Chapter 8
Chapter 8
inna cewa, matarsa zata koma gidansu yaya Amina, sbd zasu tafi makaranta. Tace, "sbd nan din ba za'a kula da ita ba? Yayi murmushi, don dama ya zaci zata fadi haka. Yace a'a saboda bata gama samun sauqi ba. Tace, Allah ya taimaka. Yace, Ameen. Haka kuma da dare ya samu 'yan uwansa mazan ya fada masu. Suma sai suka ce, hakan yanada kyau. A daren suka kwashe kayansa da Mahmud tsaf. Sannan washe gari ya kama ta Suka shiga cikin gidan tayi musu sallama, dukda dai ba kulata suke ba, sai wanda yayi biyya yake leqawa dakin yayi musu sannu. Tayi mamakin ganin dakin haka don gsky bata zaci dakin yayi kyau haka ba. Ta kalli Ismail, nagode da kulawa. Sannan tace ma yaya Amina taba ta Ummi su dinga kwana. Yaya tace gatanan. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 2⃣2⃣Shi kuwa Ismail daya koma ya kwanta a dakinsa kan katifarsa, sai yakejin dakin yayi masa girma. Zuciyarsa ta cika da kewar Mimi. Itama a nata 6angaren haka ce ta kasance, juyi kurum takeyi tana kallon Ummi wadda keta sheqa varci. Gizo Ismail yakeyi mata, sai taga kamar gashi yana sallah. Koda ta tabbata ba wai tanason Ismail bane, amma yana da dabi'un da take matuqar so, suke kuma burge ta. Yanada tausayi, ga gsky da Amana. Shine mutum na farko wanda ya kasance mai addini kuma yake birgeta. A da in taga ustaz kamarsa, sai ta dinga yi musu kallon 'yan kauye wadanda basu waye ba. Haka kuma yana burgeta Kasancewarsa tsayayyen namiji, wanda baya daukar raini, gwarzo mai tsayawa da safafunsa. Don duk lokacin da ta tuno da yadda suka yita takun saqa dashi, tana jinjina masa, domin ko a gabanta bai ta6a shakkarta ko nuna Tsoronta ba, kamar yadda sauran mazaje da yawa sukayi a baya. Ta tuna irin yadda tayi ta wulaqanta samari 'ya'yan manyan mutane, wadanda suka nuna cewa suna sonta. Kai ko khalil dinta ya wulaqantu kafin ta soma sonshi, kuma har zuwa lokacin da ya rasu, bai daina shakkarta da tsoronta ba. Tasan cewa da ya kasance mijinta, babu shakka za suyi zama ne na sai yadda tayi. Domin ba zai iya juya ta ba. Da wadannan tunanukan varci yayi awon gaba da ita. Shikam Ismail bayan ya dawo daga masallaci sallar asubahi, saiya nufi gurin malaman da suke daukar karatu. Daga gurin karatun ne ya nufi gidan yaya Amina. Lokacin abbansBBCu saddam shima zai shiga Gida. Suka gaisa, cikin salon tsokana abban saddam yace, kazo duba ajiyarka ne? Ismail cikin dariya yace, kuma fa kamar hakane. Tashin Mimi kenan daga varci, tana tunanin da suna tare da Ismail da ynxun ya kaita ban daki, sai taji Sallamar sa. Da sauri ta koma ta kwanta don taga me zaiyi. Yaya Amina tana kicin tana dora ma yara ruwan wanka, suka gaisa. Yace, 'yar amanata ta tashi kuwa? Yaya Amina tace, leqawata biyu bata farka ba. Yace, kinsanta sarkin varci ce dama, ko gajiya batayi. Yace, bari in tasheta tayi sallah. Yaya tace, "to" amma tasan cewa mimin tana fashin sallah, domin jiya da dare bayan tafiyar Ismail ta tambayi yaya audugar mata. Yaya kuwa da kanta ta fita zuwa shagon Bello ta siyo mata. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 2⃣3⃣Ya jima tsaye yana kallonta, sannan ya dauko kujerar gaban madubi, yazo bakin gado ya zauna. Babban yatsan safarta ya kama ya dan ja. Dole tayi motsi, domin taji dan zafin qafar. Yace, ki tashi kin makara, kiyi sallah. Ga Ummi har ta tashi tayi nata. Tace, cikin salonta na shagwa6a "nifa ba zanyi ba yau. Ta sake sunne kanta cikin filo don kunya. Ya gane batunta, cikin sigar tsokana yace, wai, wai, wai, shine baki fadamin ba in sai miki biredinku na mata? Koda yake naga ba kiyi ba muna asibiti, sai na zata baki fara bane. Ta dago, tayi masa wani kallo, meke daukeni ne? Ya kashe ido daya, "Baby mana. Ta tashi zaune, me kace? Kada ka manta fa naje jami'a. Yace, haka fa, kinje jami'a, na manta sam, shekarunki nawa ne ma? Ta gano so yake yaji shekarunta, don haka tace, ba zan fada maka shekaruna ba, sai dai ranar zagayowar haihuwata. Tace daya ga watan daya. Yace tabdi! Gsky ke ta musamman ce, to bari in kalleki in fadi 'yan shekarun naki, don basuda yawa. Tace, fadi muji. Yace sha takwas, sha tara, ashirin, in na cika miki kenan. Ta dan zaro ido, alamun aciki ya fadi daidai, amma sai ta wayance da cewa, sam ba haka bane, baka canka ba. Yaya Amina ta katsesu da sallama suka amsa, tace, khadija ga ruwan wanka can muje in kaiki ko? Ismail ya miqe "to nima bari in tafi dama nazo ne mu gaisa. Yaya Amina tace, kardai ka manta da sandar da za'a sai mata ta tafiya, tunda sunce zai taimaka mata sosai gurin tafiya da sauri. Ismail yace, ai kuwa nagode, shaf na manta. Anjima zamuje asibiti da Mahmud. Haka kuwa sun sai mata sandar. Kwanci tashi, babu wuya har anzo jajibirin tafiyarsu Ismail. Kafin ranar tafiyar dama ya zaga duk 'yan uwansa mata, yayi musu ban kwana, domin shi harga Allah yanason 'yan uwansa mata, yayi musu ban kwana, domin shi harga Allah yanason 'yan uwansa. Kuma yana sha'awar suyi zumunci. Wadanda basuje asibiti duba su ba, sai 'yan kame-kame gami da ban haquri yace, babu damuwa Allah ya bada ladan niyya. Haka nan yaje Daura, yayi bankwana da dangin mahaifiyar sa. Ta kano zasu tashi, don haka tun ranar jajibirin zasu tafi kano din tare da Malam Aminu. Sai yaga tashinsu sannan zai dawo. 2⃣4⃣Sun gama shirinsu tsaf, Ismail ya shiga don yin bankwana da matarsa da kuma yaya Amina. Ya dauko wayarnanda ya ta6a saima Zainabu yazo ya samu tayi aure, ya bawa yaya Amina, yace, ya dinga kira don jin lafiyarsu ba sai ya dami abbansu saddam ba. Mimi tana kwance akan gado Rigingine, ta tasa tulin littafin daya sai mata, sai dai duk na addini ne, bai sai mata novels dinba, waishi baisan ina ake saidawa ba. Yace, ta karanta wadannan don tafi buqatarsu ynxun, kuma kinga duk na turanci ne, tunda kince hausa tana baki wahala. A sanyaye yace khadija! Ta kalleshi, yace munfa shirya zamu wuce. Malam da abokinsa da kuma Mahmud zasu biyo tanan ynxun mu wuce. Ta dubeshi, "tam shikenan sai kun dawo, kamar zuwa yaushe kenan zaku dawo? Yace, sai dai munje muji lokacin da suke samun hutu. Ai zan dinga kiranku muna gaisawa. Tace, am nayi zaton kafin ka wuce zaka sakeni? Gaban Ismail yayi wata muguwar faduwa, har taso ta gane. Amma sai ya wayance tare da yin dan yaqe, "kinada gurin da zakije ne kafin in dawo? Ta kalleshi "a'a" yace to kada kiyi gaggawa, wannan kibar zancen, sai in nazo hutu, sai muga yaya za'ayi ko? Tace shikenan, Allah ya taimaka, ya kaiku lfy. Ta koma ta kwanta. Ya dube ta, "babu rakiya? Tace ka manta banida qafa? Yace, shikenan kiyimin Addu'a sai munyi waya. Su yaya Amina ce da yaranta suka rakashi lokacin da su Mahmud suka iso. Suna tsaye har saida motar ta 6ace, sannan suka koma Gida. Suna idar da sallar asubahi, jirginsu Ismail ya daga, su Malam suka dawo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37