Chapter 31
Chapter 31
ganin amsarta, sai ya zata ko batayi na'am ba, don haka, sai ya shareta. Ita kuwa tanajin fitarsa, amma kunya ta hanata fitowa. Har washegari ba suyi batun ba, duk da sunci abincin dare tare, daren ranar qananan kaya yasa, abinda bata ta6a ganinsa da su ba. Ta kasa daina kallonsa don burgeta da yayi. Sam baiyi niyyar fita ba, kuma dama ya siyo qananan kaya ne don ya burgeta. Amma sai yayi nufin gwada ta. Ya dauki makullin mota zai fita, da sauri tace, ina zaka? Yace, khadija ya kamata ki daina tambayata in zan fita kamar wannan lokacin tunda kinsan komai. Ya kusa kai bakin qofa ta rasa me zatayi, sai kawai ta riqe ciki, "wash Allah na cikin! Ya waiwayo da sauri, yasan cewa qarya tayi, amma sai ya biye mata. Ya riqeta, ya kwantar da ita a cinyarsa, yaja rigarta sama kadan, ya soma yi mata addu'a yana shafa mata a cikin. Lamo tayi cike da burin dama su kwana a haka. Can yace, kinji sauqi? Tace eh, amma kar ka fita. Yace shikenan na bari sai gobe. Tuni Hajiya taba Alhaji shawara akan su miqa ma minista jikansa, sbd dalilinta data fada masa cewa, mutuncinka zai zube a idon jama'a, in kayi la'akari da cewa Abbas shine ubansa. Gashi 'yan jarida sunata bin shari'ar, ana ta yada ku a media. Yace shikenan. Da kansa yaje Abuja, ya kira Abbas yace ya zo ya dauki dansa. Sai dai sati biyu da daukar yaron ya farka da ciwan kunne. Sun kaishi Asibiti sun dubashi, sun basu gado. Kafin yamma ashe ciwon ajali ne, sai kuwa yace ga garinku nan. Hankalin ko wane 6angare ya tasbi. Na'ima kuwa kamar zatayi hauka. Amma dole suka dangana. Allah ya raba musu gardama. Abbas ya tura ma Na'ima saqon sakinta. Bayan watanni kuma sai ta nemi jami'a anan Abuja ta samu ta shiga, amma duk ta rame. Yanxun burinta taga mimi ta nemi gafara. Momy Nafisa kuwa tafi Na'ima da na sani. Hasana da Husaina sun sama mazaje, suna shekararsu ta biyu a jami'ar 'yar adua. Usaina, Abokin yaya mukhtar, kaduna yake. Ita kuma Hasana, Lecturer ne na makarantarsu, amma dan Gusau ne. An basu, amma sai sun qare karatu sannan za'ayi bikin. Shi yasa suka matsawa Hajiya sauda kan don Allah suna son abarsu suje gurin Sis mimi tunda an fada musu unguwar da take. Sun san Gidan ma. Hajiya sauda tace, susa ransu a inuwa daddyn sh ma yace, in ya dawo daga ganin likita a England zamuje gidan gaba dayanmu. Suka dauki murna. Burinsu dai ynxun daddy ya dawo. 9⃣5⃣Mimi kuwa tunda malam ya fita da safe take tunanin wane irin lambon da zatayi in dare yayi don kar ismail ya fita zuwa gidansu Hanan. Wanka tayi, taci kwalliya sosai, da riga da wando masu dame jiki. Ya shigo bayan la'asar. Tana kallonsa yayi ta satar kallonta, lokacin da yakecin abinci. Bayan ya dawo sallar isha'i, yayi kwalliya da qananan kaya, jeans ne baqi sai farar T-shirt mai gajeran hannu. Gaban rigar an rubuta, da harshen turanci cewa ina Alfahari kasancewa ta musulmi. Lokacin itama ta canza kayanta zuwa doguwar riga irin mai rawa dinnan ta kama gashin kanta a tsakiya. Da makullinsa a hannu ya fito, ta dubeshi, "sai ina kuma yau? Jiya ban samu zuwa gurin hanan ba, kuma na fada mata, kinga ai ya dace yau inje ko? Tayi shiru tana kallonshi. Yace sai na dawo, har ya fita daga falon, sai ta bishi, "Malam! Ya tsaya. Sannan ya waiwayo, menene kuma? Tace kalli garinnan hadari ne, kasan kuma ana fara ruwa Nefa zasu dauke wu, kuma inajin tsoro. Ya kalli sararin samaniya, tabbas hadari ne. Yace, zan dawo kafin ruwa ya sakko, wadannan qananan kayan na siyosu ne don ita. Biyu ne kacal, jiya nasa daya, yau ma gashi nasa dayan. In na bari sai gobe me zan sa? Kuma in banje ba, na zama qaramin mutum. Jiya nace, ganinan banzo ba, yauma haka? Ko zamu tare? Shiru tayi masa. Har ya kai gurin motar, guguwar hadarin ta taso. Da sassarfa ta nufeshi, "kazo ka koyamin karatu mana, wai ba ka bani sharadi ba, kuma na Amince? Ya lumshe ido don dadi. Ya juyo, "amma baki fadamin ba, kuma baki turamin message ba. Tace, to ba kace min shiru alamun eh bane? Ya kai hannu ya kamo tafin hannunta, ni kuma sai nayi zaton baki harda bane. Ya fizgo ta da qarfi ta fado qirjinsa, a kunne ya rada mata, tunda kin amince, bari in fara ynxu. Dumin sautin muryarsa a kunnenta, yasa tsigar jikinta tashi. Tafin hannunsa guda biyu yasa, ya lalubo fuskarta. Ya sa bakinsa ya sumbaci le6unanta. Ta zata shi kenan, sai kawai taga ya saka harshensa ya bude mata le6e. Wata kalar sumba yake mata. Kafin minti biyu, ta rasa duk wani kuzarinta. Jin cewa zata zube ne, sai ya jingina ta jikin motar. Saukar ruwan saman bai sashi barinta ba, sai da tace, Ma..lam ru..wa! Cak ya dauketa zuwa cikin falonsu, duk sun jiqe. 9⃣6⃣Kan kujera ya shinfide ta. Sannan yaje ya rufe falon. Har lokacin tananan lamo babu kuzari. Ya dubeta, muryarsa a dushe, "tashi muje ki kwanta. Sai kuma na gobe ko? Ya lura ba zata iya hanzari ba. Don haka ya riqe mata hannu, har bakin qofa ya kaita yace, saida safe. "Lamo tayi akan gado tare da maqale filo, idanunta rufe tana tuna abinda ya faru. Ta kasa tashi ta cire rigarta data soma jiqewa. Shi kansa Malam din juyi kurum yakeyi akan gado. Qarshe dai ya gano mafitarsa daya ce, ya watsa ruwa. Yafi minti biyar ruwan sanyi yana sauka daga tsakiyar kansa zuwa tafin kafarsa. Tsigar jikinsa data tashi ce yasa yasan cewa da akwai matsala. Ya fito kafin yayi wani yunquri har zazza6i ya rufeshi. Singileti da gajeran wando ya saka, sannan ya qudundune da zanin gado. Haka ya kwana. Lura da Mimi tayi yau Malam bai buga mata qofa ba shine yasa data idar da sallah ta nufi dakinsa. Tana turawa ta sameshi yana kakkarwa. Cikin sauri tace, malam lfy? Ta zauna a bakin gadon. Tanason takai hannu ta ta6a wuyansa kuma ta kasa. "In kawo maka magani? Bai iya amsawa ba. Da sauri ta sauka ta dauko panadol da ruwa. Da qyar ya tashi zaune, ya amsa ya sha, sannan yace, "rufamin bargo." ta janyo bargo ta rufa masa, sannan ta zabga tagumi tana yi masa sannu. Kusan minti shabiyar sannan ya ture bargon, zufa ta soma zubo masa. Tace mura ce ko? In dafo maka ruwan zafi? Tea yace eh, bari inyi sallah. Ya shiga bandaki ita kuma ta sauka kicin. Kan sallaya ta sameshi, ta zauna itama ta aje tiren a gabansa, sannan ta tambayeshi, tun yaushe ne bashida lfy? Ya kalli cikin idonta, kece kika zama silar ciwo na. Ta zaro ido, cikin shagwa6a tace, da nayi me? Ya kusanto kunnenta sosai yayi mata rada. Ni dai banji me yace ba, naga dai ta sunne kai a cinya, tare da fadin "kai Malam!" shi kuma yasa dariya. Murmushi nayi don salon soyayyarsu yayi matuqar burgeni. Ranar haka ya yini bai fita ba, wai yana jinya. Ko sallah shine yayi ta musu jam'i. Yayin da mimi tayi ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37