Chapter 1
Chapter 1
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ο»Ώππ *'YAR SADAKA..*ππ *STORY & WRITING BY...* *BY* *MOMN SULTAN* *DEDICATED TO.....* *MMN AMATULLAH* *SPECIAL GIFT TO...* *MMN FAREESAH* *Alhamdulillah Naga comments iya comments,hakan ya nuna kuna da buqatan cigaba da labarin,,Dan a gaskiya nayi mamakin jama'an dakemin magana akan nasasu a group duk da ban Bude ba,,sedai inanan Zan Bude sabo zanyi adding zafafa wadanann Nike karanta comments nasu inajin nishadi lolxx* *BISMILLAHIR_RAHMAANIR_RAHIIM* *Yadda nafara a sa'a Allah kabani ikon gamashi lafiya,,Allah Ka Bani ikon rubuta abinda al'umma zasu amfana dashi su nishadantu su kuma ilmantu,ya Allah kasa duk Wanda ya karanta yaji farin ciki koda Yana cikin baqin ciki* *A koda yaushe ina alfahari daku masoyana masoya labarai nah,,iya wuya muna tare da yar dar Allah*π€πππ 1β£&2β£ Yanzu kawu bazaka bar tafiya Saida nono ba,,kaduba yadda Aisha ke fama da danyen jego Amma a haka kuke yawo kasuwa kasuwa,,Baka tsoran sanyi ya kama yarinyar nan.. Shiru kawu yayi kallan dattijuwar dake magana tana qara riqe yar qaramar yarinya a hannunta,,Wanda bazata wuci wata 3 ba.. Yakumbo kiyi hakuri ki cire soyayyan yarinyar nan a zuciyanki,,tinda kinsan dole sai mun fita Saida nono kafin mu Sami abinda zamu sa a bakinmu,,kinga Aisha dauko kwaryar nono can mu tafi kinga Rana nayi.. Dasauri Aisha ta dauko zani ta miqa hannu biyu,, yakumbo kawota mu zamu tafi,, murmushi yakumbo tayi tana cewa.. Badan nasan halin nijlah da kuka ba,Aida na riqe diyarnan harkuje Ku dawo,, murmushi Aisha tayi tana girgiza Kai,,nan yakumbo tabasu nijla suka kama hanya suna sauri kowannensu dauke da kwaryar nono suka tafi titi.. Ki daga qafa Aisha kinga Rana ya cinmana gashi yau kasuwan cika yake,, banaso muyi kwantai" kayya Mai gida,,yanzu duk saurinnan danake Baka gani,,ni wallahi bayana har ciwo yakemin.. Kiyi a hankali kinsan dai bamu da yadda zamuyi,,turo Baki Aisha tayi tana gyara goyon nijlah tace,,nifa yinwa nakeji,,ace tin safe Mai Rai besa komai a cikinsa ba,ga nono ana damuna dashi. Shiru kawu yayi suna cigaba da tafiya Dan daga kauyensu zuwa titi ba qaramin nisa gareshi ba.. Sunyi sa'a suna zuwa titi suka samu mota,,dasauri suka Shiga kayansu a hannu ga nizlah dake faman kuka a Baya.. Da shigansu mota ya tashi ana harhada kudin mota.. Drive kayi hakuri na koki arziqi,wallahi kaga banida ko Sisi sai naira ashirin,,nasan Kai musulmine zaka temakeni" Kai kuturin uba,uban wa kike tinanin ze cikamiki kudin,,kufa matsalan tsofi irinku Kenan.. Dakyar dattijuwar ta Kada Baki tace,,kayi hakuri Ka kaini sadaka,,to bazan iyaba drive ya fada Yana masifa.. Sosai ya riqa zazzaga jaraba har Baya ganin abinda ke gabansa,,kawu ne ya Bude Baki da niyyan magana ai kafin ya qarasa jikake,,gara rann gammm.. Qatuwan Mota tabi ta kansu,,gaba daya Yan Motan suka sa salati,,ihu da kururuwa suka riqayi ba masu ceto sabida gurin bana wucewan jama'a bane,,dakyar aka samu Motan dauko Kaya suka kawo musu agaji,, Sedai wannan hatsari yazo da tashin hankali domin kuwa duk cikin Motan,, driver ne kawai ya rage sai nijlah daketa faman kuka sabida matsan dataji a bayan Aisha Wanda tini Rai yayi halinsa.. Tini aka kwashesu zuwa hospital,,taimakon gaggawa aka Basu,inda aka samu nasaran tsayarda kukan nijlah,,ta hanyar bata madara,,shiko drive karaya ya Samu hannu da qafa.. Tini aka dauki photunan gawawwaki aka Fara yadawa a media Dan neman 'yan uwansu.. Tare da bazawa a gidajen radio,,Malam dake zaune yasa radio a gaba Yana sauraran labaran Rana yaci Karo da wannan mugun labari.. Dagudu ya fito a daki Yana kwala Kiran yakumbo,, yakumbo dake fitowa a bayi ta fito tana Kiran,,Malam maiya faru kakemin irin wannan Kira,,kaiko yinwa bakaji, Ka iya magana da karfi haka.. Malam be iya magana ba,,sai Dora hannu da yayi aka, shikenan mutuwa tayimana zuwan sauri,,katangar da muka dogara da ita ta rushe,, subhanallah Malam kukafa kake,,meya faru,wa kuma ya mutu,,kayi saurin gayamin kafin zuciyana ta Ida bugawa,, yakumbo ta fada cike da tashin hankali.. Kawu ne,kawune yakumbo ya mutu kawu ya rigamu gidan gaskiya daga Shi har matarsa Aisha,kafin yakumbo tayi magana Inna Babar Aisha ta shigo hannu a ka tana kuka.. Tare suka runtuma zuwa asibitin,,basu sha wahala ba,aka Basu gawan kawu da Aisha tare da nijlah da Allah yasa tana da sauran kwana a gaba.. Tinda suka dawo gida aka sallaci aisha da mijinta,, Abu yayiwa yakumbo zafi,,ta Shiga cikin tashin hankali mara musaltuwa. Bayan sadakan bakwai,Inna ta buqaci da abata nijlah Dan ta riqe tana Debe Mata kewan aysha. Kuka yakumbo tasa tana cewa,,Inna bawai naqi bane,,sedai bazan iya Baki nijlah ba,,sabida ita nake gani kama kawu,,Sanin kanki ne tinkafin rasuwan Aisha Nike Kula da dawainiyar nijlah,,Dan a dole nake Basu iya idan zasu fita yawan kasuwan sabida kukanta. Itama Inna kuka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46