Chapter 29
Chapter 29
yayi da zan warware aurenmu. [27/09 3:48 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 8⃣8⃣Ta daga masa hannu. Don Allah ka fita! Inason inyi tunani. Yace inace kin gama tunani daga yau? Ta miqe, ta ra6a ta gefensa ta fita, qasa ta koma ta kwanta kan doguwar kujera. Murmushi yayi, sannan ya shiga dakinsa. Wayarshi ta gani da sauri ta dauka ta shiga kicin. Bata sha wahala gurin ganin sunan zainabu ba. Ta dauki lambarta. Sannan ta dawo da wayr inda ta dauka. Bayan ta shiga dakinta ma harda shiga bandaki. Layin zainabu ta kira, bayan ta daga mimi ta soma magana da kakkausar murya, "kece zainabu?" tace eh nice. Dama na kiraki ne in fada miki cewa ki fita harkar mijina, in har kinason zaman lfy. Zainabu tace wai waye mijin naki? Mimi taja tsaki, "kinsanshi tunda har kina shirin aurensa. Zainabu tace, oh wai kina nufin malam? In shine sai ince kinyi kuskure. Domin aurensa shine abinda nake buri koda zaki zama ajalina. Ki sani kafin ya soki, ni ya soma so. Kuma ina sonshi, aure babu fashi! Mimi tace, mu zuba! Ni dake zanga wanda keda nasara! Ta kashe wayar, sannan ta fito daga ban dakin, ta jefa wayarta akan gado. Ta shiga yin kai kawo a tsakar dakin. A fili take fadin, wai meyasa ni bana burgeshi ne? Dame zainabu ta fini ne? Ta janyo hijabinta da niqabi ta saka, sannan taja durowa ta dauki kudi ta nufi qasa. Bata zaci yana qasan ba. Saida taji yace, ina zaki? Ba tare da ta tsaya ba, tace gidan yana Amina. Ya daga murya. Ba zaki je ba. Ga waiwaya ta dubeshi, fuskarsa murtuk, sama ta koma fuuuu. A zuciyarta da qudirin cewa shima kuwa sai tayi masa abinda ba zai fita anjima ba. Haka suka yini kowanne zuciya babu dadi. Da dare tanata fakonsa , ya shiga dakinsa yana tashi, sai kuwa ta sauka qasa , ta dauke masa makullin mota, ga jefa qasan kujera. Sannan ta kulle qofar falon ta saka makullin cikin rigar mamanta, sannan ta koma dakinta. Tana kwance, rigingine kusan minti shabiyar, sai kurum taji turo qofarsa. Tashin da tayi da sauri shine ya kawo har yaji qaran makullin. Yace bani makullin mota dana qofar fita. Tace ajiya ka bani? Inama zakaje? Ni gsky tsoro nakeji, ba zaka fita ba. Yace, tadi zanje ki bani, karki 6atamin lokaci. Cikin 6acin rai tace, nifa bazan zauna ni daya ba. Yace to kizo muje tare. Da qarfi tace, Allah ya tsare ni. 8⃣9⃣Har inda take ya tako, daf da ita ya tsaya, ya sa hannu ya dafa kafadarta, girgiza ta yayi don yaji daga ina yaji qaran makullin. Amma sai baiji qaranba, sbd sun samu mazauni mai kyau a tsakiyar qirjinta, makari guda biyu sun taresu. Sai ya soma yi mata wani irin lalube tun daga qugunta yake shafawa da hannuwa guda biyu gaba da baya. Hakan ya kashe mata jiki, har ya tilasta mata lumshe ido, daga ita harshi. Haka nan yanajin makullin, sai ya zura hannunsa ta saman rigarta don ciro makullin. Ya ciro, amma yanayinsa gaba daya ya raunana, kamar yadda itama ta sukurkuce. Ta bude idanu ta kalleshi, shima fuskarta yake kallo. Cikin ido suka kalli juna, sannan a hankali yace, saina dawo. Ta fahimci muryarsa ta canza. Kan gado ta fada ta soma kuka. Kusan minti biyar ta tashi ta rufe qofarta. Shi kansa baisan meya hanashi yin wani zance mai muhimmanci ba, aun daiyi 'yar hira yace, zai dawo kan batun aurensu, yana sauri ne don matarsa ba tada lfy. Ta so ta fada masa kiran da matar tasa tayi mata, sai kuma ta fasa. Lokacin da ya dawo, ya hau sama, kai tsaye qofar Mimi ya murda, amma sai ya jita gam. Don haka sai ya wuce zuwa nasa dakin, bayan yayi duk abubuwan da yakanyi kafin ya kwanta, sai ya kwanta. Juyi kurum yakeyi tare da tuno yadda ya caje matar tasa. Ya gama yarda itama ko bata sonshi, to kuwa tana buqatarsa, don ya lura da halin data shiga a lokacin. Yanke shawara yayi ya tuntu6eta da batun, amma sai ta huce daga wanna fushin da tayi. Da asubahi, kamar kullum saida ya qwanqwasa mata qofa kafin ya wuce masallaci. Ita kam tuni idanunta biyu, domin dai yau duk satar varci, saida yayi mata haquri. Ta amince, baya sonta tunda har ta zubarda kimarta ta 6oye makulli, amma saida ya dauka kuma ya tafi. Zucigarta dai tanata bata shawara akan ta fito fili ta fada masa abinda ke ranta. Sai dai ita tsoronta kar sai yaji sirrin zuciyarta, sannan yace, ba irinta yakeso ba, kamar yadda yayi ta fadi a baya. Takaici ne ya hanata fitowa daga daki. Koda gari ya waye, shi kuwa shareta yayi, har ya gama komai ya fita, sai dai alamu sun nuna bata bude qofar ba, har ynxun qarfe hudun yamma. Yaje ya daga labulen windonta, tana kwance akan sallaya, da alamu tayi la'asar ne. Yace khadija, ki tashi ki bude qofa mana! Tana jinsa tayi shiru, daman so takeyi ya lallasheta, amma ko zata bude ba ynxu ba. Yace kinci wani abu ne? Bata tanka ba. Ya sauka qasa. Baisan me yarinyarnan keso dashi ba. Yau duk ta hana rayuwarsa sukuni, don koda ya fita, hankalinsa yana gida. Baisan mimi da gske takeyi ba saida yaga anyi sallar isha'i ya dawo bata fito ba. Da ya leqa ya ganta kwance rub da ciki akan gado. [27/09 9:54 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 9⃣0⃣Yace kadija ki dubi girman Allah ki bude, muyi magana. Nifa bansan dalilinki ba. Hava khadija ya kk so inyi da rayuwa ta. Ganin bata tanka shi ba, sai ya yanke shawarar kiran mahmud. Kafin isowar mahmud din, ismail yaci gaba da lallashinta, amma ko motsi batayi ba. Bataji takun shigowar mahmud ba, sai dai muryarsa taji yana cewa, don Allah khadija ki bude qofar nan, muyi magana. Don Allah zaki bude ba don ni ba. Kuma ina bayanki akan kowane dalili ne yasa kika rufe qofar. Sunfi minti biyar kafin ta taso ta bude, tana layi. Cikin hanzari ismail ya shiga ya kama hannunta. Dukda qaton hijabin sallar data saka ya hada, ya dauke ta zuwa falon qasa. Yunwa da damuwa sun hadu sun ramar da ita. Ya zaunar da ita akan kujera. Yace haba khadija kowane irin laifi nayi miki, ya dace ki yanke ma kanki irin wannan hukuncin? Cikin raunanniyar murya tace, ku barni don Allah. Mahmud yace, ka kawo mata ruwan zafi, tunda bataci komai ba, hanjinta zai warware. Ya nufi kicin ya hado mata ruwan zafi. Saida yayi ta lallashinta, sannan ta amsa tanasha. Kafin tayi rabin kofi, zufa ta rufe ta. Sannan taji qarfi a jikinta. Ta kama gefen hijabinta tana sharewa. Mahmud ya dubeta khadija bai dace kiyi irin wannan ba. Horon kanki da yunwa, wannan ba dabi'ar musulmi na gari bane. Ismail yace mema akayi mata ne? Taqi bani dama in nuna mata muhimmancinta. Kullum zancenta daya ne in saketa. Nace mata in nayi aure zanyi mata abinda takeso, kuma ynxu na soma neman aure. Sai tazo tanayin irin wannan? Sai kawai sukaji muryarta tace, duk wadda zaka aura, ka aura amma banda zainabu. Cikin sauri ya miqe, sbd me zakice haka? To ai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37