saved
Download Book

Bazan qaraba,,tureta yayi ya Tashi a hankali Yana Kallan jikinsa,,rintse idonsa yayi Yana me Jin takaicin abinda nijlah ta aikata masa.. Yanzu yaya zanyi? Ta Ina zanfara gyara jikina Dana wannan yarinyar,,Babu shakka Na Hada kaina da aiki indai irin haka ta cigaba da faruwa.. Tinda nijlah taga ya Tashi itama tafara qoqarin Tashi tsaye tana toshe hanci,,kallanta yayi yayi kwafa Yana cewa,,Idan baki cire hannunki a hanci ba Saina wanke Miki fuska da wannan kashin koba Ke kikayi ba,,Zaki Wani rufe hanci kama kama wanine yayi Miki.. Badan tasoba ya cire hannun sedai takasa hadiye saliva,,Yana Shiga toilet tayi saurin binshi,,harya Shiga ya leqo Yana Mata Magana da Ido,,tini ta gane abinda yake nufi Dan haka ta tsaya tsaye Akan gadon tana kuka.. Air freshener ya dauko yafara feshe Dakin dashi Yana sakin tsaki Akai Akai,,Seda yaji tsamin ya ragu kafin ya dawo Kan gadon.. Daga tsaye yafara cire kayan jikinsa,, nijlah Na ganin Ze zare wandansa tayi saurin rufe Ido tana juya masa Baya.. Babban wandansa ya cire ya rage daga Shi Sai Dan qarami Yana kallanta.. Tana Daga tsaye yace,,kicire wannan wandan kafin nayi boll dake,,kazama kawai,,Ni wallahi tinda nake bantaba aiki cikin dare ba Sai akanki,,Yoko jaririya nadauko Sai haka.. Kukanta ta qara volume shiko yayi shiru Yana sauraranta. Zuwa can dabata ta fado masa ganin Bata da niyyar cire kayan yace,, shikenan nizan wuci Dayan Dakin Kinga saiki kwana cikin doyi,,da anjima kare yazo ya cinyeki.. Wayyo Allah kaka dan birni ze,,kifa denamin ihu Ko bakisan da makoftaba,,salan suyi tunanin satoki nayi"' uhmn uhmn Toni ka ciremin kayan Allah Bazan Iya tabawa ba.. Mamakine ya kamashi ganin yadda ta zage tana kuka takuma Qi taba jikinta ita a dole kyankyami takeji.. Babu yadda ya Iya haka yasa hannu ya cire Mata wandan,nan ya ajiye Kan gadon yasa hannu yajanyota jikinshi nan yafara cire Mata riga,,Yana gamawa ya safketa kasa Shima ya safko,,Gana daya ya tattare bedsheet din da kayan jikinsu ya dauko katuwan Leda yasa ciki,,nan ya Cilla cikin Shara Yana kallan yadda tafara karkarwa sabida sanyi.. Toilet ya Shiga ya Hada ruwa me zafi ya dawo ya dauketa,,cikin ruwan yasata yayimata wanka sosai,,Bayan ya gama Mata ya Bata towel ta daura,,Zaki Iya jirana a waje Nima nayi wankan,, girgiza masa kai tayi tana turo baki.. Banace kidena turomin baki ba,,koso kike Na zuba Miki Ido kinayin abinda kikaga Dama,,a hankali nijlah tace ah ah kayi hakuri.. Bude Mata kofa yayi yace ki zauna anan yanzu Zan fito ba dadewa zanyi b,,Yana gama fada ya Koma ciki yabar anan tsaye tana jin tsoro.. Bayan ya fito ya dauketa suka Koma daya dakin,,shida kanshi ya shafeta da Mai Shima ya shafa,,turarensa ya shafa Mata Yana Kallan yadda tayi Shiru kama ba ita ba,,Kan bed ya Koma hannunsa riqe da nata.. Suna kwanciya bacci ya daukesu,,be Iya tashin asuba ba Sai farkawa yayi yaji Har an idar da sallah,,dasauri ya Tashi ya fada toilet yayi brushe,a gaggauce yayi wanka sabida gajiya dake damunsa Bayan ya gama ya dauro alwala ya fito Yana tsane jikinsa da towel,,kallan Nijlah yayi Yana murmushi tare da Kiran sunanta a hankali.. Wardrobe ya bude ya dauko jallabiya,,nan ya shinfida sallaya ya tada Sallah,,Bayan ya isar yayi addua sosai tare da Neman mafita a al'amuransa.. Nan ya dawo kan gadon Yana tashinta,,ke nijlah tashi mana lokacin Sallah na shigewa.. Uhmn uhmn nika bari bacci nakeji,,Sallah zakiyi Sai ki koma baccin,,kinga nima Shi nakeji.. Kasa Tashi nijlah tayi saima juya masa baya datayi tana turo Dan qaramin bakinta,duk a cikin bacci.. Ganin tana Bata Masa lokaci yasashi fara yamata chakulkuli,,tinda bazaki tashiba ninasan maganinki.. Dariya nijlah tariqayi tana ture hannunsa,,nan ya dauketa ya kai toilet,,harya juya baya da niyyan tafiya yaji takira sunanshi.. Nini ban iya kunna wannan ba,,ta fada tana nuna kan famfo,, murmushi yayi ya kunna mata,,tsayawa yayi Yana kallanta kafin yace to madam Sai Kuma me,, brushe ta nuna masa tana satar kallanshi. Bashida yadda zeyi Dan haka ya dauko nasa ya matsa maclean,,amsa tayi tana boye fuska tace nagode.. Idan kin gama ga ruwa nan Sai kiyi wanka ,,ni ah ah,bayan nayi wanka dazan kwanta,,nifa kaka har fada takemin idan taga ina wanka kullum To suda ba wannan na tambayeki ba,,wanka nace kiyi ko harkin manta laifinki,,shiru nijlah tayi tana kauda fuska,,nan ya fita yana cewa kiyi sauri ina jiranki.. Bata Dade ba ta fito tana turo Baki,,kallanta yayi yaga babu alamun wanka a jikinta, idansa akanta yace,,Amma dai Baki wanka ba??? Daga masa Kai tayi ta kuma qi qarasowa inda yake. Meya hanaki Yi? Kai tsaye nijlah tace,,ban iyaba,, Murmushi kawai yayi kafin ya nuna mata sallaya,, hijabi tasa tayi saurin tada sallah Dan zuwa yanzu tafara gajiya da kallan dayake mata.. Kafin ta idar harya hau kan bed yana bacci yafara daukanshi.. Nijlah kasa hawa gadon tayi Dan tsoro,,nan ta kwanta kan sallaya itama bacci ya dauketa.. ********** Nasir nifa tsoran fita nake Dan wallahi gani nake kama malam ze iya gane wani abu,,dafashi Nasir yayi yana magana a hankali.. Kaga Bello ka kwantar da hankalinka,,ninasan malam baze kawo komai a cikin ransa ba,,tinda dai yana ganina a gari.. To shikenan Nasir Amma fa saika rakani, Tashi Nasir yayi yana kama hannun bello,,kaga tashi muce kafin lokaci ya qure.. A kofar gida suka Sami malam danya kasa zaman gida,,sabida kukan da kaka ta damesa dashi,,yayi rarrashin harya gaji Dan haka ya dawo kofar gida koze Samu sauqin wani abun.. Yana ganin su bello yafara murmushi yana cewa.. Ah ah Muhammad bello harka dawo,,daga masa Kai yayi suka qarasa kusa dashi suka zauna.. Bayan sun gaisa,,Nasir yayi qoqarin sanar da malam abinda ya faru na rashin zuwan bello birni.. Nisawa malam yayi kafin ya maida hankalinsa ga Nasir yace.. Nasir nifa banaji a jikina yarannan mashkur ze wulaqanta nijlah,,jinake kama ze riqeta Amana kamar yadda muma muka riqeta,,duk da cewar mu dole tane,,sedai ina masa zatan alkairi,,idan kuma yaci Amana shida Allah,,Dan ko bamuyi masa Allah ya isaba nasan zata bishi.. Hakane baba to Dama shiyasa mukaga ya dace muzo mu gayama,, Godiya sosai malam yayi musu kafin ya tashi ya shiga gida,,shidin ma karya yayima kaka yace bello yadawo lafiya kuma yaga gidan da aka Kai nijlah Dan Shima anyimasa karba ta musammam. Sosai yakumbo taji dadin labarin malam harta fara sakin ranta daga damuwar datake ciki,,haka ta kwana cikin farin ciki.. ******* Kwana Yasmeen tayi tana fama da kanta ga wani zazzafan zazzabi daya rufeta Banda karkarwa babu abinda take,,ahaka har garin Allah ya waye tana nan nade cikin bargo,,,mama bata iya leqataba sabida haushinta datakeji,,abbane ya fito cikin shirinsa na zuwa office kalllan mama yayi yana cewa.. Hajiya yana ganki ke daya kina karyawa,,ina ita 'yar lelen take?? Tabe Baki mama tayi tana nuna masa dakinta,,Abba be qara magana ba ya shiga dakin,,nan ya ganta kwance cikin bargo dasauri ya qarasa yana janjan bargon tare da kwalawa mama Kira.. Hajiya hajiya,,Baki da hankali Zaki barmin yarinya cikin wannan hali,,da gudu mama ta qarasa shiga tana cewa alhaji lafiya.. Inafa lafiya duba kiga halinda 'yar lele take ciki,,wallahi idan wani abu ya Samu yarinyata sainayi maganin wannan yaran me suffar munafukai.. Kayi hakuri ba laifin kowa bane bace laifinta,,shidin mijintane ko Dan ita kadai aka haliccesa dazatasa

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46