Chapter 7
Chapter 7
hanyar ldan linke gefen littafin sannan ya ajiye. Ya kalli Ummi, to tashi kije gida ko mamana. Tace, to kawu, sai Anjima. Ta tashi ta fita. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 1⃣9⃣Daga tsaye yake yana kallon Mimi. Duk runtsi saidai yace, bayason Mimi, amma ba dai yace, ba tada kyau ba, don ma fatarta ta rage haske sakamakon canjin rayuwar data samu. Ga ta da gashi, abinda yake matuqar so ga mace. Ya koma gefen teburin daya dora littafin akai ya zauna yana kallon Mimi sosai. Yaga abubuwa da yawa a tare da ita wadanda suke sawa mace ta amsa sunanta mace. Harma ya jishi cikin wani irin yanayi daya tilasta masa lumshe ido. Muryar Mimi yake tunowa irinta matan da suka amsa sunansu na mata. Domin duk macen data amsa sunanta mace, bata yin magana da qarfi. Mimi ko masifa takeyi ba zakaji muryarta a sama ba. Hakanan in tana waya, qarya ne don kana kusa da ita kaji me take fadi, in dai ba ka saurara sosai ba. Haka zalika in tana magana da kai tamkar bata so. Wadannan dabi'un da kuma shagwa6arta tana matuqar burge Ismail, kuma yana sonta ga matar da zai aura. Qarar wayarsa ya dawo dashi tunaninsa. Ya daga, Mahmud ne yace, ka fito ina waje. Ismail yace, ganinan. Yayi masa bayanin Yadda sukayi da yaya Amina. Mahmud yace, yayi hakan. Ismail ya ciro dubu biyar yaba Mahmud yace, kaima kadan qara. Mahmud yace, babu matsala ka barsu don Allah. Ismail yace, a'a ka amsa kudinfa sunada dan yawa, dukda ban qirga ba. Ni tunani ma in na cire abinda zanyi amfani dasu, sauran sai in buda account in zuba, ko don buqatar su khadija. Mahmud yace, wannan ma tunani ne mai kyau. Sun jima suna tattaunawa sannan sukayi sallama. Daren ranar, gurin misalin sha daya Mimi ta farka daga varci, sakamakon hasken wutar lantarki da aka kawo, dana rashin wankanta na kusan kwana hudu, ya sata sai juyi takeyi. Ta tashi zaune tana kallon Ismail, wanda babu riga, ta lura sam shi ba mutum bane Maison varci da tufafi. Amma yanason rufa sosai. Ynxun haka rabin jikinsa, ko ince daga qafa zuwa qirjinsa a rufe yake. Sannan fuskarsa tamkar yana murmushi. Ta dauke idanunta tare da lumshe su. Sannan ta sauke ajiyar zuciya. Wannan duk don idanunta sun kalli sumar dake kwance a tsakiyar qirjinsa ne. Hasken wuta ne yasa shi bude ido, yayi miqa tare da salati, yace NEPA sun kawo wuta kenan. Yana tashi zaune yaga Mimi a zaune. "kema hasken wutar ne ya farkar dake? Na manta ban kashe ba. 2⃣0⃣Ta 6ata fuska, cikin shagwa6a tace, jikina yana yimin qaiqayi. Yace khadija kinqi yin wanka dole kiji haka a jikinki. Tace yaya zanyi ynxun to? Yace, bari in kaiki ciki, ki daure kiyi mana. Tace amma zaka tsareni a waje? Yace eh. Riga ya saka, sannan ya nufi cikin Gidan. Saida ya wanke bayin, sannan ya kai mata ruwan wankan. Yace, babu dai na zafi, kuma kinga har ynxu da dan sauran sanyi. Tace, zanyi hakanan. Kujera yasa mata ta zauna sannan ya fita. Data gama saida tasa kayanta data dauko na varci masu dan kauri sannan tace, na gama. Yazo ya kamota suna tafe a hankali. Sunzo daidai qofar dakin fatu, sai ta turo qofa ta fito. Ta kallesu, "ikon Allah, don jaraba ba'a bari a warke ba? Su dai basu tanka ta ba. Sai da Mimi ta zauna akan katifa sannan tace, wai me matarnan take nufi da abinda ta fada? Ismail dukda ya fuskanci inda fatu ta dosa, sai yace, nima ban gane nufinta ba. Daya koma kwaso kayan wankanma, saida tace, ya dai kamata a bari a warke. Ismail yace, ai da ciwon ma ba haramun bane. Tace, eh lallai ka riqa. Shidai ya fice a zuciyarsa yana cewa, sa ido sana'ar banza! Cikin kwanaki uku zuwa hudu an kammala gyara tsaf. Lallai komai yanason gyara, inji abban su saddam, lokacin daya gama kallon Gidan. Sannan ya juya ya kalli Ismail, qanina muna godia fa. Ismail yace, Ameen. Ismail shida Mahmud sukaje kasuwa, inda suka siyowa Mimi Gado waya goma na kwanciyar mutum daya, saitinsa harda sif. Sai fanka, dan TV dinta madaidaici. Mahmud yace, ga wata shawara, me zai hana kudin da kace kaba yaya Amina, ka amshe su ka cika ka sai musu firji ko dan qarami ne. Kaga ko da ruwan sanyi suke saidawa zasu samu dan na rufin asiri. Ismail yace, haka ne, amma bari mubar musu wancan kudin tunda ga wasu nan, sai mu sai musu dashi. Dogon fridge suka siya, sannan suka nemi shatar a kori-kura suka loda kayan, suka nufi Gidan yaya Amina. Maqota sai leqe sukeyi. Wasu suce 'yan haya suka sa a gida, wasu kuma suce kodai aure abbansu saddam ya sake yi. Suka shiga da kaya suka shirya komai tsaf, firjin kuma suka sashi a dakin yaya Amina. Su Ummi kam murna babu dama. Tana fita wata maqociyarsu, Bakaraba tana ta leqe, dama tanason taga giccin wani dan gidan ta kirashi. Tana hango Ummi, ta kwada mata kira. Ummi tazo, tace kunyi baqi ne a gdn naku, ko ko abbanku ne yayi aure? Ummi tace a'a kawunmu ne zai tafi madina, shine matarsa ta dawo Gidanmu. Tace ohoo, wadda ke asibiti? Ummi tace eh. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 2⃣1⃣Daga nan fa duk wanda yazo jin meya faru, sai tace, qanin mamansu Ummi ne zaije karatu, ya dawo da matarsa Gida. Dama ita balaraba gun nan duniya ce. Ga duk maison jin wani tsegumi a Unguwar, gurinta yake zuwa don ta shahara. Tunda taga anayin fenti a gidan take shige da fice don jin dalili. Bata samu cikakken bayani ba, sai a bakin Ummi. Saida komai yayi tsaf, sannan suka tafi. Bayan sunyi sallama da Mahmud ya shiga gida, ya zauna. "khadija na barki ke daya ko? Don Allah kiyi haquri. Ta dube shi, sannan ta kwantar da kanta gefe, babu komai, karka damu dani na saba da zama ni kadai. Yace, an gama gyaran dakin naki, na gidan su yaya Amina, yaushe zaki koma? Cikin sauri ta tashi, "ynxun zan koma. Yayi murmushi, meyasa kk gaggawar rabuwa dani? Kin gaji da zama dani ko, bana kula dake yadda ya kamata. Cikin sauri tace, a'a Nayi kewar yaya Amina ne, kuma nan din ina takura maka sosai. Qasa fa kk kwana, amma kana kula dani sosai. Yace nikam inata kewar rabuwa dake, tsawon lokaci muna kwana daki daya, zamu rabu. Ta sunkuyar da kai, "ba zaka rinqa zuwa Gidan ba? Yace, zan dinga zuwa kullum kafin in tafi. Ya kamata in sai miki waya ko? Sai mu dinga gaisawa ko? Tace, ka barni kawai tunda banida wanda zan kira. Yace, ba gani ba? Tace, a'a ka saimin novels na dan dinga karatu. Yace, wadanne iri? Tace, na turanci. Yace zan hada miki dana addini, tarihin Annabawa, da kuma wadanda zasu koyar dake, kisan yadda zaki ibadarki. Suma akwai masu fassarar turanci, akwai na hausa. Tace, to ka saimin. Yace kuma sai gobe zako koma gidan yaya din, sbd yau da dare nida Mahmud mu kwashe kayankin nin, ya nuna akwatunanta da yatsansa. Tace, "to Allah ya kaimu. Ya shiga cikin Gida ya sanar dasu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37