Chapter 28
Chapter 28
daguwar riga ruwan qasa, mara nauyi, bata daura dankwali ba, ta kama gashin kanta a gefe. Tunda ta nufo shi ya kasa daina kallonta har tazo ta zauna akan kafet kusa dashi. Tace ina kwana? Yayi murmushi, "lafiya lau" kefa kina lfy? Tayi dan fari da ido " qalau" ta gyara zama tace ynxun yaya zamuyi, tunda bamuda abinda zamu hura wuta? Yayi murmushi. Fita zanyi in siyo mana abinda zamuci. Tace a'a kawai muje gdn yaya Amina muci. Yace kinsan yau dai ba zasuyi damu ba, amma bana siyo butar dafa ruwan zafi ba? Tace haba? Ni banganta ba. Ta miqe zamu dafa ruwan tea. Yace muje in gani, amma tabbas na siyo Butar ruwan zafi. Sun dafa ruwan zafinsu, suna sha, suna labari kadan-kadan. Daga bisani yayi wanka ya fita. [27/09 3:47 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 8⃣6⃣Ranar da suka cika kwana uku, Ismail yaji haqurinsa zai kasa. Don haka yaga babu abinda yafi illa ya ziyarci zainabu. Koda ya shawarci mahmud sai yace masa kar ya soma, ya dai yi qoqari ya sasanta da matarsa. Sam ismail zancen bai shigeshi ba, domin yasan tun filazal ba sonshi da Zainabun sukeyi ba. Don haka ya yanke shawarar kiranta a waya don ya fada mata cewa zai kawo mata ziyara. Misalin qarfe hudu bayan sun fito la'asar ya ciro wayarsa ya soma neman lambar zainabu. Koda yazo kan lambar saida yadan jima yana tunani kafin ya danna kira ya tafi, lokacin zainabu tana kwance a qofar dakin innarta tana buga game din maciji, sai kawai taga kira ya shigo. Ganin sunan dake rawa akan fuskar wayar, saita zaro ido tare da murza idon, sannan ta dauka cikin sauri tare dayin sallama. Sun gaisa sannan yana ganin saqonta na gaisuwar juma'a kuma yana godia, tace ashe kana gani, nayi zaton ma baka gani tunda kuna hulda da jama'a sosai. Yace ina gani, ko zan sameki anjima? Cikin sauri tace, inanan Malam. Yace, qila in shigo anjima. Tace to Malam, Allah ya kawoka. Duk mahmud yana jinshi.Misalin takwas da mintuna mimi tana daki tana danna wayarta, so take ta tsokani ismail tana kiranshi amma yaqi dagawa, sai kawai Mimi taga ya fito cikin shadda wagambari sai maiqo takeyi. Mai kalar blue, haka hularsa. Ta wundo ta hangoshi. Cikin sauri ta 6oye wayar sannan ta fito, ina kuma zakaje da darennan? Yace wata 'yar unguwa zanje bazan jima ba. Tace inzo in raka ka? Ta fadi haka ne don ranta ya raya mata ko gurin wata zashi. Yace a'a ki barshi ba ni kadai bane nida mahmud ne. Tace kasan dai inajin tsoro, don Allah karka zauna. Yace ynxun zan dawo. Tace amma bada mota zakaje ba? Yace da ita zanje mana. Nifa na tuqo motar daga unguwar su mahmud dazu, bare ynxun da babu cunkoso. Ta windon su na sama take leqensa ya fita da motar, sannan ya dawo ya rufe gidan, ta saki labule, ta koma ta zauna tana ta karanta wasiqar jaki. Yana isa gidansu zainabu, ya kira ta cikin waya ya fada mata ya iso. Cikin soron gidansu suka zauna. Sun gaisa sannan ismail yace, gani nazo a karo na biyu, banda zuciya ko? Cikin sauri tace, malam kayi haquri, ko da ba laifina bane. Wlh ina sonka, shine ma dalilin da ban iya zama gidan Alhaji ba. Yayi murmushi, to ina fatan ba zan sake samun matsala ba, don wannan karon banason aja lokaci. Tace ni ko gobe ka turo, don dama zaman jiranka nikeyi. 'yar dariya yayi, sannan yace shikenan ko ban sake zuwa akan lokaci ba zamu dinga waya. 8⃣7⃣Wasegari ya samu gayyata daga abuja, jami'ar da ya nemi koyarwa. Yaje kuma sun daukeshi, yayi murna sosai. Haka ma dangi sunyi murna, illa mimi kadai da take ganin cewa za suyi nisa da juna. Yayi mata tayin ziuwa abuja tace, ko sha'awar zuwa bataso. Yace, nasan ba zaki iya zama ke daya ba, yaya kk son ayi? Tace zan koma gidan su yaya Amina, in ka dawo sai in dawo. Da kanta tace, ya sakata islamiyya a unguwar su yaya. Sam in kaga Mimi ba zakace ita bace. Sbd dogon hijabi da niqabi. Lecturing daya soma sai ya dauke hankalinsa daga kan batun auren daya so yi cikin gaggawa. Amma dai suna waya da zainabu. Duk sati yake zuwa, wani lokacin sati biyu. Shi mahmud ABU zaria ya samu. Ismai ya kira masu aiki sun duba filin dake gidansa sun tabbatar masa zai iya yin makaranta harda madaidaicin masallaci. Bayan sun bashi tsarin ginin, sai ya soma tunanin yadda zai samu kudin ginin don kudin da aka qiyasta makarantar zataci ba qanana bane. Harkoki sun bude ma ismail, ga alherai da yake ta samu daga jama'a, domin ranar da akayi wata hira dashi a gidan TV na Africa, lokacin gidan TVn yana sabon budewa, har ya sako bayani akan makarantar da yakeson ginawa, ko sati ba'ayi ba, saiga shi mutane sun fara kiransa don son bashi gudunmuwa. Kafin wani lokaci tuni an soma gini. Babban qalubalenshi mata. Ko a makaranta, mata ne keta kawo mashi hari. To don yana malami, shi kam ba waliyyi bane, da yawa ana jarabtar Malamai da son mata da kuma kudi, in bakayi taka tsantsan ba, sai ka fada halaka. Shi yasa ya gama yanke hukunci. Yana samun hutun qarshen zango yazo, to kuwa aure zaiyi, ko ma da wacece. Wata asabar ya dauki takardar da Mimi ta rubuta duk abinda suke buqata, ya shiga kasuwa, sai da yayi rabi, tun daga kan gado zuwa saurensu. Dakin mimi kuwa saida ya tsara mata shi fiye da nasa, sannan yayi mata sayayyar kayan sawa, sannan ga sabuwar waya da kuma layi, tsohon nasa ne ma ya bata. Don har ynxun baisan tanada waya ba.zainabu ma yayi mata 'yar sayayya. Bayan sunyi hutu, dukda cewa sati biyu ne hutun nasu, amma cikin sati biyun zai yaye ma kansa damuwa. Shiyasa ma washegari da safe yana zaune falon qasa yanashan tea, saida yaga itama tazo ta zauna , sai ya dauki wayarshi yana kiran layin zainabu, da farko hankalinta baya kansa, saida taji yace zainabu, cak ta tsaya ta kada hadiye tea din data kur6a. Yaci gaba ina gari zan shigo anjima yaudai zamu gama magana. Inason kafin hutunnan ya qare zaki zama a gidana. Cikin murna take fadin sai kazo. Yana kashe waya mimi ta maida tea din dake bakinta cikin kofin, sannan cikin wata irin murya tace magana zaku gama? Ya dubeta fuska daure, "khadija aure zanyi" ji tayi tamkar ya soki zuciyarta da qaho. A hankali ta jingina da kujera, sannan ta lumshe ido, ta rasa me ma zatace. Sai kawai ta tashi ta nufi dakinta. Bakin gado ta zauna, rashin wanda zai baka shawara matsalane. Tasan tunda yace mata aure zaiyi, to kuwa yana nufin rabuwarsu tazo kenan. Wata zuciyar tace, lokaci yayi da zaki koma gidan iyayenki. A fili tace, kai da saura. Haka zan koma musu bayan shekara uku, babu wani ci gaba, ba kuma auren da suka daura min, bayan tsohon laifina na baya? Ta girgiza kai, lokaci baiyi ba. Mafita ya kamata in nema. Ya turo qofarta ya shigo. Jikin sif dinta ya jingina. Khadija ban zaci zakiyi fushi ba, Nafi zaton zakiyi murna, don lokaci
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37