Chapter 10
Chapter 10
tana varci don ta farka cikin dare har Maman bushira ke bata labarin yadda sukayi da Nurse. Zainabu tayi ta roqon ta akan cewa, ta taimaka mata don Allah don Allah ta fadawa mai asibitin. Ya kalli Maman bushira yace, ya jikin nata? Tace, da sauqi. Yace, ta farka? Cikin son qara tsorata shi, tace eh ta farka, amma bata cikin hayyacinta. Domin bata ganeni ba ma. Alhajin ya sake rudewa. To likitan bai sake dubata bane? Ance asibitin kudi, kuma na bada duk abinda akace, amma ba zasu duba ta yadda ya kamata ba? Zai fara sababinsa tace, Alhaji gara fa kabi ahankali sbd likitan ya fara tambayoyi akan shedar dukan dake jikinta. Sannan zuwan su biyu nemanka. Yace, to ni dai bari ma inzo in tafi kawai. Ya ciro kudi ya qirga dubu goma ya bata, "ga wannan ki riqe a gurinki. In sun tambaye ni kice nayi tafiya. Sannan karki sake aji daga bakinki cewa, ni na duketa." Tace, to shedar dukan fa data fito a jikinta? Yace, kice musu bulala ce ta fito mata. Ba awai ciwon bulala ba? Tamkar Maman bushira ta saki dariya, sbd ganin yadda Alhajin ya birkice. Bayan tafiyarsa tace, ai zaka gane kuranka. Nurse dai tazo kamar yadda tace, kuma ta raka ta har gurin mai Asibitin a cikin ofishinta. Da ma takan zo qarfe goma ta tashi sha biyu. Bayan Maman bushira ta gaisheta ne, sai Nurse din tace, gata nan momy. Doctor din ta kalleta, malama kiyimin bayanin dana samu daga wannan Nurse din. Maman bushira tayi mata bayanin yadda abin ya faru har ya kaiga dukanta. Sannan tace, tashi muje in ganta. Sun samu Zainabu ta farka. Tana ganin likitar ta soma kuka tana cewa, don Allah ta taimake ta. Likitar tace, karki damu, hadin kanki nake buqata. Tayi ma Zainabu tambayoyi, ta amsa. Sannan tace, to babu damuwa qarfe nawa zaizo? Maman bushira tace, ai yazo har ya tafi. Kuma zaiyi wuya ya qara zuwa don a tsorace yake. Likitar tace, qarfe nawa za'a saleshi a Gida? Tace takwas na safe ko tara na dare. Likitar tace, babu komai. 2⃣8⃣Doctor Asma'u Adamu mace ce mai kamar maza. Tana da taimako sosai, musamman akan abinda ya Shafi mata. Duk lokacin data samu matsala makamanciyar wannan, ko ba'a Asibitinta ba ne, takan nemar wa mai haqqi haqqinta. Har ta kai ga kafa qungiya mai qwato wa mata 'yanci. Suna da lauyoyi da mai qwato wa mata 'yanci. Suna da lauyoyi da 'yan sanda da malamai da kuma alqalai a cikin qungiyarsu. Bada 6ata lokaci ba suka rubuta takarda suka aikawa 'yan sanda, inda suka gayyaci Alhaji lawal zuwa ofishinsu. Da yaso yayi gardama, sai suka tura masa 'yan sanda. Dole ya zo suka tasa shi har asibiti. Lokacin Zainabu tana zaune tana shan tea. A cikin kudin daya ba Maman bushira ta fita ta siyo kayan tea din. Sun duba jikinta kuma sunyi mata tambayoyi ta basu bayanin duk avinda kenan tun daga tun daga tursasa mata auren sa da akayi har zuwa yau dinnan. Sun tasashi har Gidansu Zainabu inda aka taso qeyar innar Zainabu. Likita Asma'u ta rufe innarsu Zainabu da fada. Tace, aje a rufesu, sai gobe za'a shiga dasu kotu. Nan fa hankalin Alhaji yayi matuqar tashi. Ya shiga bada baki, tare da roqon don Allah ayi masa afuwa tunda bata sonshi, yaji kuma ya haqura, zai sake ta. Likita tace, ai dama wannan dole ne, sannan kai zaka kula da ita har ta warke, sannan ka dauki nauyin cikinta, har ta haihu ta yaye. Yace, duk na yarda. Ita kuwa inna, saida aka rubuta takarda dasa hannu kan cewa ba zata sake tursasa ta ba. Cikin su duk wanda ya sake, sai yayi zaman jarum. Bayan gargadi mai tsanani aka sallamesu, bayan Alhaji ya rubuta takardar sakin Zainabu, yayin da maman bushira ta shirya yanata-yanata, ta dauki kudin da Alhajin ya bata, taba Zainabu. Zainabu taba ta dubu uku daga ciki. Har taqi kar6a, Zainabu tace, lallai saita kar6a. Ta qara da cewa, taimakon da kk yi min, Allah ne kawai zai biyaki. Murna gurin Zainabu tamkar sallah, wannan sakin da akayi mata, matsalarta daya, wannan cikin dake jikinta. Kwana uku ta qara aka sallameta. Suka je ta kwashe nata-yanata suka nufi Gida. Kafin su wuce, dama likita ta tabbatar ma da Zainabu duk wata, gurinsu zata dinga zuwa ta amshi duk abinda aka yanke dashi. Shi kuma sun tabbatar masa cewa, sun saka ido akansa, in ya sake yiwa 'yar wasu haka, to ba shakka zai qare rayuwarsa a Gidan kaso. [18/09 3:31 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 2⃣9⃣Rayuwar Na'ima a Gidan minister dai sai a hankali, don in yana gari ne zaka ga suna kula ta, amma da yayi tafiya ko ya fita, banza ma ta fita. Abbas kuwa ko yazo gidan bata isheshi kallo ba. Haka qannensa batajin dadinsu, har gara Aisha ma data dawo hutu, takan dan kulata. Saima ta gwammace zaman gidan Abbas dana iyayensa. Don haka wata safiyar talata ta samu Hajiya Bilkisu, bayan ta gaisheta, ta amsa cikin jin kai. Na'ima tace mata, momy na samu sauqi inaso in koma gidana. Hajiya Bilkisu tace, ai gara kam ki koma don nima kin takuramin. Ta kira Abbas tace masa, "ka kira daddynku ka fada masa cewa, zaku koma gida. Ko da Abbas ya kira shi, saida ya kira Na'ima ya tambayeta cewa, ko itace ta buqaci komawa gidanta? Tace, eh itace. Ya tambayeta ko akwai wani abu da take buqata? Tace, a'a babu komai. Yace to likitan dake dubata yayi mata? Tace eh yayi yace, to zaici gaba da zuwa duba ta a gidanta. Haka ta tattara ta koma Gidanta wanda bata iya bambantashi da gidan yari, ko da dai bata san gidan yarin ba. Shi kam Abbas dalilin cikinnan ya samu abubuwa da dama a gurin mahaifinsa. Sannan, yasha gargadi cewa, ya lura da jikansa, tare da ba uwar duk abinda take so, don jikansa ya fito duniya da girma.kusan duk sati biyu, sai anyi hoton cikin don tabbatar da lafiyar sa. Namiji ne kamar yadda sukeso. Sai dai fa, har ynxun Abbas bai daina kawo mata gidanba, mata kala-kala wataran a ita yake sawa tayi musu girki, kuma dolenta tayishi tana kuka, tana komai ga ciki. Hakanan kuma duk randa yaji cewa, yana ra'ayinta dolenta ta miqa kanta, sannan kuma ya gargadeta cewa, har dai in ta bari dadynsa yaji wata magana daga gareta, to kuwa nata daddyn sai abinda yafi haka. Babu ranar banza da Na'ima ba zatayi kuka ba, gami da dana sani, ga dinbin nadama data cika zuciya da ga6o6inta. Gani take ko mimi ynxun ta fita kwanciyar hankali. Abin takaicin gashi babu dama ta koma gida sbd in daddy yaji allura ce zata tono garma. Ita kanta Momy Nafisa komai ya kwance mata. A ynxun bata qi ace auren Na'ima ya mutu ba, cikin ma ya 6are. Rayuwa kenan mai canji. 3⃣0⃣Kwancitashi har an cinye wata daya da tafiyar su Ismail. A farkon tafiyarsu, Mimi bata da wata matsala domin yaya Amina tana yi mata komai, sannan ko girki zatayi, saita tambayi Mimi me zata ci, a dafa. Mimi bata komai, sai kwanciya sai sallah, sannan takan dan taka da sandarta a tsakar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37