Chapter 24
Chapter 24
kusheta, ta kalleshi, duk nayi muni ko? Yayi dan murmushi, nidai ban fada ba. Tace to fadamin me nayi? Da ya fahimci tanason jin ta bakinsa game da yabon da yayi niyyar yi mata, sai ya canza da cewa, wai don Allah meyasa in na dawo baki doki na? Tayi masa kallon gefen ido, injiwa? Yace injini mana. In ana dokin mutum ai anayi masa tarba ta musamman da girke-girke. Ta ta6a baki, ai muma bakayi dokin ganinmu ba. Sai fa da kayi kwanaki, mutane suka gama ganinka, sannan kake zuwa mana nan. Yayi murmushi, amma zuwana na farko nan na fara sauka. Mimi tace, wannan ne kawai. Ta sake maido da wancan zancen. Baka fa bani a msa ba. Tame? Ya fada tare da kanne mata idonsa daya. Canzawar daka ce inayi. Shine nace muni na qara ko? Yayi 'yar dariya nidai bance ba. Ki kawomin ruwa mai sanyi insha, ya sake kauda zancen. 7⃣4⃣Ta sauka sannan ta dauki qaramin hijabi tasa. Yasan sbd kayan jikinta ne don sun kama fa tsam, duk motsin da tayi jikinta yana rawa. A zuciyarsa yace, lallai! Yau Mimi ce da rufe tsiraici? A fili yace Albmdlh. Ta kawo masa ruwa da kofi, ya kalli goran ruwan, lallai 'yan gayu, swan kuke sha? Tayi masa hararar wasa, wa zai bamu ruwan swan? Na fanfo ne muke sawa yayi sanyi. Ya tsiyaya ya sha. Cikin son jin me yayi niyyar cewa yaqi fada, tace ai kaima ka canza. Ya dubeta don ya riga ya dago ta. Yace, eh nima nasan na canza, na qara kyau sosai haka? Ta harareshi, ka cika son kanka da yawa. Yace inba gaky na fada ba sanar dani kawai. Tayi shiru. Yace shiru yana nufin eh ne. Ni nasan inada kyau. Ta 6ata rai, kai kyau ya dama. Ni ynxu nafison kyan hali. da ne nake kallon kyau wata tsiya. Yayi dariya shima inada shi, don naji mutane suna fada. Ranta ya sake 6aci. Da gske batasan shi zolayarta yake ba tace, ka cika wasa kanka. Kuma ance duk wanda yace shine, to ba shi bane. Yace nidai nine ismail bin Abdurrahaman. A ranta tace, karma yaga cewa na wani damu dashi ne ma, bari in masa zancen rabuwarmu. Tace gashi dai karatu ya qare, yaushe zamu warware maganarmu? Gabansa ya fadi. Nasa zaton ta dangana da wannan maganar. Maimakon yabata amsa, sai yace, ni na manta ma munyi gida fa. Ya miqe bari in sanar da yaya Amina. Itama ta miqe ta biyoshi. Nan ya labarta musu komai. Suka yi murna sosai. Yaya tace, kuma takardun da sunanka da komai? Yace cikakken sunana kuwa. Tace ko wanene wannan, Allah ya saka masa da alheri. Yace Ameen, gurina da akwai wasu kudi, zan gani ko zasu sai mana kayan gado dana girki. Ba sune dai akafi buqata ba? Yaya tace sune mana. In ma na gado ko katifa ce zatayi muku. Kayan kicin shine yafi zama dole. Yace hakane mu shirya gobe zanzo in kaiku gidan. Haka kuwa washegari yazo ya kwashesu. Gidan ya burgesu sosai. Mimi ta shiga fargaba, tana tambayar kanta wa zaisa a gidan? Bata san lokacin da tace to kawunsu ummi yaushe zaka dawo nan gidan? Ya kalli cikin idonta, ya karanci wani abu. Don haka sai yace, bari mu koma gida, zaki bani shawara ko? Ta daga gira, alamun eh. Yayi murmushi. [26/09 8:41 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 7⃣5⃣Ismail tunda ya dawo bai zauna ba, abubuwa zunyi masa yawa. Sun raba takardun neman aiki a jami'o'i kamar su A.B.U da B.U.K, har Abuja. Sannan qungiyarsu ta da'awa, suna ta gudanar da aikace-aikace, musamman na gidan marayun da suke ginawa. Sannan ga gayyata da yake samu gidajen rediyo, da talabijin da gabatar da filaye na addini irinsu tambayoyin addinin musulunci, Filin fatawa, da dai sauransu. Haka sauran jihohi irinsu kaduna, kano, sakoto, suna gayyatarsa don yin majalisi dashi. Hakan yasa ismail ya zama kullum yi nan, yi can. Ga shi har ynxun bai daina zama gaban malamai ba don neman qarin ilimi. Daukaka ta Allah, lokaci qanqani sunansa ya karade jihohin Arewa. Wannan yasa mahmud ya matsa masa. Wai ya tare a gidansa. Yaso su tare da mahmud din tunda sama ne da qasa, amma sai mahmud yace, in har ya sake ya tare a gidan ismail din, ba zai maida hankali a nasa ginin ba, wanda yayi nisa da farawa. Ranar wata lahadi misalin qarfe takwas da wani abu na dare, ismail ya shigo gurin su mimi, lokacin babu wutar NEPA ta kwanta a tsakar daki akan tabarma, tana dannan wayarta. Sallamarsa ta jiyo yasa ta kashe tocilar wayar, sannan ta kashe ta gaba daya, ta tura a qasan gado. Lokacin daya iso dakin da sallama, ta amsa. Yace farko dana shigo, sai naga kamar dakinnan da haske. Tace, idonka ne yaga haka. Ya ciro qaramar wayarsa daga aljihu, ya haska dakin. Kafin ya zauna yace, me kuke dashi na ci? Tace shinkafa mukayi da wake, sai mai da yaji. Jiya ne yaya tace, muyi alala, qila kozo, tunda ka kwana biyu baka zo ba. Amma sai kaqi zuwa. Yace ba zaki gane bane khadija. In a lissafa maki lamurran dake gabana, zaki sha mamaki. Karku damu da yin abinci dani. In nazo kamar haka in na samu zanci. Ban cika son cin yaji ba, shirya ki rakani muci abinci. Ko kuma ke kici kifinki. Tace kana son jana yawo, ni kuma banason fita. Yace shikenan ba zan matsa miki ba. Tace to bari in shirya muje. Ya ciro wayoyinsa banda wadda ya haska. Kamar ana jira sai ga kira, tamkar kar ya daga, sai kuma ya daga don ya lura da lambar anata kiransa da ita bai ta6a dagawa ba. 7⃣6⃣Kamar yadda ya zata kuwa mace ce, ya amsa suka gaisa. Yanason tuna inda yasan mai muryar.Ta katse masa tunani da cewa, baka ganeni ba ko? Yace cikin qosawa eh. Tace zainabu ce. Sai kuwa Mimi taga ya miqe da sauri tare da fadin zainabu?! Tace eh nice, malam. Zuciyarsa ta shiga bugawa da sauri. Yayi ta maza , yaya gida da mai gida da kuma yara? Tayi 'yar dariya, gida dai lfy mai gida kuwa bama tare. Munfi shekara biyu da rabuwa. Da kuwa qwara daya ne, ya dauki kayansa. Yace, subhanallahi, to Allah yayi miki za6i na alheri. Tace Ameen nagode, na gaisheka. Wannan kuma number ta ce. In ba laifi adan ajeta, don nayi ga kira baka daga ba, qila don bakasan lambar bane. Ban sani ba ko zan kira neman fatawa. Cikin wani shirinka na samu number lokacin daka bada. Yayi 'yar dariya, karki damu zanyi saving dinta, nagode. Kasa kashe wayar yayi, sai itace, ta kashe. Ya zauna bakin gado tare da cewa, auren zainabu ya mutu tun shekara biyu? Kenan ma tun ganin da nayi mata. Yaya tace min tanada aurenta, ashe ba tada shi. Sam ya manta da wata Mimi tana dakin. Ita kam tana zaune hankalinta tashe. Tambayar kanta kawai takeyi wacece kuma Zainabu? Batasan tambayar ta fito fili ba, saida taga ya tsaya cak, daga rawar jikin saving din lambar Zainabu wanda yakeyi. Shi sam ya manta a ina yake ma. Yace, am.. Wata yarinya ce. Ya miqe, ba zaki santa ba. Ya kalleta,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37