Chapter 30
Chapter 30
wannan ba huruminki bane. Wadda zan aura sai kin za6a min, sai kace uwata? Ok, na gane nufinki, wato tunda baki sona kar wadda ta soni ko? To na gaji da wannan mulkin naki. Kuka ta soma, tare da fadin dole ka barta, kamar yadda dole tasa na haqura da khalil. Yace in ba haka ba fa? Tace za kayi da ka sani. Mahmud dake kallonsj, bai katsesu ba, sai yayi murmushi. "Da ace zaku fito da abinda ke zukatanku, wlh da kun huta. Sukayi shiru. Yace shikenan zainabu an bar maganarta. Zai canza wata. Haka yayi miki? Tace eh. 9⃣1⃣Ismail zaiyi wata magana mahmud ya daga masa hannu, tare da fadin an wuce wannan. Ka samu Malam, akwai wani sanata faruk da ya samu malam da maganar 'yarsa. Banji dai kan zancen ba, amma tabbas naji malam yace mutumin ya baka 'yarsa. Ismail yace, Hanan umar faruk kenan. Nasan yarinyar daliba ta ce a Abuja. Tanan kuma ta biyo? Mahmud yace bakamin zancenta ba. ismail yace banida ra'ayin auren yaran masu kudinnan, amma tana da hankali. To in anyi haka ya zanyi da zainabu? Banyi mata adalci ba. Duk zantukan da zukeyi, mimi mutuwar zaune tayi. Sai alokacin ta gane ba wai zainabu kawai take kishi ba. Duk matan duniya takeyin kishi dasu akan mijinta. Saidai ba tada ikon cewa komai akan wannan. Sun juya harshensu zuwa larabci, inda ismail ke qorafin ba'ayi ma zainabu adalci ba. Mahmud yace kafin kayi masu, sune suka fara yi maka. Sannan yarinyarnan tana matuqar sonka. Ina mamaki da kullum kuna tare, amma ni na gane hakan, kai ka kasa. Ismail yace nima inaso in fahimci hakan, sai tayi ta maganar saki, saki. Shiyasa naga kawai in haqura. Yace to ka gwada mana, zaka iya ganewa ta hanyar ta6a jikinta. Mahmud kaqi yarda cewa kana sonta. Alhalin shine dalilin daya hana ka daketa. In kaqi yarda dani ynxun, zaka yarda dani a gaba. Mahmud ya miqe, tare da cewa, bari inje gida nima, kar Rabi'a ta kullemin qofa. Ismail ya kalli mimi, ya tausasa murya, ina makullin motar in saukeshi a gida? Ta kalli kujerar da suke kai, tana qasan nan. Suka ciro suna dariya. Ismail yace babu irin leqen qasan kujerar nan da banyi ba, ashe yana ciki. Sai daya miqe mahmud yace, dama saboda ta nuna makullin nayi shiru, amma da mashin nazo. [27/09 9:55 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 9⃣2⃣Bayan ya rakashi ya tafi, shi kuma ya kulle gida, ya kulle qofa. Har lokacin mimi tana zaune anan, amma ta zurfafa a tunani. Wacece Hanan? Ya zauna kusa da ita, "khadija hakan yayi miki ko? Ta kalleshi firgigit, batasan ma yazo kusa da ita ba, ta sauke ajiyar zuciya, "wai itama Hanan din kana sonta? Yace ban sani ba, sai naje na ganta sosai. Ya kalli cikin idanunta data tsareshi dasu. Kishi ya gani qarara a ciki. Tace, itafa tana sknka? Yace gsky tana sona, domin ta nuna min alamu. Tace, dama kana iya gane alamun mace, tana sonka? Yace, sosai kuwa. A ranta tace, to baka qware a wannan fannin ba, tunda ka kasa gane irin wanda nakeyi maka. A fili sai tace, tanada irin kyawun da kake so kenan? Yace banyi mata kallon qurilla ba. Ya rufe wannan da cewa, yau kin tsorata ni. Don Allah karki sake yi min haka kinji? Kallonsa kawai Mimi keyi, amma ita tamaicinta yafi tunaninsa. Ta miqe, bari inje in kwanta. Yace duk yinin da kikayi a gado a kwance baki gaji ba? Tace, karka damu bana gajiya da varci kai ka sani. Ya bita da kallo, damuwarta tana matuqar damunsa. Ya miqe shima yabi bayanta. Tana fitowa ban daki ta ganshi zaune a bakin gadonta. "Lafiya?" ta jefo masa tambaya. Yace, babu inda yake miki ciwo? Ta girgiza kai, a'a yace naga kina cikin damuwa ne har ynxun. In dai maganar zainabu ne ki dauka ya zama tarihi. Tace kaje ka kwanta kawai, ya wuce nima. Ya miqe ya nufi fita, sai kuma idanunsa suka hango wayarta dake kan madubi. Yace waccan wayarfa? Tare suka isa gurin, ya rigata dauka. Cikin sa'a ta amshe, tare da cewa, wayata ce bani. Yace shine baki ta6a kirana ba? Tace, ni bana kira da ita, sai dai inajin rediyo. Yace shikena saida safe. 9⃣3⃣Ya jima yana kai-kawo a dakinsa, zai tattara alamomin so da mimi take nuna masa, to me zai hana ta fada masa? Kuma meya kawo ta dinga batun saki? Wata zuciyar tace kaima ya kamata ka tantance kanka, shin kana sonta ne? Ko tausayinta kk ji? Ko ko sbaquwa ce? Can qasan zjciyarsa sai yaji an amsa da cewa duka ka hada. A fili yace, khadija! Babu batun saki. Ko da baki sona, balle zan gwada ki in gani. Washegari da safe, tana kicin tana hada masu abin karyawa, ya shigo cikin rashin walwala, ta kalleshi, "barka da safiya? Yace barkanmu. Ya kusanto ta, "bar ynxun baki huce ba Dija? Ko itama Hanan din baki sonta ne? Ta kalleshi, sannan ta ta6a baki. "in kai kana sonta, me ya shafi khadija? Yace Allah in bata miki ba, sai in fasa. Ta zaro ido, ni asuwa dan wake a hotel? Yace da gske nakeyi, amma in zaki yarda da wani sharadi guda daya. Tayi 'yar dariya, "inji sharadin. Yace zan turo miki a message. Sai ki bani amsa. Tace, sbikenan ina jira. Ta dauki tiren da abicin karin su, muje mu karya. Ya lura da yadda ta saki ranta daga yin wannan 'yar maganar. Suna karyawa, kowa da tunaninsa. Bayan sun gama ya miqe bari in fita. Tace Allah ya tsare. In ka shigo anjima zanje na wanke gashi na. Yace ki bari na kaiki da dare. Da mimi taji alamun shigar saqo a wayarta, sai ta duba, sai taga MTN ne. Kusan biyar na yamma ya dawo. Tayi kwalliya cikin riga da siket na atamfa. Ta yi masa sannu da zuwa. Ledojin daya shigo dasu ta amsa ta nufi kicin. Ya biyo ta a baya, kin jini shiru ban dawo ba? Tace nasanka da uzuri ai. Daidai lokacin ta bude ledar, kaji ne guda hudu, sai dayar kuma danyen kifi. Ta soma zubawa a freezer, tana cewa farfesun kifi zamu sha anjima kenan? Yace naje sai miki kifin, sai ga wani bawan Allah. Sai kawai ya biya, Kuma yasa asa min kaji. Shiyasa kk ga bana son yin siyayya a unguwar da aka sanni. Sai kawai wani yace zai biya. Tace, arziki ne hakan ma. [28/09 3:34 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 9⃣4⃣Yace bari inje inyi wanka, zamu fita da ismail. Gabanta ya fadi. Ina kuma zaku je malam? Ya dubeta, gidansu Hanan. Ta rufe freezer, sannan ta biyoshi, to ba ka fadi sharadinka ba. Ko dama kana yi min wasa ne? Yace oh na manta. Ina zuwa. Ya shiga dakinsa, bakin gado ya zauna. Ya rubuta cewa, "in kin yarda in sumbaci bakinki sau daya kullum, to zan haqura da Hanan. Idanu ta zaro, tana qara maimaita abin da ta karanta. Sai taji tanajin kunyar bashi amsa, amma tunda ya ta6a bata amsa da cewa shiru alamu ne, to tayi shiru. Baiga amsa ba. Don haka yayi shirinsa na fita. Ba wani gidansu Hanan zasu ba, don dai ya gwada tane. Rashin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37