Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

Canjin Rayuwa Book Four Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
Download Book

cike da kewarsu. Zainabu ta gama girki ta raba taba kowa, kusan kwano ashirin da uku. Matuqa ta qosa ta fita a madafin sbd hayaqi da kuma zafi. Ta dauki nata da kuma na mai gidan, duk da baci yake ba, amma qa'ida ce kullum sai an zuba masa. Habu da adamu suna jira ace su dauka, tace, ku dauka, sai ku fadama sauran cewa suzo su dauki nasu. Habu ya dauka tare da fadin, ke kullum abincinki baya dahuwa. Adamu yace, eh mana ke baki iya girki ba. Tace, ku bakuda kunya. Ni sa'arku ce? Maman su Habu ta fito, dama kamar tana jira, "karki takura min yara. Ai ba qarya sukayi ba. Duk ranar girkinki, saidai a zubar ko ko aci da haquri. Jikin zainabu ya soma 6ari don tsoron fada gareta. Tace, ni bazan takura musu ba kuyi haquri, ta nufi samansu. [17/09 8:49 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 2⃣5⃣Daidai lokacin kuma Alhaji ya shigo, yana jiyo hayaniya, yace, Hama lfy kuke min hayaniya da farar magriba? Tace, Zainabu ce zatayi min rashin kunya, don yara sunce ba zasu iya cin abincinta ba. Alhaji yace, sbd me? Tace, to abincin bai ciyo don bata iyaba. Alhaji mutum ne wanda komai qanqantar magana, sai ya ririta ta. Don haka sai yace, yanason duk 'yan gidan su hallara. Ya tara su har zainabun. Yace, su fada masa da gske ne girkin Zainabu babu dadi? Maman bushira tace, injiwa? To kai da zaka tambayemu baka ta6a ci bane? Yace, to iya magana, jikar zance, ban dake, don na kula kinfi son yarinyarnan da iyalina. Ya dinga bin yaran da sauran matan yana tambayarsu ko ta iya? Suka dinga cewa babu dadi. Sai 'ya'yan Maman bushira ne kurum Sukace sudai suna ci. Alhaji yace, ban ta6a cin abincinta ba amma yau zanci, in har baiyi dadi ba, kamar yadda kuka ce, to zan dauki mataki. Don bazan dinga fita da sassafe neman abinci ba, sannan kizo kina girka shi son ranki, a kasa ci ana zubar dashi. Zainabu dai shiru tayi, sbd ba tada ta cewa, amma fatanta shine Allah yasa ya yanke mata hukuncin saki. Shi Alhaji ba mutum bane maicin abincin gidansa, yafi zuwa Gidan abinci shagunan masu indomie koko gurin masu tsire. Dakinsa ya kira Zainabu yace, ta bude abincin ya gani. Jikinta sai 6ari yake, ta bude, qauri ya cika dakin. Yace, eh lallai dole yara su kasa cin abinci, tun kafin in kaishi baka ne wannan qaurin yake tashi? Ta kalleshi cikin tsananin tsoro, yace, uwarki bata koya miki girki bane? Tace, ni ban iya yin girki da babbar tukunya ba, kuma gashi a murhu. Yace, da Allah rufe min baki! Nine zaki fadawa baki iya girki a murhu ba. Ubanki baya iya ci da gidanku. Ni nake riqe da gidanku, da har zakice min baki iya girki da murhu ba. Wa zaki gaya ma kokai dan uban waye. Da dai kince sakaryar uwarki bata koya miki ba, sai yawon talla da nafi yarda. Ran Zainabu yakai maqura gurin 6aci, tace nidai gsky duk abinda za'ayi, ayi, amma a daina zagin iyayena. Kuma ai duk yaushe muka hadu da zaka ce kai ne kake ci da gidanmu? Ashe Zainabu ta tafka kuskure daya fada ta fada. Domin ba'a fadi yana fadi. Nan take ya tashi a fusace, ya hau kilarta. Maman bushira tana zaune Zugum tana jiyo ihun Zainabu, baqin ciki fal a zuciyarta, domin tana tsoron kar wannan halin da mijinta keyi ya juye kan 'ya'yanta, sbd in ka cutar da dan wani, sai an cutar da naka don kaima kaji. Haka yayi ta kilarta har ya gaji, yabarta don ba zuwa ceto. 2⃣6⃣Tun Zainabu tana kuka har ta kasa. Yace, tashi ki fitarmin a daki! Kasa tashi tayi, domin data yunqura, sai ta koma ta zube. Sai kuma ga jini ya soma zuba. Idanu ya zaro yana kallonta. Sai kuma ya soma kiran Maman bushira. Ta shigo ranta 6ace, yace, kamata zuwa daki, naga jini yana zuba, ko dai al'ada takeyi? Maman bushira tace, wace al'ada kuma? Yarinyarnan ciki gareta, saidai inka sake doko cikin. Yace, ni ban doketa a ciki ba. Maman bushira ta dago ta tana kiran sunanta "Zainabu! Zainabu! Cikin tsoro tace, Alhaji yarinyarnan tana da rai kuwa? Da sauri yasa takalmi yace dauke ta zuwa dakinta, bari in kira danladi Mai chemist. Tace, ka dauketa dai, ni ai bazan iyaba. Cikin tsawa yace, kama ta muje mana. Kan gadonta suka dora ta, duk jini ya 6ata hanyar da kuma dakinsa da nata. Ya fita da sauri. Maman bushira tace, maganinka kenan! Allah yasa ya zamar maka ishara. Zainabu dai tanaji, ba suma tayi ba, amma tana cikin mawuyacin hali. Sake yin lamo tayi tare da sakin jiki sbd jin rudewar da Alhaji yayi. Ko da danladi mai chemist yazo, dauke Numfashinta tayi. Dama shi ba wai ilimin gareshi ba, ya ta6a yin shara ne a asibitin Gwamnati, shine yazo ya bude chemist mutane suke ta tururuwa. Danladi yana ta6a ta, sai yace wai, wai, Alhaji! Gsky kuje asibiti, don gsky ba zan iya ba. Dubi jinin fa kamar an yanka qaramar dabba. Alhaji ya zaro ido cikin fargaba, to ni yanxu wane asibiti zamuje? Banason zuwa wannan asibitin Gwamnatin. baba yace bari in kwatanta maka wani na kudi ka kaita bakinka alaikum. Sun kaita, an amsheta, amma yayi kashin kudi masu yawa, sannan kuma cikin yananan bai fita ba. Bayan tafiyarsa Gida, gurin qarfe sha daya Nurse din da ta taya likitan aiki lokacin da ake qoqarin tsaida jinin, ta samu maman bushira a zaune kan kujerar dake kusa da gadon da Zainabu take kai kwance, tace, sannu mama. Maman bushira tace, yauwa 'yan mata sannu da aiki. Mun gode fa. Tace, yauwa dan Allah mama, wannan 'yarki ce? Maman bushira tace, a'a kishiya ta ce. Nurse din ta zaro ido. "Kishiyarki kuma? Kina nufin wancan daya fita mijinku ne?" tace, eh. [17/09 9:56 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 2⃣7⃣Nurse tayi shiru tana matuqar mamakin lamarin. Can tace, to wai wanene yayi mata dukan jikinta? Tace, shine ya duke ta. Wlh haka yakeyi. Yayita auro 'ya'yan mutane yanacin zalinsu. Nurse din tace, kinga ko Mama da ace Allah zan hadaki da ainihin babbar likitar dake da wannan asibitin. Kiyi mata bayani, wlh zata gyara masa zama. Maman bushira tace, rufamin asiri. In ya sani ai na shiga uku, domin dama inacin darajar manyan 'ya'ya na ne, sai kuma irin wannan ranar in yayi ta'asarsa yazo ya matsamin in tayashi. Nurse tace, inda zaki iya da na hadaki da ita. Allah zatayi muku maganinsa, sai ya daina. Kuma ko daya sunanki ba zai fito ba. Tace, to shikenan ki hadamu don zan mata bayani, amma don Allah kamar yadda kkce, kar sunana ya fito. Tace, ba damuwa. Gobe ai kina nan ko? Tace, eh nizan kwana, amma na san shima zaizo da safe. Alhaji lawal, tunda yaje Gida ya tara sauran matan yasa su suka gyara gurin jinin. Shi dai tunda ya shige dakinsa ya zauna ya zabga Tagumi, ya rasa bakin magana. Da na sani ce cankas a zuciyarsa. Tsoronsa daya kar 'yar mutane ta mutu. Ranar dai bai runtsa ba, sai juyi yake. Washegari tun takwas ya nufi asibitin. Lokacin Zainabu

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37