Skip to content

Chapter 27

Chapter 27

Canjin Rayuwa Book Four Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

yace shikenan zan kula insha Allah, nagode. Gidasa ya wuce, sai da yayi wanka ya huta, sannan ya fita zuwa gidan yaya Amina. Yayi matuqar qosawa Mimi ta dawo, ko don Abinci. Gashi a gida mai kyau, amma abinci sai ya siya. Can yaci abinci, sannan yace, yaushe zaku raka mimi can gidan? Tace sai jibi. [26/09 10:32 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa Washegari ya samu halartar gayyatar da akai masu. Maqasudin zaman dai, sbd tafsir ne na Azumin dake gabatowa. An yi musu jan hankalin hadin kai, su daina zagin juna, da kafirta juna. Sannan kowa yayi wa'azinsa ba tare da izgilanci ba, ko cin mutunci. Ka abinda Allah da manzan sa sukace, a tsage gsky komai dacinta. Malamai sunyi bayani, inda shima ismail yayi nasa bayanin, wanda ya gamsar da dukkan mahalarta taron. Sbd ismail, Allah ya hore masa hikimar iya magana. Shi mutum ne wanda zaiyi wahala yayi maka bayani baka gamsu ba. Bayan an fito ne, ismail ya miqa hanya da nufin neman dan aca6an da zai kaishi gida, sa6anin sauran malaman da suka zo da motocinsu. Wannan dalilin shine ya kawo inda aka bincika cikin malaman da suka halarci taro, aka fidda guda hudu wadanda basuda abin hawa. Washegari saiga mota sabuwa dal, babu ko lamba an kawowa ismail. Lokacin da Malam Aminu ya kirashi yazo, shiru yayi ya kasa magana, lokacin daya gabatar masa da motar. Bai san da wace kalma zai fara magana ba, duk wani alheri da zaizo masa ta gurin Malam Aminu yake tahowa. Yace Malam, Allah ya saka maka da aljanna. Sunyi ta murna. Ya kira mahmud. Dama mahmud ya iya mota. Nan suka shiga suka zagaya gari, tare da zuwa gurin abokan arziki. Sunje gidansu, inda 'yan gidan suka fito suka ga mota sunata murna. Ta fito wanka , tana shafa, ummi ta shigo da gudu. "Aunty zo kiga motar kawunmu, sabuwa dal, baqa kuma qatuwa. Mimi tayi dariya sbd yadda Ummi ta jero maganar, tare da cewa, Allah yasa alheri. Sai gashi da kansa, khadija kizo ki gani mana, munyi mota. Mimi ta miqe taje taga mota, kuma tayi murna. Yace ki shiga mana ko kin manta da yadda akeyin tuqi? Murmushi tayi, sannan ta amshi makulli, su Ummi suka shiga, ta tashi motar ta tuqa zuwa cikin layi, suka dawo. Ummi sai mamaki takeyi, tana cewa, anty yaushe kk koyi tuqa mota? Ismail ma cewa yayi ashe baki manta tuqin ba. Tace in manta tuqi? Ashe zan manta da yadda zanyi tafiya da qafata. Suka sa dariya. 8⃣3⃣Washegari Ismail da mahmud suka soma fita don koyo ma ismail tuqi. A yammacin ranar ismail, ya kira yaya Amina yace, su shirya zasuyi tasu walimar a gidansa. Bayan la'asar suka zo kwashi su yaya Amina, suka biya suka dauko Rabi'a da innarsu mahmud. Bayan sun kaisu ne, sai suka koma suka dauko su inna, dasu fatu. Dukda ba wani alatu. Ismail ya zuba a gidanba, gidan yayi kyau sosai. Katifu ne a dakunan da sabbin zannuwan gado da fuloli, sai labulaye masu tsada. Sai falon ne ma ya gyarashi sosai, don tsadaddun kujeru ya zuba da kafet din tsakiyar, shi ma mai tsada ne, TV da sauran kayan kallon zamani. Sai dai falon saman bai saka komai ba. Yace sai ahankali zai saka komai. Mimi taga qorarinsa sosai, tunda tasan shi talaka ne. Sun je sun kawo musu abin sha na gora. Daf da magriba suka koma kai su innarsa, sannan su yaya Amina. Mimi harda kuka wai abar mata Ummi. Yaya tace a'a za dai tazo miki hutu, kuma kinsan zata tayani aiki, ga makaranta. Mimi tace yaya baga saddam ba. Kuma indai makaranta ce ai zan kaita tunda ga mota a hannun kawunsu. Tace kiyi haquri har suyi hutu. Ismail dake kallonta burgeshi takeyi, don yanason shagwa6arnan tata. Shiyasa ma yaqi sa musu baki, don yanason kallonta a haka. Ita kuwa yaya Amina, taqi barin Ummi ne don zamansu, su biyun wata hikima ce, tana sa ran su shirya kansu. Sun barta da Rabi'a in sun dawo kaisu yaya, sai mahmud ya tafi da matarsa. Bayan tafiyar su ne, sai kuma suka shiga kicin don ganinsa. Freezer ce, sai tukwane da kuloli, plates da cokula, amma babu risho ko wani gas. Rabi'a tayi dariya, tace to da me zakuyi girki? Mimi tace oho masa. Suka koma sama sukayi sallah, sannan suka dawo qasa suna 'yar hira. 8⃣4⃣Ranar Mimi harta dan saki jiki da Rabi'a, don ta lura Rabi'ar ta san me takeyi. Rabi'a tace, niko da ace zaki yarda da na baki shawara. Mimi tace, me zai hana? Rabi'a tace kar kibar wata mace ta shigo gidannan a matsayin matar malam ismail. Mimi ta tattaro hankalinta gurin Rabi'a. Ta yaya zanyi hakan? Nasan dai kinsan komai dake tsakaninmu da malam din, tunda Aminin mijinki ne. Bafa son juna mukeyi ba. Rabi'a tace ni kuwa sai ina kallon so acan cikin qwayar idanunku. Na farko da baya sonki, da tuni ya sakeki. Rashin sakin jikinki shine ya hanashi nuna miki. Mimi tayi murmushi, ya fada miki ne? Rabi'a tace a'a nice nayi hasashen hakan. Mimi tace bana zaton zai soni, sbd na samu labarin yadda yakeson wata Zainabu. Rabi'a tace, tabbas yanason zainabu, amma da kinso, da tuni kin mantar dashi ita. Kiyi tunani. Mimi ta sauke ajiyar zuciya, ni damuwa ta ma ko auren namu yananan daram ko ya lalace? Oho. Kafin Rabi'a tayi magana, sai gasu sunyi sallama. Don haka, sai suka rufe bakin hirar. Tare suka tafi dukkansu, aka kulle gidan. Mahmud ne ya jasu zuwa gidansu. Sun danyi hira, sannan Mimi ta jawosu zuwa gida. Ismail yaji dadin yadda Mimi ta saki jiki da Rabi'a. Bayan tayi wanka tayi isha'i, ta saka kayan varci, ya buga qofarta, taja hijabi ta saka, sannan tace, shigo mana. Bakin katifa ya zauna, sannan yace kinga dan kayan dake kicin din ko? Sai a hankali zamu qara abinda bamuda shi. Tace maimakon kabar wani abin ka siyo gas ko risho, to dame zamuyi girkin? Ya zaro idanu, alamun sam ya manta da Risho. Sannan yayi dariya, lallai yau akeyinta. Sam na manta fa. Kinsan abubuwan da yawa, gashi ba wai inada kudin bane. Amma karki damu zuwa gobe ko risho dinne, sai in samo. Gas daga baya zamu samu. Ina son ma ki zauna ki rubuta abinda muka fi buqata, sai muyi ta siya a hankali. Ki fara da wanda muka fi buqata. Tace mu bari saida safe. Yace rubuta dai ynxun. Ta dauko takarda da biro, shi kenan dame zamu fara? Yace kayan gado, sai falon sama, abubuwan cikin ban daki, sai me? Tayi dariya sannan ta soma tuno wasu tana fada, suna rubutawa. Sun kai kusan sha daya, kafin yace mata bari ya tafi saida safe. [27/09 7:59 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 8⃣5⃣Ya jima kafin yayi varci, sbd gsky haqurinsa zai gaza. Ko da bayason Mimi, to yasan yana muradinta a gefensa. Ballantana yana da tabbacin cewa wani sashe na zuciyarsa yanason Mimi. Duk lokacinda yazo da niyyar sanar da ita hakan, sauta 6ullo masa da zancen saki, sai dai wasu abubuwan da takeyi, sai yana zargin cewa tana sonshi. Washegari da safe, yana zaune a falon qasa, yana duba wani littafi, ta sauko tayi wanka tasa

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37