Skip to content

Chapter 33

Chapter 33

Canjin Rayuwa Book Four Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
Download Book

ba. Cikin sauri yaje ya daga niqaabinta. Kamar yadda ya zata Miminsa ce. Yace, uwata. Idanunta suka kawo hawaye, na'am daddy. Sai ya rungume ta, idanunsa suna masu kawo hawayen farin ciki. Ya kalli Alhaji kabiru. "yanxun fa mukeyin maganarta. Ance min kunzo gari. Ina jira a gama hayaniyar biki, muje gidan. Tace daddy wa ke aure? Yace 'yan biyu, sai mukhtar. Tace nazo a sa'a. Ta kalli mijinta wanda ke kallonsu cikin tausayi, tace Malam baka gaida su daddy ba. Ya qaraso tare da cewa, na jira ne ku numfasa. Nan suka gaisa suka nufi ciki. Shi dai Alhaji nan ya juya shima yabar abokansa da qaninsa. Falonsa ya yace ismail ya shiga. Ita kuma ta rufe niqabinta. Alhajin ya tasa ta suka nufi ciki. Hajiya sauda tana gaisawa da wasu baqi da suka shigo, Alhajin ga shigo yana kwada mata kira, tace Alhajina ho! Yau dai gidanmu da jama'a... Ya katseta, baquwa kikayi. Ta kalli Mimi fuska rufe, tace to ta shigo daga ina? Mimi taje ta rungume mahaiyarta. Sannan ta daga niqabi. Da sauri tace, Mimi ce! Nan dai akayi ta murnar ganin Mimi. Amare suna gidan mai musu gyaran jiki. Da yake sai washegari Asabar ne za'a daura auren. Hajiya da kanta ta kirasu ta fada musu, sai gasu. Murna tamkar zu cinye ta. An kawo mata wannan da wancan duk an jibge mata, sai dai hankalinta yana can gurin mijinta. Hajiya sauda tasa ta gaba, tana cewa, in bakison wannan me zakici? Saboda kowa yaga tsohon cikinta. Ta kalli Hasana, "wai ina Malam ne, ko suna gare da daddy? Hajiya sauda tayi murmushi, yana tare dasu daddynku, harda sy yayanku. Sannan Mimi ta soma tsakurar abincin don batajin yunwa, kuma ta saba ci da Mijinta. 1⃣0⃣1⃣Su Hajiya Binta suka iso da yaranta. Ita ma rungume Mimi tayi don murna. Kowa sai mamakin ganinta yakeyi. 'yan uwan hajiya sauda da dama basu san Mimi ba , sunanta sukeji, yau sai gata gasu. Hatta kakarta saida aka nuna mata. Yau dai ta gane 'yan uwa dadi garesu. Ashe ita 'yar dangi ce, gaba da baya haka? Daddy ma sai kiranta yakeyi yana tambayarta ana bata duk abinda takeso ko? Dariya takeyi, sannan tace, ana bani daddy. Suna dakin daddy ita da Amaren, sbd ko ina mutane sun cika. Ta ce ku tashi muje gurin gyaran jikin, nima za ayi min. Ta ciro waya, "bari in fadama Malam zamu fita.Ta kira wayarsa, dai dai lokacin da ya daga Hajiya sauda ta shigo, tace, musu su koma gurin gyaran jikin. Sai taji mimi tace, Malamina, na zata zanga Miss call dinka? Ka shareni ko? Cikin sigar shagwa6a ta fada. Yace kinsan dai ko a mafarki My Dija ba zan shareki ba. Na barki ne ku walwala da 'gan uwanki. Tace kana inane ynxun? Yace inason zan tafi masallaci, amma sai na koma gida na dauki takardar budubar dana rubuta. In zan dawo zan biya in dauko yaya Amina. Tace da ka kyauta min. Ta zo dasu Ummi, kaji My Malam? Yace zan fada mata. Kina son wani abu ne daga gida? Tace, illa mai da hoda na, sai turare. Yace shikenan. Tace zamu fita da Amare. Yace zuwa ina? Tace inda za'a yi musu kwalliya. Take yaji bari ya gwada ta. Sai yace, a'a ki zauna ki huta abinki. Bata zata ba. Don haka ta danyi dim, sannan tace, shikenan Malam, sai kunzo din. Sosai ta burgeshi, ya san ko ina zatayi masa biyayya. Sai yace, Dijana kuje kawai, sai kun dawo. Tace Allah Malam in baka so, ba zanje ba. Yace, na tsokane ki ne kawai. Basu Hasana ba, hatta mahaifiyarta saida Mimi ta burgeta. Lallai Malam ismail ya ciri tuta. Hajiya sauda ta dauko zanin anko, da wasu sufofi guda uku, da lesuka masu tsada, ta kira telan su, ta bashi tare da cewa gobe takeson su, amma anko yau za'a dinka. Tela yace, an gama! Don yasan Hajiya akwai sauke kudin dinki. Haka bayan sun dawo gyaran jikin ne Hajiya sauda ta zube Hijabai kan gado sabbi sun kai kala goma, tace, Mimi ta za6a in ma tana sonsu duka ta kwashe, ga takalma da jakarsu. Mimi tace, Hajiya kin siyane dama kin ajiye? Tace a'a saida sj mukeyi. Su Hasana suke kaiwa makaranta. Daga baya kuma sai muka kama shago. Odarsu ma mukeyi yanxun daga dubai da china. Mimi ta za6a, ta kuma za6arma yaya Amina, itama harda jaka da takalmi. 1⃣0⃣2⃣Qarfe uku akayi kamun Amare, lokacin ne kuma za'a saka anko. Mimi tayi kyau matuqa, duk da cikinta yasa tayi qiba. Kwalliyarta tasa ta saje da amare, duk da itama har ynxun da 6ur6ushin amarci, tunda bata dade da fara amarcin ba. Jeren kumbo ne akayi. Wannan karon ne na farko da Mimi taga irin bikin nan, kuma yayi matuqar burgeta. Yaya Amina sun iso da yaranta sunga tarba gurin Hajiya da ita kanta Hajiyar. Sunci, sunsha, sannan aka kwashe su a mota zuwa gidansu yaya Abba inda acan ake kamu din. Sai dare sannan Ismail ya kira Mimi yace, su yaya Amina su fito ya maida su gida. Tace abar Ummi, tunda zasu dawo gobe, sbd gobe ne daurin aure. Hajiya ta had musu kayan biki. Mimi ce ta raka su har gurin mijinta. Sun shiga mota, shi kuma ya fito, suka ke6e da Mimi. Yace, ke kam nasan sai an gama biki ko? Tace, sai yadda kace. In kuma kafison na koma, sai mu tafi, ka kawoni da safe. Ya kai hannu ya kama nata, ki zauna kuyi bikinku. Daddy ma dazu yace min, wai inyi haquri sai an gama biki, in barki. Tace ai yadda kasan yana tsoron kar in gudu, ba ayin awa daga bai kira layina ba. Ismail yayi dariya, gurina ya amshi lambar. Ya murza hannunta, yau zanyi kewarku, da dana. Tace mu ma haka. Har ya kai mota zai shiga, ta ce Malam! Ya dawo, tayi qasa da murya saitin kunnensa, "don Allah kar kayi tunanin kowa sai nawa. Ya shafi kumatunta. Yace ai kinyi kane-kane a zuciyar nan. Baki bar gurin da zata tuna wata ba. Zan kiraki an jima, in bakiyi barci ba. Ta shafi kumatunsa, zan jira ka. Saida motarsa ta fice, sannan Mimi ta juya zata koma cikin gida. Ashe duk daddy yana kallonsu daga inda yake zaune. Sai ya fito ya kira Mimi, Uwata! Da sauri ta nufeshi tace, ina ka 6oye daddynh, tun dazu banganka ba, sai dai waya. Yace muna ta fama da jama'a Uwata. Naga mijinki ya tafi. Tace yayarsa ce da yaranta. Yace naji dadin ganin yadda kuke da mijinki, kina sonshi, kuma naji dadin ganin yadda kk samu canjin rayuwa. Tace daddy kullum ina saka cikin addu'a Allahvya saka maka da Aljannarsa, sbd kalar mijin daka za6amin. Yana sona sosai daddy. Kuma shine ya nuna min hanyar wuta data aljanna. Daddy ka yafemin laifukan dan yi mak. [29/09 2:42 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 1⃣0⃣3⃣Yace, Mimi ba kiyi laifi ba, daidai kk yi da kk gudu. Kinga momynki a bikin nan? Mimi tace, Inason in tambaya, amma sai abin ya shigemin. Ya bata labarin komai. Yace, ynxun haka Na'ima tananan gida. Momyn ku suna bikin qaninta shiyasa bata zo ba, amma Na'ima kunyar fita takeyi. Ko makaranta sai

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37