Chapter 23
Chapter 23
sauraro. Dariya tayi, sosai sannan ta tura masa cewa, roqo na da kai, shine in kaji wannan matsalar tawa ka taimakamin, kuma ko da kisan kai ne ya kasance hukunci na to zan dauka. Ta tura masa. Haka tayi ta tura masa wadannan saqonni na wasa da hankali, tun yana nuna mata yanason jin ko wace matsala ce, ta daina jin tsoronsa ta fada masa, har ya gaji yayi banza da ita. Tare da haka, in ya kira yaya Amina yakance, a bashi Mimi su gaisa. Cikin ja masa ajin data saba yi take amsa su gaisa. Inya tambayi matsala, sai tace babu. Kwancitashi su Ismail sun kammala karatu na digiri, tare da sakamako mai kyau. Hukumar qasar ta tuntu6i daliban da aka yaye a wannan shekarar, ko akwai wanda yakeson yin aiki tare da su bisa ga albashi mai tsoka? Su Ismail kam cewa sukayi sunfi son suzo su amfanar da ilimin da suka samo ga al'ummar qasarsu. Sannan Ismail yanason samun nasa iyalin, ya gaji haka. Mimi bata ta6a yin murnar dawowar Ismail ba kamar wannan karon. Domin gsky tayi kewarsa, tanason ganinsa, sosai matuqa. Wani abu da ya sake burge ta shine tasha gwada Ismail da sim kala-kala, don taga ko yana hulda da mata, amma sai ta sameshi a natsattse wanda bashi da lokacin shashanci. Sun iso gida cike da murna da doki. saidai Ismail ya baro madina cike da burin komawa don samun digirinsa na biyu, in komai ya tafi masa daidai. Dakinsa ya sauka, wannan karon zai kama masauki amma sai ya saita lamuransa.7⃣1⃣Shi mahmud bashi da wannan matsalar ta gurin zama, domin suna da mazauninsu, daya daga cikin gidajen mahaifinsa. Sunyi isowar dare ne wannan dawowar. Kusan qarfe biyun dare suka shigo katsina. Kai tsaye gidansu ya wuce, ya sauna da kayansa. Su kuma su Mahmud da Rabi'a da dansu mus'ab yayi wayo sosai, suka wuce nasu gidan. Ismail ya buga gidan. Yayyinsa maza guda biyu sukazo sun a tambayar ko wanene? Ismail yace nine Ismail. Da sukazo suka buds mass, suna yi masa sannu da zuwa. Sun yi sallama Sai da safe, suka nufi ciki. Shikam bai kwanta back Sai daya share dakin. Want Abu daya bawa Ismail mamaki, bayan yay sallar asubahi ya dawo, ya kwanta don ya huta, bai yi niyyar fita ba don yana tsammanin babu Wanda yasan ya dawo, gurin qarfe goma yaji sallama a qofarsa. Barcin nasa sama-sama ne. Don haka Sai ya tashi ya suka jallabiyarsa ya fito, ya baqon nasa, Sam bai sanshi ba, amma ya miqa masa hannu, suka gaisa. Mutumin ya Ciro wasu takardu ya miqa masa, game saqo daga wani bawan Allah, yace in Baka tun kusan wata uku da suka wuce. Ismail ya kalleshi cikin rashin fahimta, saqon menene? Yace mai gidana be, inayi masa aikin sama. Ni kafintan same ne. Duk wani aikin gidajensa ni keyi masa daya shafi Sana. To shine ya tambayeni ko ma sanka? Nace unguwarmu daya. Ta yiwu Baka sanni ba, ina can bayan mayo be, gidan malam kadi. Ismail ya kalleshi. Gidan su hashimu? Baqon yace, yauwa, to ni wansu hashimu be. Zakkar gida be, ko ince kyautar gida yace in Baka. Wadannan takardun gidan be. A can unguwar GRA be gidan take. in ka shirya Sai mine in Nina mama. [25/09 3:10 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 7⃣2⃣Cikin mamaki, Ismael yace a ina wannan mai gidan naka yake, kuma yaya sunansa? Baqo yace nidai sunana Nasiru amma shi mai gidana ya hana ni in fadi sunansa ko unguwarsa. Yace, shi yayi ne don Allah, kuma malam ya sakashi a cikin addu'ar Allah ya biya masa buqatunsa na alheri. Ismail yace jirani ina zuwa. Ya koma daki ya canza kaya, ya fito yace, zo muje gurin malam. Sun samu malam Aminu, inda dan aike yayi masa bayanin kimai. Bada 6ata lokaci ba, suka nufi gidan, harda mahmud, wanda ismail yayi masa waya, shima yazo ya samesu. Sun samu mai gadin gidan ya bude musu suka shiga. Mai gadi yazo ya gaishesu tare da tambayar su ko wanene mai gidan cikinsu? Mahmud yace, wa yasa ka gadin gidan? Yace 'yalla6ai ne. Yace min duk randa wanda yaba gidan yazo, shi aikinsa ya qare. Mahmud yace, to ya sunan shi 'yalla6ai din? Tsoho maigadi yace, ya hanani in fadi sunansa. Sun zaga gidan qato ne sosai. Ginin na gefe hawa daya. Mai gadin ne yabasu makullan ciki tare da nuna musu ko ina na gidan. Shikam ismail filin gidan ne yafi burgeshi, domin har ya hango yadda zaiyi makaranta a gurin, harda masallaci. Take ya sanar da su malam Aminu sha'awarsa da gurin, suka ce tabbas bakan yayi. Sun yi bankwana da maigadi bayan ismail ya bashi dan abinda ke hannunsa tare da bashi baquri kan cewa bai fito da kudi ba. Suka fito suka kulle gidan suka tafi da makulli. Babu abinda gidan ke buqata saidai kayan da za'a zuba na amfani. Sun koma gida, inda Ismail ya kawo dubu biyar tare da sabbin jallabiyu a cikin kayansa yaba dan aike tare da bashi haquri, kan cewa dawowarsa kenan daga karatu bashida kudi. shi kuwa dan aike godia yayi, tare da cewa, ni ai babu abinda yafi faranta mun rai kamar sada ka da saqonka da nayi. Domin tun shekaran jiya yake cemin cikin satinnan zaku dawo. Ismail yace, wato harma ya san lokacin da zan dawo. Dan aike yace gsky ya sanin kenan. Sukayi bankwana, ismail ya rakashi tare da yi masa godiya mai yawa. Ko daya dawo daki, yayi iyakacin qoqarinsa don ya gane ko wanene. Amma hakan yaci tura. Sai kurum yayi masa addu'ar Allah ya cika masa burinsa, duniya da lahira. 7⃣3⃣Mimi suna da labarin dawowar ismail amma basu ganshi ba. Mimi bataji dadin hakan ba, domin sai taga kamar bai damu da ita ba. Sai washe gari bayan la'asar, yinin ranar Mimi tayishi ne cikin qunci da rashin walwala. Har yaya ta nemi dalili, amma sai Mimi tace, kanta keyi mata ciwo. Tana zaune a tsakar dakinta tana yanke qumba, kanta babu dankwali ta kama gashinta a tsakiya, kamar yadda ta saba tun tana 'yar gayunta, muryarsa ta jiyo yayi sallama, sai sowar yara ta jiyo suna yi masa sannu da zuwa. kamar ta tashi ta fita sai kuma ta fasa, ta kalli jikinta, riga da wando ne wadanda shine ya sai mata su. Taje madubi ta kalli fuskarta. Sai ta samu kanta da zazzaga hoda a tafin hannunta ta hure, sannan ta shafa ta hau tsakiyar gadonta ta zauna, ta kunna TV. Catoon sukeyi. Kusan minti ashirin da tara, sannan ya kalli dakinta, ita wannan bata nan ne? Yaya tace, tananan. Dazun dai tayi fama da ciwon kai, amma yayi sauqi. Da sallama ya shigo. Ta dago tamkar lokacin taji shigowarsa. Qwarjinin dake kan fuskarsa ya doketa, tayi saurin sunkuyar da kai, sannu da zuwa. Yace, sannunki, in zauna bakin gado? Ta dago ta dubeshi, yaune zaka nemi izinina? Yayi murmushi, ai na qara wayau ne ynxun. Da kinsan yaro ne. Tayi dariya, to ka zauna. Ya tsura mata ido, "kinci naman hawainiya ne? Yayi tambayar cikin tsokana. Ta zaro ido, meka gani? Duk lokacin da na tafi na dawo, sai inga kin canza kala. Gabanta ga fadi, tsoronta kar ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37