Chapter 1
Chapter 1
Chanjin rayuwa book 4 1⃣Saboda ta samu canjin rayuwa, daga jahilci zuwa ilimi, daga rashin tarbiyya zuwa tarbiyya, daga mara mutunci zuwa mai mutunci. Sauda, da farko nayi wa Mimi wannan auren ne don in quntata mata, in qona mata rai, kamar yadda ta qona min. Amma daga baya tunani ya shige ni, nayi nazarin dalilin wannan auren zata iya samun canjin rayuwa. Ismail zai iya bata ilimi na addini wanda ta rasa daga gareni. Sannan, ilimi zaisa ta zama mai tarbiyya ko dan yaya, tunda anbar shiri tun rani. Dalilin da yasa nace kar kuje gurinta, nima nace kar su sake nemana, sbd idn bata tare damu, zata fi samun tarbiyya. Shi ba zaiji shakkar mu ba, ko tsoron mu in tayi abin hukunci. Kuma yanda na lura dashi, bashi da shakka, kinga kenan ba zaiji tsoron duk wata barazanar ta ba. Haka kuma ba zamu taimaka musu da kudi ba, sbd shi kansa banason mu kashe masa zuciya, ya kasa neman na kansa, ko yaushe yana jiranmu. Haka kuma ita kanta rashin taimaka musun zaisa ta saba da Rayuwar babu, wadda bata sani ba ada. Yanke alaqa dasu shine zaisa ita da shi suyi abinda ya kamata. Hajiya sauda ta sauke ajiyar zuciya, "Na fahimceka sosai Alhaji, saidai nayi wani kuskure daya. "ya kalleta, na tura musu dubu dari. "karki damu, saidai karki sake tura musu kudi. Da zaki iya ma ko wayarsu karki sake kira. Ta danyi shiru tana nazari. Ya katseta, kar kisa ma kanki damuwa, nayi miki alqawarin bibiyar miki labarin duk halin da suke ciki. Ta tsura masa ido, a cikin qwayar idanunsa ta tabbatar da abin da yake fada. Tace, shikenan Alhaji. Allah yasa mu dace. Yace, "Ameen matar qwarai". Ya kama hannunta, "nasan ranki ya nutsu da yaron, kuma nima na fahimci cewa, yaron mai hankali ne. "Sukayi dariya. Yace, kinsan menene sauda? Tace a'a. yace, "Ni kaina ina cikin matsanancin kewar Mimi. Na sani sarai tunaninta ne ya hana ciwwonnan sauka. Tace, nasan za'ayi haka, amma tunda kanada wannan qudurin, wajibinka ne ka daure, ka jure, ka kuma kauda kai, sannan mu hada da Addu'a, Allah ya taya mu. Yace, Ameen ya rabbi. Ynxun kuma na samu natsuwa tunda Allah yasa kin fahimceni. Ranar nan suka yini suna qoqarin kyautata ma juna. 2⃣Haka itama Mimi tayi ta jinya, yaya Amina da Ismail suna matuqar kula da ita. 'yan uwan mamansu na Daura sunzo, sun duna jikin Mimi, sannan sun kawo musu kudin gonarsu da aka saida. Don haka shirye-shiryen tafiyar Ismail ya kankama. Haka nan 6angaren Mimi, zuwa ynxun Ismail yayi nasarar saka Mimi ta fara sallah dole, ba don ta so ba. Yawan nasiha da nacinsa ya sata sauraronsa. Ya nuna mata yadda zatayi sallah, kuma ya dauki nauyin yi mata akwalla. Ranar daya fara tsananta mata tayi sallah da kuka tayi sallar. Da farko ma bata yi ba, sai da yace shikam ba za yayi jinyarta ba, matsawar ba zata yi sallah ba. Ya nuna mata shifa tafiyarsa zaiyi. Yaya Amina ita ma cikin son ta tsorata ta tace, in ko ka tafi, nima zaman me zanyi? Kinga kenan saiki zauna babu mai jinya, ba mai kula dake. Tana kukan nata tace, yayi mata alwalla. Tun daga ranar, duk lokacin sallah in yayi, sai ta yita. Wani abin da yaba Mimi al'ajabi shine tunda ta soma sallah, sai ta samu kanta cikin wata natsuwa, ta kuma qara imanin cewa sallah tana kusanta bawa ga ubangijinsa. Haka kuma lokacin da yace zai dinga koya mata gajerun surori, bata qi ba sbd sallah. Kwanci tashi har taci wata daya da sati daya a asibiti. Lokacin ne kuma da Doctor din dabyayi mata dori ya dibar mata zaizo ya duba in dori yayi kyau, sai ya kwance. Ranar litinin da misalin qarfe goma na safe, likitan suka shigo shida doctor salis. Kallon qafafun nata kawai yayi, yace inasa ran cewa dorin yayi kyau. Zan kwance shi ynxun sai ku kaita ayi mata hoto, sai ku kawo mu gani. Ismail cikin murna yace, Alhamdulillahi, dama na gaji da zaman asisibitin nan, har ita ma khadijan ta gaji ko?. Ya fada tare da kallonta. Mimi ta kalli likitan, kenan in hoton ya nuna cewa, dorin yayi za'a sallameni ne? Likita yace, eh, to ku daiyi hoton mu gani. Bayan an kwance tana ta shagwa6a, ta qanqame yaya Amina. Likitan yace, a kaita hoto ynxu. Ismail ke tura ta a kujerar tura marasa lfy suka nufi gefen hoto. Yaya tana jere da shi suna magana. Yace, "Yaya Allah yasa hoton babu tsada sbd Kinsan fa babu sauran kudi, gashi kudin dakinmu dana sake biya ya qare. "Wai saura nawa ne ma kudinnan da aka ajiye sbd tafiya? Yace "ta6" ai baifi saura dubu goma ba acikin dubu hamsin din dana ba Mahmud don kar in kashe, amma duk sun qare. Tace, ai dama zara bata barin dami. Barkanmu da sallah sis 🙌 [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 5⃣A qofar gidansu yakeyin wankin, amma yanajin nauyin shanya kayan Mimi a igiyar waje, sbd duk qananan kaya ne matsattsu. Sannan har pant din ta yake wankewa, don haka sai ya daura igiya acikin zauren kusa da qofar dakinsa yana shanya kayanta a gurin. Wani lokacin ma sai ya jira sun dan sha kadan ya kwashe, sbd yaran Gidan marasa ji, wani sa'in suna zubo da kayan qasa. Yau ma daya gama wanka, yayi shirinsa zai fita, sai ya kwashe panties din da vests yaje ya shanya su kan akwatunanta, ya kunna musu fanka, sannan ya kulle qofar ya nufi gidansu Mahmud. Hirarsu kullum bata wuce ta tafiya. Mahmud yace, Ismail kasan Rabi'a ta daga hankalinta akan batun tafiyarnan? "saboda me to?" Inji Ismail. Mahmud yayi 'yar dariya, wai tana tsoron kar in hadu da wata acan in manta da ita. Nace ta daina wannan tunani, tana damun kanta bayan anyi mana baiko. Sai tace, to yaushe zan dawo? Nace mata ban san lokacin ba. Shine take fushi dani. Ismail yace, mata kenan 'yan rigima. Ni baga wannan shagwa6a66iyar Yarinyar ba. Lokacin da zan fito fa kuka takeyi, wai bazan fito ba. Mahmud yasa dariya, to ba yaya Amina tananan ba? Yace bata nan, tana gidansu. Tazo dai da safe, amma ta koma sbd batajin dadin jikinta. Kasan Allah, Mahmud na gaji da zaman asibitin nan, ita kuma gata da shegen son jikin tsiya. An ce, ta dan dinga dan takawa, amma taqi. Shiyasa na barta ita kadai don tayi zuciya ta motsa. Mahmud yace, Ismail saidai fa kayi ta haquri, domin yarinyarnan cikin shagwa6a ta taso, hakan ya zama jinin jikinta. Ai ma kaci nasara tunda tana cin duk abin da aka dafa aka bata, sannan ta amince zata zauna daku. Ismail yace, ni damuwa ta ynxun, inda zan barta in zamu tafi. Mahmud yace, inda lafiyar ta lau ne, da sai mu tafi tare da ita. Ismail yace, kasan Allah, ko lafiyarta lau bazan iya tafiya da ita ba, haka kawai taje ta dameni. Tunanina in barta gurin yaya Amina da mijinta, tunda suna da dakin yara, da kuma dakin da mahaifiyarsa da take ciki kafin ta rasu. 6⃣Mahmud yace, hakane, kai ai yaya Amina tanada zumunci. Nasan ma ba zata qi ba. Ismail
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37