Skip to content

Chapter 18

Chapter 18

Canjin Rayuwa Book Four Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

yake cewa, bayi zaton bake daya bace. Tadan ware idanu, da alamun Mamaki, "nida wa kk zaton samu? Yace, qawarki mana. Ta dafa hannunta da saman gadonta, tare da karkata kanta, ta dora kan kafadarta. "Nikam banida qawar data wuce Ummi, sai ko Aishatu. Yace, kardai kicemin har ynxun baki fita? Tace to ina zani kawun su Ummi? Wa na sani? Yayi dariya sbd sunan da ta kirashi dashi. Sunan nan da kk fadamin yana bani dariya khadija. Me zaisa ba zaki kirani da sunana ba Ismail? Tayi murmushi, "to ni bana iya fada ne. Na fa girmama ka ne. Ta fada da sigar shagwa6arta. Nidai gsky a daina fadamin wani kawun su Ummi, a kirani da wani abu kawai. Ta dubeshi, to Malam? Yace a'a ni dalibi ne, koyon karatu nakeyi. Kice min Ismail bin Abdurrahaman, ko kice, Abu Rumaisat. Tace ban gane Abu Rumaisat ba? Yace sunan yarinya ta kenan ta farko in Allah ya so. Rumaisat ko kice ummu suleim, duk sunanta ne. Ba kayi aure ba, amma kana fadin Yarinyar da zaka haifa? To in Maman taqi yarda fa? Maman babyn. Ya rasa dalili, sai yaji gabansa ya fadi, da take Cewa baiyi aure ba. Yace, nasan zata yarda, domin duk matar da zan aura, ba taqi yimin biyayya akan hakaba. Zataso abinda nakeso. Game da batun aure kuwa, zanyi shi da zarar na kammala karatuna. Kafin lokacin na samu mai sona. Mimi ta samu kanta da damuwa, sakamakon amsar daya bata. Tayi shiru. Ya katse ta, bayan ya Kalli agogon hannunsa. Lokaci yana tafiya. Nazo ne muje kiyi ma Rabi'a barka. Karki cemin a'a, duk abinki yaukam sai kinje. Mimi ta 6ata rai. Yace tashi tashi kawai. Ta miqe tana fadin nidai banason fita ne. Yace, kuma saikin fita ba, gashi da nisa kuma a qafa zamuje, dare ne bare kice kar wanda yasanki ya ganki. Tace kai baka gane nufina ba. Ni fa banason inyi hulda da kowa ne, ballantana in saba da kowa. Yaya Amina da kai da yaranta kun isheni. Yace, amma ai kinsan cewa mutum rahama ne ko? Shikenan muje, ba sai kunyi hira ba, bare ku saba. In kinyi mata varka, kiyi shiru. 5⃣5⃣Ta dauki qaramin mayafinta ta yafa. Ya kalleta, kisa hijabi mana khadija. Tace duk fa hijaban da ka kawomin qasa suke ja. Ni ban saba dasu ba, ina yin sallah dasu ne. Yace karki damu kome suke ja, in dai baki sani ba zakiyi sallah da abinki. Bata sake cewa komai ba, ta bude durowar ta ta ciro ta saka, suka leqa tayiwa yaya sai sun dawo, shi kuma tsaya suka gaisa, ya fada mata inda zasu je. A hankali suke tafe iskar damina tana kadasu, zukatansu sun cika da nishadi. Ismail yace, ki tunamin in zamu dawo akwai wani gurin saida kifi, sai mu biya in sai miki. Cikin doki tace, tam, dama nayi kwana biyu banci kifi ba. Nagode. Yayi 'yar dariya, "menene na godiya? Tace, gurinka na koya. Koni ka saima abu in na amsa, sai kace min wai ka gode. Ta dubeshi, kai baka damu da cin kifi ba ko? Yace, aikam bai dameni ba. Amma ynxun na koya a gurinki. Tasa dariya, shikenan mun koya ma juna abu kenan. Yace ai dole kiyi abinda nakeyi. Tace, sbd me? Cikin zolaya yace, kin manta da jinina dake yawo a jikinki, ya gauraye da naki? Tace, daman hakane? To kai ba'a sa maka jinina ba, amma ya ka fara cin kifi? Yayi dariya, sbd ganin yadda ta shiga, ta yarda da abinda ya fada mata. Yace ni ai kara nayi miki. Yadda naga kinata son kifi dinne, shine nima naji ina sonshi. Tayi dariya, "kuna siya a madina ko? Nasan sunada shi, lokacin da mukaje umra da daddy naci sosai, sai dai nasu ba maggi sosai, yace, inaci mana, musamman innaji kewarki, sai in sayi kifi inci. Wani dadi taji a Zuciyarta, Ashe yana tunata. Tace kasan me? Ya dubeta, "a'a. Ban zaci kana tunani ba. Yace, sbd ke ba kya tuna ni, shine kk zaton nima bana tunaki? Ya ce, hakane don yaji ta bakinta. Wa ya fada maka ba na tuna ka? Yace, To in kinyi kewa ta me kkyi? Ta dago ido ta Kalli sararin samaniya babu taurari, sai alamun hadarin dake gudu. Sannan ta dubeshi, "qila zaka manta da wani hankacif daka ta6a bani, in ka tuna, to shine nakan dauko in kalla, wani lokacin ma har in shaqi qamshin turarenka. Dadi yaji matuqa, sannan yace, ashe na kai har haka a gurinki? Kafin tayi magana, yace, gashi har mun iso gidan, sai naga babu nisa ko? Ya fada tare da kallonta. Tace, nima dake fadin nisa, sai naga munyi sauri. Yace, to shiga kimin iso, zan kira angon qarnin ynxun a waya. [22/09 9:54 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 5⃣6⃣Tana shiga Mahmud din yana fitowa, yace, ga dakinnan, ki shiga. Bari mu shigo, ynxun ya kirani. Ta shiga da sallama dakin mai jego. Tana zama suna shigowa. Suka gaisa, Ismail ya miqa ma mimi yaron, ta amsheshi tare da kallon Ismail, "banfa iya daukar jarirai ba, karka sakemin shi." Hannuwansu suka hadu, dukkansu sun samu kansu cikin wani yanayi sakamakon hakan. Ta kalleshi. "me me ake cewa? Yace, hausawa suna cewa, Allah ya raya ko Allah ya amfanashi da dai sauransu. Ta kalli mai jego, "to Allah ya raya shi, yayi masa albarka. Ta sake kallonshi, haka yayi? Suka sa mata dariya. Mahmud yace, yayi. Nan kuma sai su Ismail suka canza harshe zuwa larabci. Ismail ke tambayar Mahmud "da wa yaron ke kama?" Mahmud yace, da ni mana. Ismail yace, a'a yafi ka kyau. Ismail ya miqa ma Mahmud yaron, tare da qifta masa ido, alamun zai tsokani Mimi, "khadija to in kin haifi naki yaron wa zai daukar miki? Ta harari Ismail, "ni ba zan haifi ko wane yaro ba. Don ko Aishatu ban ta6a daukarta ba saida tayi girma. Rabi'a tace, ba zaki haifi yaro ba. Sai yarinya? Mimi ta zaro ido, ni dai ba ruwana. Suka sa mata dariya sbd yanayin yadda tayi maganar Ya tsugunna kusa da ita, "yaya kk ga yaron? Cikin harshen turanci tace, yanada kyau sosai. Domingo mimi tafi iya harshen turanci fiye da harshen uwa. Duk lokacin da zatayi magana mai kalma goma, to turanci zai zama guda bakwai. Don haka saddam da Ummi suke qaruwa da ita. Tana taimaka musu da homework. Sun jima a Gidan har goman dare ta gota, sune dai sukeyin Hirarsu, ita dai Mimi jinsu kawai takeyi. Hammar daya lura tanayi ne yasa shi miqewa, "to bari dai mu tafi, yau dai mun hana 'yan barka sakewa. To duk wadda tazo saidai mamansu Rabi'a ta leqo a miqo mata yaron." Mahmud ya miqe shima, "nima wucewa zanyi" sukayi musabaha tare dayin sallama. Mimi ma sukayi sallama da Rabi'a. 5⃣7⃣Suna fitowa shagwa6a66iya Mimi tace, Ni kam na gaji kawun su Ummi, bazan iya tafiya da qafa ba. Yace, ba don kince min kawun su Ummi ba, da na goya ki hai gida. Cikin hamma hade da shagwa6a, ta ce, don Allah kawun su Ummi, ka mu hau abi hawa. Kaga inajin varci kaji? Yace kin cika langa6ewa khadija. Tace ni ba kaga qoqarina ba, don Allah ban

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37