Skip to content

Chapter 34

Chapter 34

Canjin Rayuwa Book Four Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
Download Book

dai tasa hijabi. Mimi tayi ta mamakin Abbas, tace ban zaci zaiyi haka ba daddy. Shima yace, nima ban zaci basuda tarbiyya ba, har na takura rayuwarki. Ai nine silan komai. Kije ki kwanta. Zamuyi magana, sai an watse biki. Gado daya suka kwanta da Hajiya sauda. Mimi tasha labarinsu Na'ima. Hajiya sauda tace, ai gara wahalar da kk sha, da ace ke kk auri Abbas. Daddynku fa har cewa yai gara da Allah yada kk bijire masa. Mimi tace, ni ko inacan ina dana sanin bijire masa. Kuma lokacin don dai Nomy Nafisa tace min duk abinda Za'ayi kar in yarda, wai daddy yace in naqi yarda zaya haqura. Sai daga baya na gane kamar da makirci. Nan dai Mimi taba Hajiya sauda labarin komai. Hajiya tace, saida Hajiya Binta tayi zancen nan, amma nace kar a zargeta, dama 'yarta take son takai gidan. To ai in baka da haqqin mutum, gashinan yadda suka kwashe. Sun raba dare, suna hira kafin sukayi varci. Washe gari daurin aure, ansha sha'ani. Tela ya kawo dinkunan Mimi, sai shiga takeyi tana fita. Yaya Amina sunzo harda Rabi'a. Mahmud ya kawota don shima yayi mota. Sun ga kula, kuma sun kwashi kayan walima. Shi dai Ismail sai kallon Mimi yake, sbd kyawun data qara. Ta jashi ciki, wai ya gaida su kakarta, da kuma dangin mamanta. Inna sa'ade tace wannan Malamin nan bane shaikh Ismail bin Abdurrahman? Mimi tace, shine. "Dama shine mai gidanki? Mimi cike da alfahari tace shine. Sukayi ta sa masa albarka. Suna fadin shirye-shiryensa da suke kallo, da kuma irin qaruwar da sukeyi. 1⃣0⃣4⃣Haka da suka ratso ta falon mata, sai gaida shi akeyi irin gaisjwar ban girma, wadda mazoya suke yiwa wanda suke so. Haka biki ya tashi, sbd Amare sunada nisa. Mimi taso zuwa kai Amare. Daddy yace, ki bari ki sauka lfy, sai kije ma kowa. Tace to shikenan, ba don ranta yaso ba. Ta haqura don dan zaman nan ta san dadin 'yan uwa. Washegari duk mutane 'yan biki suna ta tafiya, don haka Mimi sake kwana tayi. Hajiya Binta da zasu wuce tace ma Mimi, sai kin haihu kuma zamu zo. Har mota mimi ta rakasu. Yau dai Alhaji da Hajiya da kuma Mimi sun zauna sun sha labari, inda Mimi ta basu labarin bayan rabuwa, suma suka bata. Kuma taji mamakin yadda Alhaji yabi diddigin inda suke. Ashe shine ma ya ba ismail gidannan. Kuma sai yau Alhaji ya gano Nafisa ta hada komai, don mimi ta fada masa har yadda tasa ta ta turo masa text. Ransa ya 6aci, kuma yace, sai yaci mata mutunci. Hajiya sauda tace, a'a karka yi mata komai. Banqi ka fada mata ba, don tasan ka sani. Amma ai Allah ya gama nuna mata sakamakon maci amana. Mimi tace, hakane daddy. Take ta kira ismail, ta fada masa yazo, shima yasha labari. Kuma sai ranar yaji dalilin daddy na sharesu, kuma ya gamsu. Domin in har Mimi tana cikin gatanta ba zata juyu agareshi ba. Sun bar gidan goman dare. Bayan motar su shaqe da abubuwan biki. Suna kwance sunyi kewar juna tace, Malamina yaushe zamu koma Abuja? Yace sauran kwana uku, kin manta ko? Tace na manta sosai kuwa. Ai naji dadin zuwa gida lokacin bakinnan . Naga 'yan uwa, sun ganni. Ta rungumo shi, Allah barni da kai har abada. Yace, Amin tace, kayimin alqawarin cewa ba zakayi min kishiya ba. Yace, Dija banida ra'ayi, amma bansan qaddarata ba. Ina son kema kimin alqawari, in qara aure yana cikin qaddarata ba zaki juyamin baya ba. Ta qanqameshi, "nayi maka, amma zan shiga wani mawuyacin hali, sbd ina tsananin sonka. [30/09 6:43 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 1⃣0⃣5⃣Washegari sunyi girke-girke sbd ziyarar dasu daddy zasu kawo musu, da su yaya Abba da sauran qannenta. Yaya Amina da Rabi'a sune suka taya su. Gidan tamkar biki, haka ya cika. Daddy yaba Mimi kyaututtuka sannan kuma ya fada musu yaba sauran 'ya'yansa irinsu, sakamakon wa'azin da yaji a wani kaset daya kalla na Ismail, mai taken yin adalci ga iyali. Sannan yayi wa ismail kyautar qaton fili, yace ya gina irin makarantar da yakeso. Take ya yanke shawarar zai gina jami'a ta musulunci, duk da ya san ba abune mai sauqi ba, amma zaiyi hakan. Su Malam Aminu sun samu kyaututtuka. Shi kujerar makka, mahmud gida. Sunkai har dare a gidan, sannan suka tafi. Ranar da zasu koma Abuja, sunzo sallama daddy yaba su makullin wani gidansa dake Asokoro, yace su zauna har sai ranar da suka gaji suka tashi don kansu. Ranar wata talata, Mimi ta tashi da naquda, ismail bai fadama kowa ba, saida ta haihu. Kuma abin da ya burge malaman asibitin mai zaman kansa, yadda ismail ya shiga har cikin dakin haihuwar yana shafa kan matarsa tare da lallashi da addu'o'i har ta haifi santalelen yaron su mai kama da su. Hajiya sauda ya soma fadawa, sai daddy da kuma su yaya Amina. Duk da sun yanke cewa gida zata dawo, saida su Hajiya sauda sukaje Asibitin da take a Abuja. Shi kansa Alhajin saida yazo. Momy Nafisa tazo asibitin, sai kunyar Mimi takeji, sbd Alhaji yazo ya warwareta, kuma ya fada mata cewa taci darajar sauda, sbd itace tace, in barki da ishararki. Ranar ta kira sauda tana bata haquri. To yau kam ta yarda cewa, duk wanda yace, tukunyar wani ba zata tafasa ba, tashi ko dumi tabar yi. Yadda taga Mimi, Mijinta yana ji da ita, ga daukaka, ga kuma soyayyar da take yiwa mahaifinta ta dawo sabuwa. A katsina gidan suna ya cika. Dan yaci suna Aminullah, sunan Malam Aminu, Ismail yasa, domin ya nuna masa qauna. Hasana da Usaina sunzo. Abin sha'awa suke ta kula da 'yan suna. Gurin bada abin tsaraba in mutane zasu tafi, sun samu alheri. Malam Aminu kuwa yaji dadi sosai, wannan kara da ismail yayi masa. 'yan gidan su ma sunzo. Zo kaga idanu gurin fatu, sun ga abin duniya, abinci kuwa sunci sun diba a leda, duk da Mimi tasa anyi musu kyaututtuka na musamman matsayin dangin masoyin mijinta. 1⃣0⃣6⃣Kwanaki arba'in sukayi, duk sati Malam ke zuwa duba su. Abin da yaba Mimi mamaki ta kuma qara miqa masa wuya, yadda shine ya kawo mata abubuwan da zata yi amfani dasu don gyaran jikinta, sannan ya fada mata abubuwan da zata yawaita ci. Yaso sunayin arba'in su dawo, amma tace yayi haquri sudan zaga suga 'yan uwa. Da gusau suka soma (har naji kamar in bisu inje gurin tawa Baida'u Gada) sannan kaduna, duk kwana dai-dai sukayi, sannan suka dawo, sukaje Dangin Hajiya sauda. Sun zaga acan kwanansu biyu. Duk da ba masu kudi bane , taga soyayya irin na dangin uwa. Sannan sukaje masari suka kwana daya, daga nan sai Malumfashi gurin Hajiya Binta. Bayan sun dawo ne kuma suka soma shirin komawa gida Abuja. Har da Hajiya sauda da yaya Amina a 'yan rakiya. Qannenta kuwa su Hasina dasu husna, harda kuka don sun saba da Al'amin. Shi kansa Alhaji yayi keawar dan jikan nasa. Ranar 'yan rakiya suka dawo suka barsu da kayan arzikin da suka rakasu da shi. Qarfe taran dare, Mimi cikin kayan varci, tana ta lila Al'amin a gadonsa ya soma varci, sai taji qamshin turaren masoyinta, kafin

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37