Chapter 17
Chapter 17
rayuwa. Kan Alhaji Bashir ya kulle, kenan ya daure ma dansa gindi yayi duk abinda yakeso, kuma bazai iya hanashi sa6ama Allah ba kenan? Minister ya katseshi da cewa, nayi zaton zakayi min magana akan hauhawar farashin man fetur ne? Alhaji Bashir yace, a'a ba wannan bane. Shi kenen saida safe mayi maganar kasuwanci, in Allah ya tashemu lfy, minister yace, Allah ya kaimu. Kada kasa kanka a damuwa game da batun wadannan yaran. [22/09 11:55 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 5⃣1⃣Kwana Alhaji Bashir yayi da abin a ransa. Washegari ya nufi katsina. Tun saukarsa hajiya sauda ta karanci damuwa can qasa tare dashi. Amma data tuntu6eshi, sai yace, wai babu komai. Ta takura masa da tambaya don ta fada masa cewa, saidai inba zai fada mata ba, to ba zata takura masa ba. Amma batun matsala tabas tasan yana ciki. Sannan ya fede mata komai. Yace, ni damuwata ban san ta ina zan 6ullo ma lamarin ba. Hajiya sauda cikin damuwa tace, dama Alhaji baku binciki halinsa ba? Yace, ni ina na wani bincika. A zatona yayi tarbiyyar 'ya'yansa, nayi hasashen sunada lfy tamkar nawa. Ashe nayi kuskure. Shi kansa ministan, sai ynxun nake sanin nasa halayen, sbd haduwarmu babu dadewa muka qulla wannan auren. Hajiya sauda tace, duk abinda ya faru, da kuma wanda zai faru nan gaba, duk laifinka ne, kai kawai ka duba abinda zaka samu ne kawai, ka dauki 'yarka ka bada. Yace, sauda abinda ya faru, ya riga da ya faru, sai dai a kori gaba. Ni ynxun roqo na a gurinki, ki bani shawara, domin kaina ya riga ya kulle. Hajiya sauda tayi shiru, tana tunanin me zatace. Gashi dai lokacin da za'a qulla abin ba'a nemi shawararta ba, sai ynxun da za'a kwance shi. Tanason ganin mijinta cikin kwanciyar hankali, musamman shida ke fama da ciwon suga. Don haka ba tare da ta tuno masa wani abu da yayi mata abaya ba tace, shawara dai daya ce, tunda shi uban yaqi kuyi batun, ka samu shi abbas din kuyi magana. In har baya sonta, da zaman uquba gara su rabu kawai, Allah ya hada kowa da rabonsa. Yace hakane kawai mafita, ai nayi da na sani babu adadi, har ina tozarta Mimi, ina cin zarafinta, ashe ba dan mutunci bane, kuma bai fito daga cikin mutunci ba. Hajiya sauda tace, kuskure ne dai ya riga ya faru, sai dai muce, Allah ya tsare gaba. Kwanansa uku ya koma Abuja sbd kawai ya gana da Abbas. Da safe Abbas ya sameshi a Gida. Bayan sun gaisa, yace, na kiraka ne don muyi magana ta fahimta, ni da kai. In har kana ganin bakason Na'ima to kawai ku rabu. Allah ya raya muku danku. Abbas yace, daddy ka samu daddy na kuyi magana, kamar yadda kukayi lokacin da zaku qulla auren, in ba haka ba zaice nine na saketa sbd banajin maganarsa. Alhaji yace ni zan masa bayani, abinda nawai nakeso shine ka fadamin abinda ke ranka Abbas yace, daddy nima inason a rabamu. Alhaji u, shikenan jeka zanyi magana da Dadyn naku. 5⃣2⃣Sai dai duk yadda Alhaji Bashir yaso suyi maganar da minister sam yaqi. Ransa ya 6aci sosai. Don haka ya taka har gidan Abbas ya samu Na'ima, ya tambaye ta ko akwai wani canji tsakaninta da mijinta? Tace, babu wani canji, domin ynxu ko wace irin mace kawowa yakeyi, kuma dole inyi musu girki, sannan ya daukarmin yaro ya kai musu shi, kowace jaruwa tayi ra daqunarsa. Yace, dauko mayafinki da kayanki kizo muje gida. Wannan shine mafarin tsiyar data 6arke Tsakanin Alhaji Bashir da minister. Qiriqiri minister yace, shifa bai yadda da wannan hukuncin ba, saidai inta koma can Gidansa da zama har zuwa lokacin da zata yaye jikan nasa, tabashi abinsa. Alhaji Bashir yace, wannan kuma wani abu ne da ba zai yiwu ba ko a cikin mafarki. Buqatarsa kawai Abbas yaba 'yarsa takarda, in ta yaye dansu, suzo su dauka. Wannan rigima itace ta datse kasuwancin da suka qulla suke aiwatarwa. Ikon Allah kenan. Shiyasa akace, komai mutum zaiyi, tofa yayishi don Allah. Masu son Zainabu sunata fitowa tun daga lokacin da ta haifi danta saurayi, amma kowa fada masa takeyi tanada wanda takeso, duk da cewa ba tada tabbaci akan samun wanda takeson, ko inda yake bata samu labari ba, bare tasan ko zata samu shiga. Amma begensa yananan cikin Zuciyarta, dashi take kwana, tana tashi. Bugu da qari, dole inna ta zuba mata ido, sbd tsoron hukuma, duk da irin son kudinta. Ita fatanta Zainabu tunda ta haufi danta lfy, ta samu miji ta qara gaba, ko bata yaye danta ba. Su kuwa mutan madina suna can suna ta karatu, babu ji babu gani. Ismail ya qware sosai a fannin tafsiri, yana da haddar litattafai da dama a cikin kansa. Malamansu suna jinjina ma Qwaqwalwarsa sosai. Sun sake samun wani hutun, lokacin Rabi'a matar Mahmud tanada tsohon ciki. Wannan hutun sun sameshi daf da azumin watan Ramadan. Sunso tsayawa, amma sai Malam Aminu yace, su dawo sbd shine sukeson ya gabatar da tafsir a sabon masallacin da aka gina nan Unguwar su. Masallacin Juma'a ne katafare. Kuma lokacin azumi za'a budeshi. Don haka suka nufo gida cike da doki, sbd shi Ismail mutum ne maison ganin yana daukaka kalmar Allah, kuma jama'a su qaru da iliminsa. [22/09 4:38 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 5⃣3⃣Wannan karon sun sauka cikin shirye-shirye sbd karatun azumin da zasuyi. Sam bai zauna dasu Mimi ba. Tun ranar da suka iso suka gaisa, ko kan kayansa bai dawo ta kansu ba, sai dai suyi waya da yaya. Sai ana sauran kwana biyu Azumi, sannan ya samu zuwa gidan yaya Amina, ya kwance kayansa ya basu tsarabarsu. Ranar ma dai bai zauna ba, sbd yana shigowa, Mahmud ya kirashi ya sanar dashi cewa, Rabi'a tana kan gwiwa. Da sauri ya fita ya samu Mahmud din a qofar gidansu Rabi'a. Fada ya rufe Mahmud din dashi kan cewa a fito da ita akaita asibiti. Zasu tafi nemo mota kenan, saiga wan rabi'a ya fito daga cikin gidan, cikin murna ya fada masu cewa, ta sauka, kuma an samu da Namiji. Murna gurin Ismail tamkar tashi matar ce ta haihu. Da dare ya shigo Gidan su yaya Amina, Aishatu ce kadai a tsakar gidan tana ta wasan ruwa, yasa hannu ya dauketa cak. Yayi sallama a qofar dakin yaya, tana sallar isha'i, yace Ummi yaya kk barta ita kadai a tsakar gida tana ta wasan ruwa duk ta jiqa jikinta. Tace, nima ina sallah ne kawu. Ynxun na ida. Ya miqa ta ,amsheta kisa mata kaya. Auntynki tana ciki? Tace, tana cikin tana sallah itama. Mimin batasan dalilin dayasa ta damu da Ismail ba wannan zuwan nasa. Duk da cewa, shi sam bai damu da ita ba wannan karon, tanason yin abinda zai birgeshi. Haka wannan karon yafi wancan zuwan wayewa, da gogewar ilimi, sannan kyawunsa yafi na wancan zuwan. Ko itace ke ganin haka? Oho. Lokacin da ta jiyo muryarsa, saita samu kanta da fesa turare a jikinta da kuma dakinta, ta zauna a bakin gado. Sai Zuciyarta ke tambayarta wai sbd me tayi hakan? Kafin ta lalubo amsa, har yayi sallama, ta amsa. Yace, in shigo? Tace ka shigo mana. 5⃣4⃣Ya shigo, cikin salon zolaya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37