Skip to content

Chapter 33

Chapter 33

Yar Sadaka Book One Complete Hausa Novel 1,237 words 0 views Progress saved
Download Book

Maza? Cike da shagwaba Yasmeen tace toba Naga yanzu kowa man saka fari yake shafawa.. Badai kowa ba kuma a yanzu duk namijin dayasan kanshi Baya zaben kyau,, kyankyawar tarbiyya Ake Zabe gashi ke kin Nuna Baki da ita.. Bakin Yasmeen a gaba tace toba nadena ba" Allah yasa cewar mama. Yanzu saiki tura masa text message ki bashi hakuri, nasan ze karanta. To Yasmeen tace ta tashi tana murna Dan ita ta manta da wani text massage" Zazzafan sako Yasmeen ta tsara tare da turama mashkur. Zaune yake ya dawo daga restaurant Yana qoqarin hadama nijlah abinci yaji qaran zuwan sako cikin wayarsa.. Be duba ba ya cigaba da abinda yake,,Saida ya Gama hada Mata tea ya dauko ya dawo kusa da ita Yana miqa mata... Nina koshi nijlah tafada cikin shagwaba" Amsa kisha banasan musu" To tace ta amsa tana sha badan taso ba,,ki dauka wannan abincin Shima ki cinye inba so kike likita yaqi bamu sallama ba.. Batayi magana ba tafara cin abinci tana ci tana yinqurin amai Shi kuma Yana shafa bayanta ahaka harya Samu taci da yawa. Gefe ya koma Yana qare Mata kallo tare da tinanin ta inda ze dauki matakin daya dace Kan Yasmeen.. Wayarsace tafara ruru nan yasa hannu a hankali yayi picking wayar ta hanyar kaita kunne Hade da sallama.. Daga daya bangaren mummy ta amsa da kyar tace" Auta kana da hankali kuwa,,ko kanaso kace jinyar matarka yafi zuwa Ka gaisheni?? Bakinsa na rawa yace' kiyi hakuri mummy anjima Zan zo idan ta fito babu Wanda ze zauna da ita,,mummy nijlah na buqatar kulawa sos.... Bata Bari yaqarasa ba tace" rufemin Baki kafin na bigemaka Shi ta cikin wayan" kazo Ka sameni yanzu base anjima ba inasan ganinka,,Ko ita ta haifamin kai dazata riqeka yarinyar da Ko haqqinka bazata Iya saukewa ba Amma kake rawar kai akanta.. Shiru mashkur yayi be qara Magana ba Har Saida mummy ta gama yafara Bata hakuri"mummy kiyi hakuri insha Allahu yanzu Zan zo"kadama kazo auta kadai zauna kana jinyar banza Naga ita tafi karbanka Akan kazo muyi shirye shiryen bikinka... To kawai yace yana sauraran mummy tagama fada ta katse wayar' tinda yafara waya nijlah ta kafeshi da Ido tana sauraran abinda yake fada' Ko Bata tambayaba tasan fada akemasa Wanda Waze wuci akanta Ake abin ba,,Yana gama wayar Shima ya zuba Mata Ido tare da cewa' Ke Kuma wannan kallan fa? Dauke Kanta nijlah tayi tana mejin tausan halin da tasashi ciki,,haka nan Taji tanasan ganin kaka,,koba komai Zata rungumeta a jikinta ta rarrasheta yanzu ki bata dame yimata haka sai Wanda Zena mulmula Mata nono Wanda ta dauka hakan a matsayin wahalarwa da hukunci me tsaurin gaske.. Ganin Yadda ta zurfafa cikin tinani yasa mashkur qarasawa kusa da ita Yana cewa" amarya tinanin me amaryana take? Boye fuska nijlah tayi taqi dagowa,,duk yadda yayi nasan ganin fuskanta taqi yadda yamata wasan harya gaji ahaka wani sakon ya sake shigowa cikin wayarsa... My baby ya gani nan yayi murmushi tare da duba sakon,,Yana karantawa Yana dariya harya Gama ya rungume wayar a qirjinshi Yana cewa" Allah yasa haka babyna naji dadi kalamanki sedai bazan iya Baki reply ba har sai matata ta Samu sauqi keda kika dariyana.. Dagowa nijlah tayi tana sauraransa harya Gama magana Dan a fili yake magana" haushi da takaicine suka kamata Dan idan bata mantaba sunan dataji Yana Kiran Yasmeen kenan dashi a lokacin datake kwance Kan ruwan cikinta"mtssss yaji anja tsaki Wanda besan daga inda ya fito ba,,dasauri ya dago kansa Yana kallan nijlah da zuwa yanzu hawaye suka fara cika Mata Ido.. Kasa magana yayi sabida tsabar mamaki wai me wannan yarinyar take nufi Dani,,badai kishi take da baby ba? Tabdijan indai ko hakane zanga irin zaman da zanyi dasu ahaka,,gashi Bani dasan raba Iyalina... Yana cikin tinani nurse ta kwankwasa dakin,,firgigit ya dawo daga tinanin tare da bata umarnin shigowa" da sallama nurse ta shigo ta Basu ta kaddatar sallama tare da yiwa nijlah fatan samune lafiya,,da ameen Mashkur ya amsa nijlah ko bata iya magana ba sabida abinda ya tokare Mata maqogwaro.. Nurse na fita mashkur yafara hada musu kayansu,,Saida ya Gama ya juyo Yana Yana cewa,,zaki iya tashi mu tafi idan kuma anan zaki zauna to? Nijlah bata amsashi ba ta tashi a hankali tana sa takalminta" dasauri ya fita yakai kayan mota ya dawo ya riqe hannunta suka fara tafiya" duk inda suka gifta kallansu Ake kowa na fadar albarkacin bakinsa ahaka har suka Kai mota nijlah na yimasa shagwaba wai ta gaji da tafiya,,be kulata ba ya zagaya ya Bude Mata mota Yana cewa" Wai Bana gayamiki ki koya yadda Ake Bude Moto ba,,koni driver kine? Murmushi nijlah tayi tace,Toba gashi can Wani ma Yana budewa matarsa Mota ba,, Kallan inda nijlah ta Nuna mashkur yayi nan yaga wasu Mata da miji,,mijin ya budewa matar mota ta fito hannunta dauke da baby girl Yar qarama.. Murmushi yayi Dan Shima mutanan sun birgeshi" beyi Magana ba ya zagaya bangaren driver ya Bude,,Yana Shiga itama ta Shiga nan ya tada motan suka fara tafiya.. Seda sukayi Nisa ya juyo Yana kallanta" a hankali yace,,amarya Nima Zaki Iya Bani irin wancan babyn,,Naga kema yarinyar ta burgeki Ko? Cike dajin Dadi nijlah tace" eh mana Zan Iya" cike da farin ciki Mashkur yasa hannu ya janyota jikinsa Yana shafata yace" yaushe Zaki Bani? Kai tsaye nijlah tace" Abu me sauqi Duk lokacin da kakeso Allah Zan Baka,,ba ance ana bacci Ake haihuwa ba.. Tinda mashkur yaji abinda nijlah tace haushi ya kamashi anan ya gane batamasan abinda yake fada ba.. Ahaka Har suka qaraso gidan mummy" Sai da ya daidaita parking motan kafin ya Bude ya fito,,itama ya Bude Mata. Hannunta ya riqe suna tafiya a hankali Yana aiki yimata sannu" kai tsaye falon mummy ya nufa da ita... Yawan comments yawan typing. *Momn sultan ce*✍✍✍ 💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘 *STORY & WRITING BY...* *BY* *MOMN SULTAN* *DEDICATED TO.....* *MMN AMATULLAH* *SPECIAL GIFT TO...* *Dr JANAN.....* 5⃣0⃣&5⃣1⃣ Mummy na ganin shigowar mashkur hannunsa riqe Dana nijlah ta Mike tsaye"jikinta Har kyarma yake gurin finciko nijlah ta cillata Baya tana nuna mashkur da dan yatsa'wallahi Karya kake mashkur nadena zubamaka Ido kana yadda kaso" kwana fa kayi tare da wannan shegiyar yarinyar,mummy ta fada tana nuna nijlah dake rabe jikin bed tana hawaye' Nan take zuciyar mashkur tafara bugawa da qarfin gaske Babu abinda yake kallo Sai nijlah data daskare tsaye tana mamakin halin mutanan da Allah ya hadata Zama dasu" Yanzu shikenan ahaka zanyi rayuwa? Adakeni lokacin da akaso,,a zageni Duka Ni daya? Nijlah ta tambaya Kanta tana sakin kuka meban tausai.. Girgiza Mata kai mashkur ya shigayi yanasan hanata kukan,,da yanada Iko jikinsa ze janyota ya rarrasheta koya rage Jin abinda yakeji a cikin zuciyarsa.. Dan gidanku auta Bada kai nake Magana ba,,kodai kurma ka Zama? Fuskar mashkur sake yake kallan mummy Amma a can cikin zuciyarsa bacin raine chinkuye a ciki sedai bashida damar nunawa mummy Hakan.. Ka tsareni da ido Ko bakaji tambayan danayi Maka ba? Murmushi yayi Wanda yafi kuka ciwo ya Bude baki ahankali zuciyarsa na bugawa yace'mummy bafa a gurinta Na kwana ba,,inacan muna tsara yadda za'a gudanar da bikinmu da Yasmeen to shine dare yayi,Saina zauna Na kwana acan.. Yanzu

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46