Chapter 13
Chapter 13
sati biyu da gama aikin hajji za'a koma hutu. Ka ga kuwa har zamuje mu dawo. Ismail yace, Allah ya kaimu lokacin, ai hutun ma ya qarato. Su Ismail sun dan tara kudi sakamakon wani aiki da sukayi tare da amincewar hukumar makarantarsu. Wadanasu masu hannu da shuni ne suka nemi makarantar ta taimaka musu da dalibai wadanda zasuyi musu rabon abincin sabil, da yake can qasar kowa so yake yi yaga an cinye nasa. Shine makarantar ta nemi dakiban ta tuntu6e su ko akwai wanda keson yi. Ismail da Mahmud suka shiga cikin sahun wadanda suke son yi. To anan ne suka samu kudi. Kamar yadda suka tsara hakan ce ta kasance, domin sunyi aikin hajji lfy sun gama lfy. sannan suka koma makaranta sukayi shirye-shiryensu suka nufi gida Nigeria. Abuja aka sauke su. Zukatansu fal da farin ciki mara misaltuwa. Ismail yace, gsky Gida daban ne, duk da cewa Abuja ba katsina bace, sai naji wani irin dadi, duk da cewa qasar dana baro tafi tawa komai, amma farin cikin na daban ne. "Ai Gida yayi." inji Mahmud. [20/09 12:59 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 3⃣8⃣A kaduna sukayi azahar, sannan suka dauki hanyar katsina cikin qosawa. Mahmud yayi murmushi don Jindadi, don cewa zaiga iyaye da kuma Rabi'a. Ya kalli Ismail, na qosa matuqa mukai Gida. Ismail yayi dariya, "wai kai wa kk zumudin gani ne haka?" Mahmud yace, su inna dasu Malam, sai kuma rabi'a. Ismail yayi murmushi. "Gara dai ka fadi gsky. Mahmud yace, gskyr kenan, kai wa ka qosa ka gani? Ismail yace, yaya Amina mana da 'yan yaranta, tunda ni ba uwa gareni ba bare uba. Sai dai 'yan Gidanmu da yayuna, duk da cewa, su ba lallai bane suyi murna da ganina. Amma harga Allah nidai ina sonsu, kuma nayi kewarsu. Haka ina kewar Malam sosai. Mahmud yace, kayi tuya ka mance da albasa, matarka fa khadija? Ismail yayi murmushi, "kasan harga Allah na manta da ita." Mahmud yace, sbd me? Ismail yace, sbd ko waya na kira, ba ko yaushe take amsa ba. Ba ta damu dani ba, shiyasa. Amma duk sadda zan sayi Tsaraba bana mantawa da ita. Mahmud yace, kenan bakayi kewarta ba? Ismail yace, ba sosai ba. Don nasan itama bata damu da ganina ba. Mahmud yace, kamata yayi kawai ka taho da ita in zamu dawo. Ismail yace, banajin hakan a jikina, ni kwanakinnan ma mafarkin Zainabu ke damu na, da kuma yawan tunaninta. Mahmud cikin jin haushi yace, wacece kuma zainabu? Nayi tsammanin ma ka dade da shafe babinta? Gidan wani fa take. Ismail yace, na dade da shafe babinta Allah kuwa. Tunda tayi aure, ka ta6a jin nayi maganarta? Mahmud ya girgiza kai. Ismail yace, ni kaina bansan dalilin dayada ta dawo cikin rayuwata ynxun ba. Mahmud yace, sharrin shaidan da mugayen mafarkai. 3⃣9⃣La'asar sakaliya, guraren qarfe biyar suka sauka garin katsina. Shatar mota sukayi zuwa gida, za'a fara sauke Ismail gidansu yaya Amina, domin suna kan hanya, sannan a wuce da Mahmud. Ta kan layinsu Zainabu zasu wuce, sbd Gidansu yana bakin titi. Tun kafin su qaraso yaketa leqen gidan. Daf da zasu gota gidanne, kamar cikin mafarki, idanunsa suka qyallo masa Zainabu ta fito daga maqotansu dauke da bokiti a hannunta. Da alamu ruwa ta debo. Ismail cikin sauri yace, Kalli Zainabu, Mahmud. Mahmud ya waiwaya ya hangeta. Yace, tabbas itace. Qila tazo ganin gida ne. Ismail dai yana can yanata waiwayen Zainabu har ta shige gidansu. Ya lumshe ido gabansa yana wata irin faduwa. Gida Zainabu tazo kamar yadda Mahmud yace, ko kuwa aurenta ne ya mutu? Mahmud ya lura da yanayin da Ismael ya shiga. Don haka sai ya harareshi, cikin salon son kushe Zainabu yace, duk ma ta tsufa, qila ma ynxun ta haifi yara uku. Da sauri Ismail ya kalleshi, "haba dai Mahmud! Sai kace, akuya, duka yaushe akayi mata auren? Mahmud yayi dariya, tsufan ne naga yayi yawa. Ismail dai bai tanka ba illa dai yanason sanin labarinta. Sadam yana fitowa an aikeshi sai kurum yaga mota ta tsaya. Shima tsayawa yayi, domin ganin ko su kawun nasa ne. Sororo ya tsaya yana kallon kawun nasa tamkar wani sabo fil. Da gudu ya juya cikin gida yana fadin mamanmu! Kizo ga kawunmu nan ya iso! Mimi ta rasa dalilin dayasa taji gabanta yayi wata irin faduwa. Tana daga cikin dakinta, ta sake jiyo saddam yana fadin, kinga kawunmu sai kace wani balarabe. Da sauri su yaya Amina suka fita, ga tsohon ciki, Ummi kam da gudu ta isa ta qanqameshi. Cikin murna suka gaisa da Mahmud, sannan aka kwashe kayan Ismail zuwa cikin gidan, sannan ya rako Mahmud zuwa gurin motar, sukayi musabaha, yace, ka gaidamin Malam. Sai na shigo zuwa dare. Ya koma cikin Gida, ya samu su yaya sunata yi masa shirye-shiryen inda zaici abinci. Ya Kalli yaya, dama ciki ne dake? Shine muna waya baki ta6a fadamin ba, da nayi miki tsarabar kayan jarirai da kuma pampers. Suna arha acan. Ina gani gurin abokan karatunmu masu iyali. Tayi murmushi, cikin kunyar qanin nata. Tace kurum sai ince maka inada ciki? Kafin ya sake magana tace, mu shiga ciki mana ga abinci. [20/09 12:59 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 4⃣0⃣Ta kalli Ummi, "kira auntynku mana, ko tana varci ne, sarkin varci." Ya kalli dakin, "dama tana ciki ne? Yaya tace, eh, sai dai ynxun haka varci takeyi. Yaya ta soma gabatar masa da abinci dana sha mai sanyi harda kaza aka soya masa. Yace da baku wahalar da kanku ba gurin soya min kaza, ko acan na jima banci ba, sbd ta hau min kai. Yaya tace, ai kuwa gashinan ka zama tamkar balarabe. Ka ganka kuwa? Ismail yayi murmushi, bari inci Alalata dai yaya. Yana ci suna hira. Ummi ta shigo tace, mamanmu aunty khadija tana varci. Tace ki tasheta kawai. Yace a'a ki varta kawai. Bayan ya gama, suka fito, yace, su saddam su kwashe kayansu sukai masa dakin khadija. Tana kwance tamkar mai varci, amma idanunta biyu. Gabanta ke faduwa tanajin jin qamshinsa, lokacin daya shigo dakin, bata ta6a jin irin qamshin ba. Yana tsaye yana kallon ta. Yaya ta shigo tasa hannu ta girgiza ta, "khadija ki tashi mana, magriba tabkawo jiki, ke varci baya yi miki wahala." Miqa tayi sannan tace, yaya kk ce mene? Tace, ki tashi Malam Ismail sun iso dazu. Shikam yana jingine da bango ya harde hannuwansa. Mamakin ramarta yakeyi, ga shi tayi baqi, ga qurarraji a fuskarta. Da ma ita ba qiba ba, sai tyi tamkar wata baby. Mimi kasa dago ido tayi ta kalleshi. Kanta a qasa tace, sannu da zuwa kawun su Ummi. Sunan data kirashi dashi yasa shi murmushi. Yace, yauwa sannunki malama khadija. Muryarsa da taji ta canza ne yasata dago kai. Jin muryar tayi tamkar ta balaraben da ya koyi hausa, ko ko bafillatanin da hausa bata isheshi ba. Mamakin kyawun surarsa ta bayyana a fuskarta, ta kafa masa ido, batasan lokacin da bakinta ya furta cewa, kai! Amma kayi kyau da yawa. Qasar ta canza ka, ta amshe ka. Yayi murmushi, a zuciyarsa yace, ina girman kan? Ya dubeta, nayi kyau? Khadija dama can ni mai kyau ne. Tadan ta6e bakinta tare da yin dana sanin fadar hakan a ranta, ta lumshe ido.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37