Skip to content

Chapter 2

Chapter 2

Canjin Rayuwa Book Four Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

yace, ba zata qi ba insha Allah. Yaya Amina, aita zamar min uwa saidai ince Allah ya bani ikon yi mata biyayya. Mahmud yace, Ameen, ai tafiyar tamu ma tazo. Naji yana cewa nan da qarshen wata, sati uku dai a taqaice. Ismail yace, tabbas tafiya tazo, Allah dai yasa a sallamemu kafin ranar. Kai ni gobe ma zan samu likitan ince masa sallama kurum nakeso. Mahmud yace, kafin su sallameku, ya kamata itama ta dan taka su gani. Matsa mata ai zakayi. Sai daf da magriba sannan suka rabu. Gida ya koma ya kwashe kayan shanyarsa, sannan ya daukar mata wasu kayan ya nufi asibitin. Yana sauka ana tada sallah. Don haka sai ya bada ajiyar ledarsa cikin wani shago, ya shiga sallah. Har zai bari sai yayi isha'i, sai kuma ya tuna itama tana buqatar yin sallar. Zaune ya same ta akan gadonta, taci kuka ta gode ma Allah. Tausayinta ya kamashi, amma sai ya dake tamkar baiga fuskarta ba. "Muje kiyi alwalla! " Tayi banza dashi. Yazo zai dauke ta zuwa bandaki, tace, ka barni, ka tafi abinka. Dama nasan dole ka gaji dani, iyayen da suka haifeni ma sun gaji dani, sun gujeni bare kai da suka jona maka ni? Banga laifin ka ba. Amma meyasa kasa nayi maka alqawarin zama tare da ku bisa sharadin cewa zaka kula dani, sai gashi tun kafin mubar asibitin ka gaji? Nasan kaida 'yar uwarka kuna dawainiya dani, amma yadda ka nuna nima 'yar uwarka ce, na zata za'a dan jima kafin in gundureku. Ismail yadan tausasa murya, cikin sigar lallashi yace, wai waya fada miki cewa, mun gundira dake ne? Ni kin bani haushi ne yadda kk qi kidan taka ko sau daya ne. Kuma khadija wanki naje nayi miki, ya sake matsowa kusa da ita daf, yasa hannu ya dago fuskarta, cikin wani salo ya kira sunanta, khadija! Ta dago jajayen idanunta ta kalleshi. Yace, "Wlh baki gundiremu ba, kuma bamu gaji dake ba, kuma ke 'yar uwarmu ce. Tace, nidai nafiso ka bani saki na, ka tafi abinka. "Ya dora yatsansa akan la66anta, "shhhh, ki daina cewa haka mana qanwatah. Kiyi haquri! In kaiki kiyi alwalla ko? Taqi magana. Da qyar ya lallasheta, sannan ya kaita alwalla. Bayan isha'i ne tana cin cake da fanta, yace, kinji tafiyarmu zuwa qarshen wata ko? Tayi takwa-takwa da fuska "to ni kuma ina zaka barni? Ya kwaikwayi muryarta, shine nakeson muyi shawara dake. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwan 3⃣Mimi, wadda ake turawa tana jinsu, duk qarma-qarmar da yakeyi tana jinsu, kuma ta sani. A zaton ta ma da kudinta akeyi mata komai, har suka qare ya shiiga nasa. Tace, to yaya Amina su sallamemu mana tunda dai babu kudi. Yaya ta kalli Ismail, "Nima nawa tunanin kenan, ko ya ka gani? Ismail yace, bari dai ayi hoton mu gani. Allah yasa dai kudin babu yawa. Ynxun ma tunanina ko zan barku anan inje in amso ragowar na hannun Mahmud. Yaya tace, muje dai, in kaji kudin, sai ka tafi. Dubu shida da dari shida ne kudin hoton, don haka dole ne ya tafi ya amso ragowar kudin, kafin ya isa, saida ya kira layin Mahmud din, don haka mai acha6ar da ya kaishi, shine ya dawo dashi. Don haka suka biya akayi musu, sannan suka amshi sakamako suka koma. Sai sha biyu sannan likitan ya dawo ya duba, yace Alhmdlh, kuma tana da jiki mai kyau. Don haka zata iya soma koyon tafiya. Ismail ya kalli doctor. Ismail ya kalli Doctor salis yace, za'a iya Sallamar mu? Sbd gsky duk abinda muke dashi ya qare. Doctor salis yace, karka damu malam Ismail, kayi qoqari sosai. Ba duka namiji za'a samu ya tsaya kan matarsa haka ba. Mimi ta dago, ta kalli Ismail, idanun ta da alamun tambaya. Sai yayi murmushi, ya kalli likitan, ai yaya baya kasa dawainiya da qanwarsa. "Take likitan ya kalli Mimi, sai ya tuna 6aran6aramar da yayi, don haka yace, "oh na manta hakane, yaya ne ashe. " Yammacin ranar, Ismail babu yadda baiyi ba da Mimi ta dan soma takawa, amma taqi, sai kuka takeyi wai ba zata iya ba. A qarshe haushi ne ya cika Ismail ya fita waje ya zauna akan benci. Tunanunnuka ne kashi-kashi suka addabeshi, yana mamakin yadda yaketa neman layin Hajiya sauda, amma baya samu itama kuma ta daina kiranshi. Sannan yau sati uku kenan da ita hajiyar ta sallami Mahmud daga koyar dasu hasana. Ko yaushe in Ismael yayi ma Mahmud wannan qorafin, sai yace, karka damu ni dama ko basu sallameni ba, dole in barsu tunda kaga karatu zamu tafi. Game da rashin waiwayar 'yarsu kuwa ka qara haquri. 4⃣Gashi yana tunanin ina zai samu kudi, ko ba don ciwonta ba, ko don sbd tafiyarsa. Sannan in an sallamesu, ina zai ajeta? Domin gsky bai kyautu ba yasa ta dakin zaure.Duk bama wannan ba, gurin wa zai barta? Yana jiyo ta daga ciki tana magana cikin shagwa6a, "to kazo mana, ka kamani zan kwanta ne fa kaji! Shiru yayi mata, sai dai zuciyar sa tana tambayarsa meyasa ynxun Mimi bata kiran sunansa? Bata cewa, Ismail, bata cewa, malam. Nauyinsa take ji, ko menene? Oho! Tayi, har ta gaji tayi shiru. Saida yaji kiran sallar la'asar, sannan ya shiga dakin. Har lokacin idanunta da hawaye. Ya kalleta, sai kuma ta bashi tausayi, yace, khadija! Taqi kallonsa. Ya gane alamun tayi fushi kenan. Yace, zan yi miki alwalla ne, nima zan tafi masallaci. Ta kumburo baki, to ka kiramin nurse Ramatu. Inaso inyi fitsari ne. Yace, ba zan kira wata ba. Muje in taimaka miki. Nurse dinnan fa da kkga tana kulaki, ina bata wani abu. Kwanakin nan da bani dashi, ban bata ba, kinga tana shigowa? Mimi tace, to fa, kai namiji ne, shine zaka taimaka min? Banida lokacin 6atawa khadija, sallah zanje. Menene zaki 6oyemin wanda ban gani ba? Kuma tunda ni matsayin wanki nake, ai ba wani damuwa. Ta zaro idanu, me ka gani? Bayan yaya Amina ce takemin komai. Da zaka ce... "kafin ta kai qarshen maganar, har ya dauketa cak ya sakata a toilet din. Ya zaunar da ita a kan kujerar da yaya Amina kan zaunar da ita in zatayi mata wanka. "sai kuma me zan taimaka miki dashi? " ka fita nidai kawai! Zaki iya yin komai harda fitowa? Tace, nidai ka fita! Murmushi yayi sannan ya fice, "to karki dade, kusan mintina hudu tace, "to kazo ka fito dani! Tayi maganar, ranta a 6ace. Ya shiga, inyi miki alwalla? Ta turo baki, "ni nayi abina. "A qasa yayi mata shinfidar sallah, yace, kiyi a qasa, tunda an kwance maki. Yasa mata hijabin sannan ya fita. Bayan ya dawo ya soma hada kayan da yaya Amina ta cire mata da safe. Yace, zanje gida inyi wankinmu, ya dan taru, sai kuma inyi wanka. Ta 6ata rai, cikin shagwa6ar ta tace, ni kuma ka barni da wa? Yace, da Allah mana! Dama shine mai tsarewa. Kinga kuma kinji sauqi babu laifi ko? Ya qarasa cikin sigar lallashi. Ta matse kafada cike da shagwa6a, idanunta suka soma zubo da hawaye, nidai bazan zauna ba. Ya ce, (cikin takaici ) karki zauna, inkin gaji da zaman Asibitin kidan taka mana, ki yarda kidan taka

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37