Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Canjin Rayuwa Book Four Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
Download Book

ko a sallamemu, amma kinqi. Ya dauketa cak ya dora ta akan Gado. Sai na dawo. Bata dai ce komai ba, shi kuma yayi tafiyarsa. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 7⃣Ta aje cake din hannunta akan gado, "Nidai ka tafi dani mana." yace kwantar da hankalinki, wannan ba abin damuwa bane, ga yaya Amina, sai ku tare, inkin sauqi sosai, in nazo sai mu tafi. Tace, to ka fadawa yaya Amina dinne? Yace, ban fada mata ba, amma nasan cewa ita babu matsala. Tace, shikenan yaya jikinta fa? Yace, da sauqi, dukda banbi ta gidanta ba. "Ya ciro wayarsa, bari in kira Abban su saddam ya bata mu gaida ta. "sun gaisa da abban su saddam, sai ya tambayi mai jiki. Abbansu saddam yace, gatanan tanata rawar sanyi, ta qudundune, ta dai sha magani. Ismail yace, to ka gaisheta. Khadija ma tanayi mata sannu. Abbansu saddam yace, zataji. Ya kalli Mimi, kinji har ynxun jikin ko? Tace, Allah warki yaya! Allah ya bata lfy. Washe gari yaya bata samu zuwa ba, sbd jikin nata. Ismail yace, to yau yaya zamuyi da wanka? Ko in miki? Ta zaro idanu, tana kallonsa, a ranta tace, shi wannan nufinsa dole sai yaga tsiraici na ne? A fili tace, na haqura sai taji sauqi. In tazo zatamin, harda gashina zata wankemin, yayi datti, duk ya dameni. Yace, wai meyasa baki yarda dani ba, sai kace zanyi miki wani abu. Ki tsaya ko gashin ba sai in wanke miki ba? Naga yadda tayi miki ranar nan mana. Tace a'a karka samin ruwa a kunne. Ni saloon nakeson zuwa. Yace to yau kidan taka ne mana khadija. Kinga basu so mu tafi da wata matsala ne. Da sunga kindan taka zasu sallamemu, sai in kaiki duk inda kk so. Ranar dai da qyar ya samu ta dan taka, daya biyu yana sagale da ita, sai ko ta fada jikinsa. Wani iri yaji, tsigar jikinsa ta motsa. Yayi mamaki, bai ta6a jin haka ba aduk irin daukanta da yakeyi mata a cikin wannan jinyar. Cikin sauri ya dagota daga jikinsa, muryarsa a sarqe ya dago ta, "kin cika ragwanta, to zauna kidan huta. 8⃣Cikin sati daya, mimi tana dan fita tare da taimakon yaya Amina don taji dan sauqi ta dawo, da kuma taimakon uban gayya, Ismail. Burinsu lokacin a sallamesu, domin basuda kudi a hannunsu. Ranar litinin kuwa Doctor salis da lukman, likitan da yayi mata dori suka tabbatar ma da mimi sallama. Ismail yayi murna tamkar dan kurkuku a ranar daya fito. Duk sunyi murna sosai. Yace, ma yaya Amina ta shirya kayansu, shi kuma zaije ya dan karkade dakinsa. Yaya tace, ina zata? Gidanmu zamu wuce tunda mun riga mun sanar da Abbansu saddam. Yace da inason indan gyara mata dakin na Gidanku, tare da dan sa mata abin kwanciya kafin dai mu wuce. Tace, hakane. Tare da Mahmud suka share ko ina na dakin sannan suka dauki shatar tasi zuwa asibiti. Likitoci da Nurses sunyi masu murna da barin asibitin, nan ne ma Doctor salis ya basu tabbacin cewa, duk lokacin da wata bukatar taimako ta taso, to qofa a bude take su tunkareshi. Yaba Ismail katinsa mai dauke da lambobinsa a jiki. Ismail ma bai qwauron baki ba ya fada masa cewa, shi zai tafi karatu ne a madina, amma duk abinda ya taso ga yaya Amina nan. Doctor salis yayi masa fatan alheri, tare da samun nasara. Zainabu tana zaune a bakin gadonta da 'yar rediyo a hannunta, tana sauraro. Ta babansu ce ta dauko lokacin da zata dawo gdn Alhajin bayan barowarta daga asibiti, sosai rediyon ke debe mata kewa, da shirye-shiryensu, musamman wanda suke karanta littafin hausa. Da ta qagara taji wani littafi da ake karantawa, sai ta samu bushira tana ce mata ina zata samu littafai? Bushira tace mata, sai dai na haya. Wannan ne mafarin karance-karancen ta. Kuma suna debe mata kewa don tana cin karo da matsalolin da suka zarta nata. Kuma tana qaruwa sosai. Don haka sai tayi haquri ta dangana, ta kuma ci gaba da kai ma Allah kukanta. Shi kuma Alhaji lawal bai canza ba, saima abinda yayi gaba. Hakanan wani abin dake damunta shine tunda ta dawo gidan batayi al'ada ba. Saidai bataji wani canji a jikinta ba. Tsoronta daya, kar dai wani cikin ne ta sake samu, domin gsky ba tada burin hada zuri'a da Alhaji lawal, sai dai masoyinta Ismail. Kullum cikin sa take, duk da wata zuciyar tana fada mata cewa, Ismail yayi mata nisa. Amma bata debe tsammani ba tunda tana Addu'a. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 9⃣Haka rayuwa take, dama idn kace tukunyar wani bazata tafasa ba, taka ko dumi ta bar yi. Na fadi haka ne sakamakon gani halin da Na'ima take ciki, Ga ta kwance cikin halin laulayin ciki, amma shi ko a jikinsa. Gashi irin crikinnan ne mai aman tsiya. A qarshe ma da yaga ba zata yi masa wani amfani ba, sai ya yaye zaman gdn. In ya fita tun safe sai dare. Bata sanin shigowarsa, sannu bata hada su. Ganin abin yana qara gaba, ta daga waya ta kira momy tace mata, "ki fada masa zanzo in maido ki nan gida gurina, tunda daddyn ku yana katsina ba zaisan kina gidan ba. Washe gari da sassafe kafin ya fita, Na'ima da bin bango takai saman Abbas, ya fito cikin shirin fita ya ganta sharkaf a kwance a falo, cikin tsawa yace, ke! Ki fita a falona banason qazanta, karki sake kiyimin amai anan. Cikin numfarfashi tace, don Allah ka kaini Gida, su kaini asibiti. Yace, ba zaki haumin mota ba, saidai in ki kira su, suzo da tasu, su daukeki, su 'yan gidan naku. "yace ke sauka muje zan rufe gefena. Tace, to don Allah ka kiramin su. Yace, banida lambar kowa a Gidanku. Qiri-qiri yaqi kiran su sam, sannan ya tasa qeyarta har dakinta ya fice abinsa. Ita ce ta sake kiran momy ta fada mata komai. Momy tace, gatanan zuwa. Gidan aminiyarta Nana ta soma zuwa, ta karanto mata komai. Nana ta sa6i mayafinta tace, muje Gidan uwarsa domin lallai sai tasan halin da ake ciki, in yaso ta jawa danta kunne. Momy Nafisa tace, shiyasa na biyo ta gurinki, don nasan dole zaki kawo shawara mai amfani. Cikin motar Momy Nafisa suka dunguma zuwa gdn minister. Saida masu Gadi sukayi waya cikin gdn bayan sun fadi ko su suwaye, sannan aka basu izinin shiga ciki. A falo aka dauke su. Sunfi qarfin minti sha biyar sannan masu aiki suka kawo musu abinsha. Cikin isa da cin magani, Hajiya Bilkisu ta sauko gurinsu, dai-dai take kallonsu. Hakan yasa su momy Nafisa yin dari-dari. 1⃣0⃣Hajiya Nana ce tayi qarfin halin cewa, Hajiya dama abinda ya kawomu, qara muka kawo miki, qaran Abbas. Sai sukaga tayi wani murmushi, wanda ba zasu iya fassara shi ba. Hajiya Nana taci gaba da cewa, tunda muka kai yarinyarnan banda wulaqanci da cin mutunci babu abinda take fuskanta daga gareshi. Gashi ynxun tana fama da laulayin ciki amma yaqi ya kaita ko asibiti. Momy Nafisa tace, kuma banda diban matan banza babu abinda ya... "Hannuwan da Hajiya Bilkisu ta daga shine ya dakatar da Momy Nafisa. Cikin matsanancin 6acin rai, Hajiya Bilkisu tace, ina

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37