Skip to content

Chapter 11

Chapter 11

Canjin Rayuwa Book Four Complete Hausa Novel 1,213 words 0 views Progress saved
Download Book

Gida da cikin daki. Zuwa ynxun ma takan dan taka ba sanda, amma ba sosai ba, din Mimi tana da tsoro. Haka nan Ismail kan kira su a waya yana jin lafiyar su a duk lokacin daya samu sukuni. Sai dai kamar yadda hausawa suke cewa, zara bata barin dami haka yake. Domin kudinda Ismail yabar ma yaya Amina sun qare, sannan abincin ma ya qare, sai dai awo sukeyi in abban saddam ya dan samo. Haka ruwan sanyi in sun saka na saidawa a fridge, sai a yini bai fisu yi Naira hamsin ba, ko kuma maqota su amsa bashi. In kuma da kudi zasu saya su tafi shago. Hakan yasa suka shiga halin matsi, musamman ga Mimi wadda bata saba da irin wannan rayuwar ba. Kafin akai wanu lokaci, Mimi ta qara lalacewa, tayi baqi, ta kode. Ga wasu qurarraji da suka fito mata a fuska. Wata safiya Mimi tana zaune akan tabarma a tsakar dakinta, ruwan Lipton ne a gabanta da yankan biredi. Hawaye suka zubo mata da ta tuna abinda takeyin kari dashi a gidansu. Ta kalli fatar jikinta, a fili tace, dubi yadda fata na mai daukar hankali ta dawo. Ta shafa sassan wuyanta, ga rama wadda ta sani yin muni. Ta kalli dakinta, dole jikina ya zama haka, babu cima mai kyau, ba AC, ba makwanci mai kyau, ga hayaniya. Sai dai duk da haka babu abinda zance ma wadannan mutanen. Saboda sunyi matuqar qoqari daidai qarfinsu kenan. Duk abinda takeci a gurinsu bata saba da cinsu ba koma tace, bata ta6a ci ba. Amman batada za6i, dole taci, domin yunwa ba tada hankali, kamar yadda taji wani almajiri yana fadi in yazo bara. Haka nan ta tsantsoma taci ta tashi. Su kuwa mutan madina suna can karatu yana tafiya yadda ya kamata, musamman dayake sun samu wadansu 'yan Nigeria acan suna gabansu a karatu. Don haka basu sama wata matsala ba, domin har abinci sukan samu gurin 'yan uwa mazauna can wadanda suka je da matansu. Hazaqa da nacin karatu, da nacin halattar majalisin da malaman sukeyi sune suka sa Ismail kar6uwaba gurin malamansu da dama. [18/09 10:20 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 3⃣1⃣Wata rana suna zaune da Ismail da Mahmud, sai Ismail yace, ko yaushe tunanina in mun gama karatunnan mun koma Gida, wace sana'a mutum zai kama don ya kare mutuncin kansa. Mahmud yace kamar yaya? Ismail yace, banaso in zama daya daga cikin malaman da gwamnati take juyawa ko 'yan siyasa. Inaso in riqe kaina ta hanyar sana'a ta, yadda zanji dadin fadawa mutane gsky. In kirasu zuwa ga addinin Allah, ba tare da na canza maganar Allah da manzonsa zuwa son zuciyata ba. Kwadayin abin hannun mutane shike sa wasu malaman kasa fada masu gsky. Ya dafa Mahmud, ka san Allah, sai ynxun ne ma na dana zo nan na qara sanin darajar ilimi. Na fahimci cewa, babu wani mai kudin daya kamata abi shi Gidansa don koyama 'y'ayansa karatu. Ilimin addinin musulunci ya girmi haka. Kamata yayi duk mai buqata yabishi zuwa makaranta. Mahmud yace, hakane batunka Ismail. Amma in mun yi digiri dinmu, ba koyarwa zamu nema a jami'a ba? Ismail yace, zamu nema, ba don dokar makarantarnan ta hana dalibi yin sana'a ko aiki ba, da munyi aiki ko sana'a. Mahmud yace, da ko littattafai muke siya da irin su jallabiyu muna turasu can Gida. Ismail yace, ko ta gurin Malam ne, da an samu alheri. Amma tunda qa'idarsu ce, sai mu haqura mu bisu yadda sukeso. Mahmud yace, karka damu, zamu yi wannan tunanin in mun kusa hada karatunmu. Ismail yace, inason in gina makaranta, babbar makaranta, amma lamarin babu sauqi. Mahmud yace, inda anan qasar ne, zaka samu masu taimakawa, amma mu masu kudin qasarmu, gsky taimakonsu da sauqi. Masu taimakon basuda yawa, wasu ma in zasu taimaka sai sun debi 'yan jarida. Sukayi dariya, sannan suka tafa. 3⃣2⃣A batun kyau, Ismail yayi kyau. Sun yi kyau na ban mamaki, musamman Ismail, wanda ya kasance fari. Jajir yayi sbd AC, ga cima mai kyau. Yayi 'yar qiba, farinsa yayi tas-tas, gashin kansa da sajen sa zuwa gashin bakinsa, sunyi shar tamkar an shuka su. Idanunsa sunyi tas-tas le6unansa sunyi jajir. Kallo daya daka masa, zaka san ya canza. Kai ko shi da kansa ya kalli kansa yana gode ma Allah daya halitta shi. Ko Mahmud dayake baqi yayi kyau, yayi sumul. Kwanci tashi rayuwa tana tafiya, har azumi ya kawo kai. Su Ismail sukan dan yo aike daga dan abinda sukayi ta ragewa daga dan abinda suke samu na tallafi daga makaranta. Wani dan uwansu dalibi shine ya hadasu da wanda zasu dinga turawa saqon, sai Malam ya amsa sannan ya kira abbansu saddam yaje ya amsa. Farkon azumi sai yaya Amina ta samu ciki, ta kama laulayi, sai aikin gidan ya koma hannun Ummi da saddam. Rashin lafiya yaya Amina takeyi sosai. Hakan shi ya tilasta Mimi fitowa don kamawa su Ummi aiki. Tana taimaka mata da girki, shara da wanke-wanke. Sbd lokacin ta warke sarai, sai dan dingishin da takeyi wanda ba dolene a gane in ba kayi mata kyakkyawan sani ba. Shima dingishin da takeyi saida sukaje asibiti, Doctor salis ya fada musu lokacin da likitan da yai mata aikin zaizo. Ko da lokacin yayi sunje kuma sunyi masa bayani, yace karta damu zata koma rass dinta. Tsoro taji lokacin da zata soma tafiya. Amma tunda batajin ciwo agurin, babu wata matsala. Haka kuwa kafin sallah, tayi sumul a fannin lfy. Saidai fa ga wanda yasan Mimi zaiyi wahala in ya ganta ya ganeta. Hakanan tunda tazo gidan bata ta6a fita ba, ko kanta saidai a wanke a gida. In ya isheta, tasa yaya ta kama mata kalba, domin ko a da bata damu dayin kitso ba. Amma lokacin sallah a ranar idi ta saka Ummi ta rakata saloon ta wanko kanta. CANJI DAI NA RAYUWA gashi nan qarara a gurin Mimi. [19/09 9:35 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 3⃣3⃣Alhaji bashir ya kalli Hajiya sauda, sannan ya 6alli karas din data wanke masa yakeci, sbd likitansa yace, lallai yana da kyau ya dinga cin karas sbd yana qarawa masu ciwon suga qarfin ido. Yace, "kina dai korata ko?" ba haka bane, ta yaya zan gaji dakai? Yace to kince in tafi Abuja. Tace kawai naga ka dade bakaje bane, kusan tunda ka sallamawa yaran nan kasuwancinka, sau daya kaje. Gashi har anyi azumi, an gama, yau kuma sallah. Yace, shikenan zance Nafisa ta tattaro yarannan gaba dayansu, suzo katsina suyi sallah anan katsina. Sam bana jin dadin yin sallah ko ina inba gida ba. Kinsan wannan. Tace, shikenan suzo nan din. Yace, banda Na'ima tanada tsohon ciki, da sun zo da ita nan itama cikin danginta. Sauda tace, zaiyi wuya minister yabarta, yadda naji kana fadin yanaji da jikansa. Yace, hakane kam. Sai kuma Mimi ta fado mata a rai. Ko ynxun ina Mimi take? Ko tana cikin wane hali? Anya kuwa ba zata bi shawarar Hajiya mardiyya bane? A wani zuwa da tayi ne, suna zancen Mimi, tace ynxun ke Hajiya sauda kin biyema zancen mazannan, kinbar 'yarki ba tare da kinsan halin da take ciki ba? Kiyi tunani fa, su maza ba kamar mu bane, zai iya jure rashin ta, kuma

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37