Chapter 19
Chapter 19
ta6a yin tafiya kamar ta yau ba fa. Nayi qoqari mana. Yace, ba zamu samu mota ynxun ba, kuma ko da mun hau mota, inda za'a sauke mu da nisa, tafiya sosai kafin aje gidanku, sai dai in aca6a. Tace eh naji mu hau aca6a din. Yace, ni banason mata suna hawa aca6a. To ka siya mana mota mana. Yace lokaci ne, insha Allah. Mahmud ya fito, "har ynxun baku tafi ba? Ismail yace, tana nan tana shagwa6ar ta, ba za ta iya zuwa gida a qafa ba. Mahmud ya miqo ma Ismael makullin mashin dinsa, tare da cewa, kuyi amfani da mashin dina tunda ban kaiku nisa ba. Kuma ga hadari yana haduwa. Ismail yace, to kar ruwa ya sameka fa. Mahmud yace, ko ya sameni kaga ni daya ne. Ismail ya amsa, tare da fadin shikenan muje ko? Tace, yaya zan hau? Ka san fa sau daya na ta6a hawa mashin, lokacin zanje in samu khalil a gareji. Saboda sauri ban san ta yaya na hau aca6ar ba, na dai ganni akai. Ina tsoron mashin da yawa. Yace ki dafa ni ki hau. Ta dafa shi ta hau suka soma tafiya. Don ya tsorata ta, sai ya taka birki, a tsorace ta qanqame Ismail, tana salati. Ya sa dariya. "Ya kamata ki rage tsoro. Ita kam batasan ma yana yi ba. Illa hannuwanta da tasa ta zagaye cikinsa ta riqe gam. Sannan ta kwantar da kanta a Gadon bayansa. Wani irin nishadi Ismail ya tsinci kansa aciki mara misaltuwa. Don haka maimakon ya nufi Gida kai tsaye, sai ya dinga shawagi ta layuka, sannan ya sassauta gudu, iga iskar hadarin tana ta kadawa, sai Ismail ke ganin kamar su kadai ne a garin katsina da kewayenta. Ita kuwa Mimi wani daddadan varci ne taji yana fizgarta, iskar tana ratsa ta ko ta ina. Ga kuma qamshin turaren Ismail dake saka Zuciyarta shiga cikin wani yanayi mai wuyar fassara. [23/09 5:32 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 5⃣8⃣Can yace, zamuje siyen kifin ne, ko muje gida? Ji tayi tamkar suyi ta yawon su a haka har abada. Don batason abinda zai tashe ta daga yadda suke. Amma kifi fa? Sai tace zanci kifi mana. Ya karkata kan mashin zuwa Gidan suya. Gurin ya burge Mimi musamman tunda taji qamshi yana dukan hancinta. Ya kalleta, zamu ci anan ne? Tace, amma zamu yi ma su yaya Amina tsaraba in munci bamu ko? Yace, yadda kika so, tace, in ba mutane muci, sai mu sai musu nasu. Babba daya ya sai musu, sai tataccen 'ya'yan itace mai sanyi, wanda za'a taceshi a juye maka cikin kofi a gabanka. Sunaci, Ismail yana kallon Mimi, wadda ke ta yin hannu baka, hannu qwarya. Yayi murmushi, "ci sannu Dija! In bai usheki ba zan qara miki." Ya shiga salo mata tsokar kifin sala-sala, yana ajiye mata a gabanta. Ta lumshe ido, "kar kaga laifina, inason abin nan. Ta salo tsokar ita ma ta aje a gabansa, "In baka ci, nima sai ya ginsheni. Ya dauka ya saka a bakinsa. Haka sukayi ta salo ma juna tsokar kifin, suna turawa a gaban juna, har suka cinye. Suka sha abin shansu. Yace, zaki qara? Ta girgiza kai, "cikin yayi dam. Dama banci abincin dare na ba." Yace, kunyi tuwo kenan? Tayi 'yar dariya, "shine kam. Na kasa sabawa da tuwo. Shi kadai ne har ynxun bai min ba, duk a abincin mu na Hausawa. Yace yaya ta fadamin, kin kasa sabo da tuwo. Amma kikanci kadan. Kafin tayi magana, sai sukaji iska mai qarfi alamun tasowar hadarin. A tare suka miqe, da sauri, ya biya sannan suka dauki nasu yaya Amina suka dane mashin. Fatansa tayi irin zaman dazun wanda itama hakane muradinta. Tana lafe a bayansa suna keta gudu, sai ko ga ruwa mai qarfi ya sauka. Sake qanqameshi tayi. Yayin da shi kuma ya rage gudun sbd ya Kalli gaban shi da kyau. Sha biyu da wasu abubuwa suka tsaya a qofar Gidan su yaya, sun jiqe sharkaf. Ya sauka ya buga gidan sosai, kafin suka ji takun Abban su saddam. Sai da ya tambaya wanene? Ismail yace, mune. Sannan ya bude. Mimi ta kalleshi, "kazo ciki mana ruwa yayi sauqi! Yace karki damu, gara in tafi sbd dare zai qara yi. Abban saddam yace, to ka kwana mana anan? Yace, a'a duk na jiqe kayana suna gidanmu. Saida safenku. Ta daga masa hannu tare da fadin bye! Sai da yaga abban saddam ya rufo qofa, sannan ya wuce. Ita kuma tana shiga taba abban saddam ledar tsarabarsu. Yace, bari in taso miki Ummi, don irinki ce, sarkin tsoro taqi varci a dakinku, wai ita kadai. 5⃣9⃣Bayan ta kunna tocila, sannan ta rufe qifar, ta cire kayanta ta maida na varci. Tayi lamo akan Gado, sam varcin yaqi zuwa mara. Sai tuno yadda suka kasance da Malam takeyi. Bata ta6a jin a kafatanin rayuwarta irin na yau ba, domin batasan ya zata fasalta yadda taji ba har a fahimce ta. Saidai a can qasan Zuciyarta tana tambayar kanta shin yadda ta ta6a jikin Malam ya dace, su da zasu rabu? Ta sake yin juyi akan gadon tare da maqale filo, sbd sanyin da taji yana ratsata. A fili tace, kai gsky bayansa yafi katifar nan dadin varci. Wata zuciyar tace, ba wani laifi domin har ynxun mijinki ne, tunda baku rabu ba ai. Haka tayi ta tunani tare da surutai barkatai har varci gwanin iya sata yayi gaba da ita. Washegari yaya tayi ta ma Mimi tsiya, tana cewa, mun zaci ko kun kama daki ne, mu biyo ku da kayanku? Mimi tace, munje siyan kifi ne ruwa ya tare mu. Tace, muma munci kifi, gsky sun iya gashi. Dariya kurum Mimi tayi. Tun kwanakin baya Mimi tana yawan tuno mahaifanta, haka kuma har abada ba zata manta da gatan da dadynta yayi mata ba. Kewar ganinsu takeyi. Sau da dama takan zauna daki taci kukanta ma'ishi, ta share hawaye, saidai tanajin kunyar tunkarar mahaifinta sbd ta kasa yi masa abinda ya dace, a lokacin daya dace. Duk da cewa ya nuna wa momy Nafisa cewa zai haqura in taqi yarda kamar yadda Momyn tace mata. Amma ita ta yarda cewa tafi kowa laifi don me yasa ba tabi abinda yace ba tun farko? Don haka ta tattara duk wasu laifuka ta dora a kanta. Sannan zata jira lokacin da Allah zai sake hadasu don ta roqesu gafara. Kwanaki biyu da fara azumi, Mimi tana zaune a saman gadonta tana karatun littafin tahzib mai fassara da hausa, duk lokacin da take karanta littafin dashi da Al'adab, sai ta dinga tunanin cewa gsky rayuwar da tayi ada, rayuwa ce irin ta dabbobi, tunda batasan komai game da addininta ba. Abinda ya kamata ace ta sani tun tana ajin rauda shine take karantawa ynxun. Bokon da dauka a matsayin wayewa, ashe qauyanci ce ga wanda baida ilimin addini. Duk ilimin Bokon da take taqama dashi, wani lokacin Ummi ke cinta gyara a fannin addini. Kai ta fahimci ko maganar fatar baki ta mai ilimin addini ta bambanta da ta mai taqama da boko. [23/09 5:37 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 6⃣0⃣Ummi ta katse mata tunani da cewa, kunna TV dinki kiga kawunmu yana yin tafsir. Sai tsalle Ummi keyi.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37