Skip to content

Chapter 21

Chapter 21

Canjin Rayuwa Book Four Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
Download Book

saci kallon Mimi, cikin zolaya yace, 'yar amanata ma na lura fushi takeyi dani. Ko kallo ban isheta ba. Mimi ta dago ta dubeshi, ya dan rame, hakan sai ya qara masa kyau. Shaddar jikinsa mai tsada ce sosai, mai ruwan siminti, hular kansa ta dace sosai. Ta maida kanta taci gaba da firar dankalin da dama shi takeyi tun kafin ya shigo. Ta kammala ta kwashe 6awon sannan ta kai kicin ta wanke hannunta, duk yana kallonta, suna 'yar hira da yaya. Ta zo ta shige dakinta. Ya bita tare da cema yaya, bari inyi lallashi. Can saman Gadonta ta harde qafafun ta. Ya shigo da sallama,a ciki ta amsa. Ya tsaya a gaban gadon, "yau fushi kkyi dani? To, kiyi haquri. Ya ranqwafo tare da sa hannuwansa duka biyu ya dafa gadon. Kinji. Sam ta kasa fada masa cewa, rashin ganinsa ne ya bata haushi. Sai ta kauda kai. Yace, kullum ina fada ma yaya ta gaisheki, sannan ina fada mata uzururruka na, ko bata fada miki? Ta turo baki, ni fa rashin zuwanka bai dameni ba. Cewa din dakai ni matarka ce. Ya zauna, na fada a ina? Cikin salon shagwa6arta ta nuna TV, "anan mana, daka bada sadaka, harma kace, da na yaya. Yayi murmushi, yana son salon shagwa6arta. Yace amma nace matata khadija? Ni fa nufina wadda zan aura. Ta ware idanunta ta kalleshi, zakayi aure ne? Yace eh mana insha Allah. Ta ta6a baki tare da cewa, Hu'um! Zuciyarta fal da takaici. Ta dubeshi, "to ni yaushe zamu rabu? Tayi tambayar cikin daurewar fuska yace, kinsan dai ko ba lokacin azumi ba, laifi ne mace ta nemi a sake ta, babban laifi ne ko!? Ta sake turo baki, ai shi ma alqawari cikashi abu ne mai kyau ko? Yayi murmushi, "haka ne, amma banda haramtaccen alqawari. Ina nufin kayi alqawarin laifi. Misali mutum ne yayi alqawarin aikata wani laifi da Allah baya so, to ba'ason ya cika. Tace, jiya fa naji kana cewa saki halasne, a cikin tafsirinka. Yace, sai kuma nace me? Allah baya sonshi, dukda halas ne. Na lura in kinyi ilimi nan gaba za'ayi fama dake kema.6⃣4⃣Yasa hannu cikin aljihu ya ciro kudi 'yan dari biyar-biyar. Yace zan sallameku sbd batun sallah dake gabatowa. Tace, ai yaya zaka bawa kudi. Ni ina zuwa kasuwa? Yace, nima bance kije kasuwa ba ai. Tace, to naga zaka bani kudi ne. Yace na fasa baki ki shirya gobe muje tare. Tace, kana son sole sai wanda ya sanni ya ganni kai kam. To shikenan, ki rubuta min abinda kk so. Ya miqe ya shiga dakin yaya ya qirga dubu goma ya bata, yace ta saima yara kayan sallah. Tayi godiya tare da cewa, kaima da kk fama da kanka. Kaima fa dalibi ne har ynxu. Yace wani bawan Allah ne ya sameni nayi masa bayanin yadda zai fidda zakkarsa, shine da ya cire ya bani. Yaya tace, Allah ya taimaka. Ai ranar da kayi wa'azin zakkarnan, dole zukatan mutane su raunana, indai da sauran imani, su fito da zakkar su ba da. Yace kinsan kudi shiga zuci ne dasu. Sai su dinga ganin kamar in sun bada zakka kudin zai qare. Ba su san in sun cire haqqin Allah daga cikin dukiyarsu ba, Allah zaisa musu albarka, qila ma tafi ta da. Tace, rannan ma munji ka bada sadaka harda mu. Allah ya saka da alheri. Yace, Amin. Tare da miqewa. Ya koma dakin Mimi, "bani in kin rubuta. Ta miqa masa 'yar guntuwar takarda. Ya amsa, ya bude. Sai yaga ta rubuta cewa, duk abinda ya sauwaqa. Ya kalleta, zuciyarsa dajin dadin hakan da tayi. Yace nasan ba zan iya sai miki abinda kk so ba, amma zanyi iyakacin qoqarina. Ya juya ya fita. Kwana uku bayan nan, Ismail yazo Gidan da safe, misalin qarfe takwas, Mimi tana varcin safe. Ya gaisa da yaya sannan ya shiga dakinta. Bai mata dogon kallo ba, ya aje ledar hannunsa ya duba durowar gefen gadonta ya dauko takarda da biro ya rubuta cewa, ga kayan nan, in kin farka ya ke mai yin kyau a varci. Ya dora takardar a tafin hannunta. Sannan ya fice, yayi sallama da yaya ya wuce. [25/09 9:28 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 6⃣5⃣Mimi kuwa tana farkawa taji da abu a hannunta, sai ta duba, taga abinda ya rubuta. Sai tayi murmushi tace, waton in idanuna biyu banida kyau, amma a varci inada kyau. Ta dauki ledar ta bude, wani tsadadden leshi ne mai kalar 6awon dorawa, sai Atamfa 'yar England sai takalma masu kyau da tsada. Ba anan tasha mamaki ba, saida taga irin man shafawarta da hodarta, sai kuma jan bakin da take shafawa. A fili tace, "ina Ismail yasan wadannan? Lallai zan tambaye shi inji. Ta ciro hijabai dogaye guda uku, sai niqabi guda daya. Tace, wai harda wannan yakeson in sa, ta6! Na dai saka hijabin in zanyi sallah. Ta kaima yaya ta gani. Suka tayata murna. Tace, in yazo anjima sai ince yakai dinki ko? Yaya tace, eh kam ya kai don inda na kai nasu Ummi macece, kuma ba wani qwarewa tayi ba. Dama su Ismail sun kafa kwamiti qarqashin jagorancin Mahmud inda za'a dauki sunayen marayun Unguwar, da na kusa dasu. Don haka sai suka sai kayan abinci dana sallah na yara, maza da mata. Sannan sukaje suka kai ziyara gidan yari, inda yayi musu wa'azi tare da basu taimako. Ana saura kwana biyu sallah, ya kawo masu Mimi cefane jibgi guda, da kuma kaji, sannan Washegari ranar jajibiri masu hali sukayi ta aiko masa da nama cikin manyan ledoji. Yaba Malam Aminu, harda Mahmud, sannan ya miqa cikin gidansu. Irin wadannan abubuwan suna burge Mimi.6⃣6⃣Hasana da usaina suna zaune suna kallon rufe tafsir din Ismail, Hasana tace, kai Malam yayi wlh! Na qosa daddy yayi mana izinin zuwa muga sis Mimi. Itama nasan ynxun ta hadu. Usaina tace, ai na dauki number din da ya bada wadda yace mutane suyi message kawai banda kira in sunada tambaya, so muyi masa text cewa, mune. Sainya fada mana gidansu, sai muje muga sis Mimi. Muryar Hajiya sauda ta katsesu da cewa, Allah yasa in samu labari. Wai ba ku nace ma tana lfy bane. Kuma fa na fada muku cewa, akwai matsala in munyi yunqurin zuwa gurinta zata sake guduwa. Karku damu tunda muna samun labarinta. Muyi ta Addu'a komai zai wuce. Hasana tace, Hajiya shi Malam a matsayinsa na Malami ba sai ya nemi lambarki ba kiji komai daga bakinsa? Usaina tace, ya fa san nan gidan meyasa ma ba zaizo ba? Hajiya sauda tace, Nice da laifi, don na tura masa saqo cewa, naji dalilan mahaifin Mimi, kuma na gamsu dashi. Don haka nima zaka jini shiru. Kaima kayi haquri karka sake nemana ko a waya. Ina mai sake baka amanarta. Lokaci yana zuwa da zamu nemeka da kanmu. Kunji tun daga lokacin ban sake nemanshi ba, shima bai sake ji daga gareni ba. Hasana tace, to sai zuwa yaushe ne sannan za'aje gurinta? Usaina tace, ke kam kamar bada hausa Hajiya tayi magana ba? Hajiya sauda tace, zaku soma musunku ko? To ni nayi nan! Ta nufi kicin. Ranar sallah, Ismail ya matsawa Mimi wai ta shirya suje masallaci. Da ma tun ranar

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37