Skip to content

Chapter 20

Chapter 20

Canjin Rayuwa Book Four Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
Download Book

Ita kanta Mimi batasan meyasa ta sauri ba don ganin ta kunna TV. Dirshan ta zauna a gaban TV din tana kallon Ismail cikin qaton masallaci, mai cike da jama'a sunyi tsit suna sauraron daddadar muryarsa. Ta qaro sautin TV din ta koma saman gado tana kallonsa. Tsawon awa daya daya dauka yana yin wa'azin, haqiqa ya ratsata. Bata ta6a zama ta saurari wa'azi ba kamar yau tunda take. Yaya ta shigo tana cewa, kinfa kawunsu Ummi ko? Mimi tace, gsky yanada basira sosai, ya iya tafsir. Yaya tayi dariya, ji tayi tana alfahari dashi. Mimi kuwa, qosawa ma tayi ta ganshi. Inda ya sake burgeta, yadda ya yita amsa tambayoyin mutane da sukayi ta rubutowa bayan an gama wa'azin. Haka ya yita basu amsa cikin ilimi da hikima tare da kawo hujjoji cikin Qur'ani da Hadisai, ko kuma ittifaqin malamai. Mimi dai Ismail ya burgeta har qarshe. Don haka yau da sukayi qosai da kunun gyada, da kanta ta debi nasa ta shirya masa, ta shinfida darduma tana jiran zuwansa. Amma har kusan tara baizo ba. Bata ta6a damuwa don Ismail baizo ba irin yau. Jiya ma da yazo Ummi ce ta kawo masa abin buda baki, amma yau wata kimarsa ce ta qaru a idon Mimi. Tayi ta kai kawo a cikin daki, ta qosa sosai ta ganshi. Agogon dakin ya buga qarfe tara da kwata, ta miqe da nufin ta tambayi yaya, wai yau Kawunsu Ummi ba zaizo ba? Sai kawai taji muryarsa yayi sallama ya shigo gidan. Ta koma baya ta zauna a bakin Gado. Qosawa tayi su gama gaisawa da yaya Amina ko ya shigo, amma ya jima can kafin ya shigo. Da farko ta tsara zata tareshi cikin murna, amma yana shigowa sai taji wani jinkai ya taso mata, ta kishingida tare da fadin sannu da zuwa. Ya zauna bakin gado, sannunki da hutawa. Tace, kaine da sannu. Yau kam bakazo shan ruwa ba? Yace, eh wani bawan Allah ne ya gayyace mu shan ruwa. Can mukaje. Tace ok. 6⃣1⃣Sun danyi shiru na wasu 'yan daqiqoqi, kafin Mimi ta kori Shirun da cewa, mun kalli tafsir dinka, yau kayi qoqari. Yace, to nagode. Wayarsa ta soma ringing. Ya dauka tare da sallama. Ta amsa, macece. Yana qoqarin tambayar wacece, sai ta katseshi da cewa Malam mun yini lfy? Yace lfy Qlw. Tace dama Malam ba kira ne in gaisheka. Wani haushi ne ya tirniqe shi a zuciya. "Amma don Allah kaiki sake kirana." ya kashe ba tare da ya jira jin amsarta ba. Mimi ta kalleshi, "wacece?" shima ya dubeta, "Nima bansan ko wacece ba. Tace, ina ta samu number dinka? Yace ina zan sani? Kinsan Allah, khadija abinnan yana bani haushi da Mamaki. Wai mata masu daraja da aka sansu da kima shine suke tallar kansu ga mazaje. Kafin tace wani abu, sai daya wayar ta soma ruri. Tamkar kada ya dauka, amma saibya daga, kamar yadda yayi zato itama macece. Kamar ya kashe, saidai ya fasa, ya amsa gaisuwar da takeyi masa a qagare. Tace, din Allah Malam zanyi talbaya ne akan bashin azumi da nasha, gashi har wani azumin yazo. Jin cewa ita neman fatawa takeyi, sai ya saurareta, yayi mata kuma cikakken bayani yadda zata gamsu. Mimi dai tana kallon Ismail cike da birgewa. Duk abinda yayi sai taga yayi masa kyau. Ya kalleta. Bari inzo in tafi. Tace da wuri haka? Yace dama nazo ne in duba ku. Akwai wasu litattafai da zanyi nazari, sannan zan qara karatu a gurin Malam, duk a daren nan. Tace ok. Yace, babu wani abu ko? Ta girgiza kai, tare da fadin babu jolai. Yace shikenan in tafi sai gobe kenan? Ta daga kai. Ismail ya soma karatun nan da qafar dama inji hausawa. Domin kafin azumi ya raba, saida labarin basirarsa da hikimar wa'azinsa ya watsu cikin birni da qauyukan katsina. Faya-fayan karatunsa da kasina naji dana gani, sun fantsama a kasuwa. Su kuwa wasu shaidanun matan, labarin kyawunsa sukeyi, da yadda yake shigarsa ta manyan kaya da kuma jallabiyu 'yan gske. Wasu kuma yadda yake fitar da larabci da turanci tamkar yarensa shi ke burgesu. Kai ko hausa Ismail keyi zakaji hausarsa mai burgewa. Wasu kuma suce, iyayi da salo. [25/09 9:26 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 6⃣2⃣Masallacinsu kam yana cika tantsam har ta harabar makarantar. Ganin haka sai Ismail ya kawo ma manyan malamai dasu Malam Aminu shawarar cewa, me zai hana su kafa asusun marayu don taimakon marayun dake unguwarsu da maqotan Unguwar. Suka amince. Shida Mahmud suka soma bada tasu gudunmuwar har yace ga ta yayarsa da kuma matarsa. Shi kuwa Mahmud harda ta dansa mus'ab ya saka. Daganan sai Ismail yace yanason kowa ya saka tashi sadakar a ranar na duk abinda Allah ya hore masa. Ranar dai yayi wa'azi ne akan falalar dake cikin taimakon marayu da tsabar ladar da hakan ke dashi. Kafin wani lokaci mutane sukayi ta zuba kudi, wadanda kuwa basuda shi sukayi alwashin kawowa gobe. Kafin sati daya saida takaisu ga bude asusu a Banki. Sbd, wadanda suke kallon wa'azin a TV kuma suna son su bada tasu sadakar. Wannan al'amari ya haskaka Ismail, amma dukda haka bai kasance daga cikin malaman da in daukaka tazo musu, zakaga sunayin girman kai ba. Yana bin duk malamin daya san zai samu qaruwa dashi, ko da kuwa ya girmi malamin. Hakanan ko qaramin yaro ya nuna masa kurensa a harkar karatu yana kar6a. Sannan ko yau yayi tafsir, bayan ya tashi wani yace masa, jiya fa kaza ba daidai bane, in ya dawo gobe zaiyi bayani cewa jiya nace kaza, ba daidai bane, wani dan uwa yayi min gyara. Haka nan shi yayi imani cewa, daukaka ta Allah ce, ba wai iliminsa ne ya kaishi ba. Daukaka daban, ilimi da hikimar wa'azi daban. Ismail ya zama cikin uzurin da sai yayi kwanaki baije gidansu Mimi ba. Ita kuwa Mimi sai take zargin ko don yaga ya soma zama wani abu shine zaija baya dasu. Yau kwana uku tanason ganinsa don taji wacece matarsa din daya bada sadaka harda ita. Amma baizo ba, saidai su ganshi a TV in yana tafsir ko lacca, wadda aketa faman gayyatarsa. Yana yiwa maza ko mata, wata lacca da aka nuna yayi wa mata mai taken Ramadan lacca. Tasha mamakin yadda yake fadawa mata su riqe mazajensu, da hanyoyin kula da miji. Ya kuma kwadaita musu irin romon ladan da zasu samu a gurin mahaliccinsu. Sai taga duk ta zama wata sokuwa, domin ita kanta da take macen bata san abubuwan dashi ya sani ba, na game da yadda ita kanta mace zata kula da kanta. Ta jima tana Mamaki, kuma ta sake yarda Ismail ya dara kallon da takeyi masa.6⃣3⃣Shikam Ismail yakan kira yaya Amina su gaisa, yaji lafiyar Mimi a gurinta, kuma tana sanar da Mimin, domin bashida lokacin kansa. Ba su suka ga Ismail ba, sai azumi yana ashirin, misalin qarfe uku, lokacin Ummi tana daga citta zata kai niqan geron kunun tsamiya, ta gai dashi. Ya amsa tare da cewa, ina mamanki? Mimi qin dago kai tayi. Ummi tace, tana ciki. Yaya ce ta fito tana fadin dan gyangyadi ne ya soma dauka ta, sai kuma naji muryarka sama-sama. Yace, nine kun ganni sai yau. Ya

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37