Chapter 36
Chapter 36
kinji ma bashida amfani, don haushi zakiji. Ta nace, shi kuma ya fada mata komai. Ranar ce ta farko da suka raba daki tunda suka hada, saidai in daya baya gidan. Cijewa Ismail yayi baije lallashi ba don yasan ba zata saurareshi ba. Ita kam hakan ya sata zaton ko ismail ya daina yayinta. Kwana tayi kuka, sannan tunda duku-duku taja motarta ta nufi gidan Ubanta. Yaji fitarta daya duba sai yaga tabar Al'amin. Shine yayi masa shirin makaranta, ya kaishi. Daga can ya samu malam Aminu suka zanta akan batun zainabu, shima Malam ya amince da Ismail ya auri zainabu, sbd ubanta yazo gurinsa kusan sau biyar. Yace, suje aji sadaki, ya bada, a daura kawai ta tare. Daganan sai ya wuce gidansu gimbiyar sa. 1⃣1⃣0⃣Sun gaisa da Alhaji bayn sun shiga falon baqi. Alhaji yace, saiga mutuniyar fuska kumbure kuma har ynxun sai kuka taqi cewa komai. Ismail ya koro ma Alhaji komai. Alhaji yayi murmushi, "Ni dama nasan tatsuniyar gizo bata wuce ta qoqi. Mata sun tsani kishiya, kuma bayan da biyu ma akace mu fara, sannan uku ko hudu. Ita dama tana auren Malami zata ce ita daya zata zauna? Ismail yace nida banida ra'ayin sake aurema daddy, amma in yana cikin qaddara ta dole nayi. Yace karka damu, kaidai kayi qoqarin adalci, Mahaifiyarta tanada abin ce mata, kuma zata dawo anjima. Ko da Alhaji ya fadama Hajiya sauda maqasudin zuwan Mimi gida, a gaban Mimin Hajiya sauda tace haka ne? Mimi tace hakane. Ran Hajiya sauda ya 6aci, tace dama kina zaton mijinki ya zauna dake daya ne har abada? Ta dago ido ta kalli Hajiyar, "ya fa yi alqawarin ba zaimin kishiya ba, Hajiya sauda tace ga mahaifinki nan zaune, ni ma yayi min alqawarin ba zai min kishiya ba, amma yau kishiyoyi nawa gareni? Mimi tayi shiru. Hajiya ta sake cewa, inace harda ke kun hada baki aka auro miki Momynki Nafisa? Kin manta duk da wannan? To inaso ki sani, mata da yawa suna hana mazajensu aure, a qarshe sai mazajen suje suna bin matan banza. Sannan wasu suna hana mazan su aure a qarshe sai kuma su mutu ayi auren. Banda ma wannan qannai nawa gareki mata? Ce miki akayi ko wacce an bugo mata mijinta ne? In kin hana a auri qanwar wasu waccan ta hana a auri qanwarki, shikenan sai su tabbata babu aure? Inaso ki koma gidanki, ki nutsu ki ba mijinki qwarin gwiwa yayi muku adalci. Karki canza daga son da kk masa. Ki qara gurin kyautata masa. Ki riqe amanarsa, ki zama mai haquri da kuma ki hada da addu'a. In dai ni na haifeki, to karki kuma zuwa gidannan da sunan yaji. Ku kashe, ku rufe keda mijinki. Alhaji ya dubeta, "Mahaifiyarki ta gama fada miki komai. Ni dai zan qara miki da cewa kiyi haquri. Haka mimi ta koma gidanta cikin damuwa, sai dai zantukan mahaifiyarta sun isheta tunani. Ko da ya dawo lallashin ta yayi, tare da nuna mata cewa ba don bai sonta bane. Har zuwa ranar asabar din da aka daura auren, sama-sama suke, sai dai Mimi tace ya nemi gurin da zai saka matarsa, ba zata zauna tare da ita ba. Baiji komai ba, dama ya kama gida, unguwarsu Mahmud, can ya sata. Ranar farkonsu ya tausaya ma Zainabu sbd irin son da take masa. Ita kuwa Mimi kwana tayi kuka, ta san cewa ynxu sun zama su biyu masu shi. Daga masallanci, gidan ya wuto. Tana varci shima ya kwanta kusa da ita. Data farka ta ganshi, sai kawai ta fita ta koma kicin tana hada abin kari. Sai da ta gama soya dankali, da qwai da sauransu, sai taga ya dauki kwando ya jera, yace kiyi wani, wannan zan tafi dashi. Ta daga murya sbd me? Yace sbd Allah da kuma cewa kin isa. Ya debo dankali, muyi in tayaki. Banason ki zubar da kanki gurin zainabu, don a komai bata kaiki ba. Inason kiyi zama da ita na adalci, ki nuna mata girma. Kar kiyi wasa da muqaminki na Uwar gida. [01/10 8:09 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 1⃣1⃣1⃣Zantukansa ta hada dana Mahaifiyarta data sake kiranta a waya ta nana ta mata. Dole ta haqura, kuma ta yarda cewa, mijinta fa ba laifi yayi ba don ya qara aure. Sunna ya raya. Ba taji haushin kanta ba, sai ranar daya kawo mata zainabu, gaba daya sai taji ba taga abin kishi ba. Ita kuwa Zainabu sai taji tana shakkar Mimi. Ga wani qwarjini da Mimin tayi mata, har ita kanta Mimin ta lurabda haka. Don haka sai ita Mimin tace, kar fa kiji komai, nan gidan mijinki ne. Zainabu ta yarda Allah ne kawai ya bata Malam, domin mai kamar Mimi ba zai kalleta ba. Mimi ta sauka, wannan ma Namiji ne, sai yaci sunan Alhaji. An sha suna, sannan itama zainabu ta kama nata laulayin. Lokacin Ismail baya qasa. Sun tafi Africa ta kudu. Shine ya kira Mimi ya fada mata cewa Zainabu babu lafiya, don Allah ta dubata. Mimi ta tausaya mata halin da ta sameta. Ita ce takai ta Asibiti. Bayan gwaje-gwaje an gano ciki wata biyu. Mimi ta wuce da ita Gidanta kafin mijin ya dawo. Dakin su Al'amin ta sauketa. Da yake ynxu tanada masu aiki, yarinya da tsohuwa, sannan sunada Mai gadi. Mimi tsakani da Allah take kula da Zainabu, kwana biyar ya dawo, samun Zainabu danyayi gurin Mimi tana samun kula, sai ya sake daga darajar Mimi. Harma ya fada mata cewa, My Dija, na jima da yarda cewa ko dabba na daure zaki kula da ita, bare Mutum. Hakan ya qara mata qaimi gurin zama zama da kishiyarta lfy. Zainabu ta haihu ta samu 'ya mace. Ga mamakin Mimi sai Zainabu tace ya sama 'yar sunan Mimi wato Khadija. 'ya kuwa taga kaya gurin Mimi. 1⃣1⃣2⃣Mimi cikin motarta tare da yaranta, a Abuja sunje bikin Na'ima ne ta auri wani maqwafcinsu da matarsa ta rasu gurin haihuwar danta na biyu. Bayan biki ya watse da ranar da zata tafi tace, bata barin Abuja, saita nemo mina qawarta. Gidan iyayen mina taje neman labarin. Har gidanta qanin mina ya raka Mimi anan cikin Abuja. Sun rungume juna sunata murna, kafin suka 6arke da labari. Mina tasha mamakin jin cewa, sheikh Ismail Abdurrahman shine Malaminta da mahaifinta ya bata. Tace, ta san shi domin yana daya daga cikin malaman da take nutsuwa da wa'azin su. Sai mallon mimi takeyi tana Mamakin ta. Tace dubeki kamar matar shugaban qasa, wai matar Malami. Mimi tayi dariya, tace kinsan Allah duk wadda mijinta ba Malami bane, ina mai jajanta mata, domin ta rasa abubuwa da dama. Me zanyi da wani shugaban qasa da ba zai samu lokacina ba sai na mutan qasa? Barni da mijina mai kasheni da kalolin soyayyarsa. Mina tace, qwarai na yarda dake, domin wata lakcarsa da naji yana yiwa mata da maza, saida nace, Allah yasa haka yakewa iyalinsa. Mimi tana dariya, tace yana min. Suna cikin haka saiga wayarsa. Mina kallon mimi takeyi tanata zuba shagwa6a a waya. Wai gobe zata dawo, shi kuma yace idanunsa aun qosa su ganta. Ta bashi mina sun gaisa, suka yi bankwana tare da amsar lambar juna. Rayuwar su mimi abin koyi ce ga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37