Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

Canjin Rayuwa Book Four Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

A sanyaye tace, dama kazo ka sakeni ne? Kafin ya amsa, qaramar wayarsa ta soma ruri. Ya daga ya fita a dakin yana amsawa. Mimi ta zauna tasa kanta cikin gwiwarta tana kuka. Batasan dalilin kukan ba bare asalinsa. Wata zuciyar ta ingizo ta tare da rada mata cewa, tayi tafiyarta. Ta sauka ta dauko akwatunanta, ta dauki daya, ta soma kwaso kayanta tana zubawa a ciki. Shikuwa yana gama waya ya dawo, da bango ya jingina yana kallonta. Bai hanata ba kuma bai tambayeta dalili ba, har ta gama ta dauki mayafinta tasa takalmi, sannan taja jakar, dariya ce taso ta su6uce masa, amma sai ya fasa. Ya tare qofar dakin. Tace, ka bani hanya zan wuce! Yace zuwa ina? Tace ina ruwanka dani? In tafi ko ina ma, mun hada zuri'a ne? Kawai ynxun ka bani saki na. Kai ko baka sakeni ba ma tafiya zanyi. Ya girgiza kai, bamu bada zuri'a ba, sai dai bansan gaba ba. Amma ynxun kafin ki tafi tsaya mu gama magana, in yasa sai ki tafi, ba zan hanaki ba. Ya nuna mata bakin gado, ki zauna anan! Fuskarta a daure ta zauna. Shima ya zauna. [26/09 4:09 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 8⃣0⃣Fadamin mecece damuwarki wadda tasa har zaki tafi ki barmu? Shiru tayi, domin ta rasa me zata ce. In zata fadi gsky, to kishi ne kawai ke cinye ta a zuciya. Amma sai tace, na gaji da kushe ni da kkyi. Duk lokacin da ka tashi, sai kace min mummuna. Sannan kaqi ka cika min alqawari na. Yayi murmushi, ni ban ta6a ce miki mummuna ba. Ta kalleshi, ba girmanka bane yin qarya. Domin kune masu fadin illarta. Jiyan nan kace min ko yaushe ina canzawa. Yace, canzawa nace ko muni nace? Tayi shiru. yace, banda jiya sai kuma yaushe nace miki? Cikin qarfin gwiwa tace, da muke asibiti, lokacin da nace, bana sonka me kacemin? Inka manta in tuna maka. Cewa fa kayi kaima kafison mace mai kyau. Ya sake yin wani murmushin, tabbas nace haka, amma nace bakida kyau? Tace kusan haka ne? Yace ba dai hakan bane tunda kusan ne. To naji wannan sai kuma batun alqawari, duk alqawurran dana daukar miki a gaban Doctor salis wanne ne ban cika ba? Tayi shiru, tabbas yace zai nesanta ta da iyayenta kuma yayi. Yace zai kula da ita daidai qarfinsa, kuma yayi, in zata duba tsawon lokacin da ta dauka tana jinya, sun yi ta dawainiya da ita. Ta dubeshi, sai na rabuwa, shine baka cika ba. Yace banda shi na cika sauran? Ta daga kai, alamun eh. Yace to bari in tuna miki. Kinsan na jima ina yi miki alqawarin cewa zan yi miki fiye da kk taso anayi miki na gata ko? Tayi shiru tana kallonsa. Ya tausasa murya, inason ki jira ni in cika wannan alqawarin, ko zamu rabu, ki bari in gama yi miki gatan dana tsara ma kaina, inji dake wani irin dadin da baki sanshi ba. In yasa nan, sai inyi miki abinda kk so. Tayi wani dan tunani. Sannan tace, zan yarda ne kawai in kaima ka yarda da abinda zan fada ynxun. Yace inajinki. tace zaka daura aure ne lokacin da ka warware nawa auren. Yace ban fahimta ba? Tace, ina nufin ba zaka ki aure ba, sai lokacin daka warware nawa auren. Yayi shiru don shi tun jiya ya gama tsarinsa. Ya tsara zai auri zainabu don ya gaji da zama haka, ita kuma lokacin data gama shirmenta sai su shirya don babu saki acikin zuciyarsa a ynxun. Daga nan sai ya kaita gaban iyayenta ta nemi gafararsu, duk da Hajiya tace zasu nemeshi in lokaci yayi. Amma dubi yadda ita kuma ta 6ullo masa da wata magana. 8⃣1⃣Ta katse masa tunani da cewa, kayi shiru? Yace, kina ganin zamana babu aure ba ragewar mutunci na bane a matsayina na mai fadakarwa? Ta miqe tsaye, tayi dan taku daya zuwa uku, sannan ta kalleshi, ni da kaine kawai muka san cewa ba kada mata, amma Duniya ta jima da sanin cewa kanada aure. Yace naji saidai karki manta ni fa mutum ne, kuma ba yaro ba, wanda yakai. Kinsan dole ina buqatar abokiyar halittata. Kinsan shekaruna nawa ynxun? Tace ban sani ba, qila zaka gota talatin. Yace yauwa, to in na rantse miki ba zanyi kaffara ba, a takure nake, sannan inason yara. Ynzun dubi mahmud, matarsa tanada ciki na biyu. Ya numfasa, khadija saka idonki cikin nawa, ta kalleshi. Yace ina buqatar abokiyar rayuwa. Ta sunkuyar da kai, wannan ai zancenka ne da kuma wadda zaka aura. Kukan Aishatu ta jiyo, ta miqe da sauri, har tana tuntu6e da qafarsa zata fadi. Ya sa hannuwansa ya tare ta. Sai tsintar kanta tayi a jikinsa.Duk zun jisu cikin wani yanayi. Shine yayi ta maza. Yace ina zakije haka? Kike sauri zaki fadi kije ki karye, dama gaki nan kamar 'yar tsinke. Ta tashi da sauri, bakaji kukan Aishatu ba? Da sauri ta nufi gurin Aishatu. Ta shigo riqe da hannunta, sai lallashinta takeyi. "Yarinya tana kuka kin firgice, ranar da kk haifi naki, sai yaya? Ta harareshi cikin wasa, me zai hadani da haihuwa? Yayi qasa da murya, "wai ba kyajin komai game dani? Tace Aishatu dai tana kallonka. Ya miqe, bari dai in gafi tunda kin fasa yajin. In yaya ta dawo ki fada mata cewa nazo, kuma batun tarewa ya kawoni. Ynxu zance in samu mahmud ne muje kasuwa mj sayi abinda ya sauwaqa, mu zuba a gidan, to shikenan. 8⃣2⃣A zaure zuka hadu da yaya. Nan suka gaisa yayi mata bayanin dalilin zuwansa har yadda sukayi da mimi. Dariya yaya tayi, domin ta gama gano mimi tsabar son mijinta takeyi, amma sai bata nuna ma Ismail din ba. Tace khadija kenan 'yar daru, 'yar shagwa6a. Zamuyi magana da ita. Amma ni shawarata karka tsaya bata wani za6in ko nan ko can. Kawai kace mata ku koma, ko don sbd kauda hankalin mazu zaton bakada aure. Yace nima haka nekeso, amma kinsan rigimarta. Gashi zai da'awar in saketa takeyi. Ni kuma gsky sai inga in nayi haka ban kyauta wa mahaifiyarta ba. Yaya tace wannan ma bata taso ba. Kudai koma din, qila ma ku sasanta. Ismail yace, Allah yayi mana jagora. Yaya tace Ameen. Sukayj sallama tayi ciki shi kuma yayi waje. Kafin sati daya, ismail ya sayi abinda ya sauwaqa, sun kai sjn shisshirya. Sannan sun shirya walima, inda su yaya da maqotanta sukayi musu girki, shinkafa ce da waina, sai kaji. Girkin yayi kyau sosai, ga kuma abin sha. Bayan sun tashi daga walimar ne, sannan sukazo suka kwashe kayan sawar mimi, shi da mahmud. Kayan Gado dai tabarma su Ummi. Duk da haka basu koma ba, sbd ismail zasuje kaduna da kuma Abuja, don gabatar da wasu muhadarori, da kuma lakcoci. Haka kuma suna durowa katsina, ya tarar da takardar gayyata daga gwamnatin jihar katsina. A hannun Malam Aminu ya samu saqon. Yace wannan taro ne na manyan malamai, to ni meya kaini gurin? Malam yace daukaka ce daga Allah, ismail. Shawarar da zan baka kayi taka tsan tsan, domin Malamai ma wasu basa tsoron Allab, musamman in sunga Allah ya baka nasibi. Sannan kar kayi sanyi gurin fadar gsky, komai dacinta. Ismail

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37