Skip to content

Chapter 32

Chapter 32

Canjin Rayuwa Book Four Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
Download Book

JI dashi. [29/09 7:22 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 9⃣7⃣Bayan sallar isha'i ne ta leqo don yi masa sai da safe, "yau baki amshi karatun ba" Tace wane karatu? Yace, kin manta ne? Jiya fa kk ce in dinga koya miki karatu. Tace ai jiya ne kawai nace. Yace, naga alamun kin manta da karatun da nike nufi. Zokiji, ta zauna a gabansa yana kan sallaya. Jallabiya ce, a jikinsa mai ruwan qasa, kuma mai gajeran hannu. Ta lura yayi wanka ne bayan fitarta. Ya matso da bakinsa kunnenta, abinda ta zata shine ya fada mata. Ta zata ya manta, domin tana sane ita, kuma tana ra'ayi. Don haka zama ta gyara. Ya tallafe fuskarta suka kalli juna a cikin ido. A hankali yake magana. "INA SONKI KHADIJA..." Wani dadi taji ya rufeta. Har ma ta lumshe ido, lokacin ne ya saukar da la66ansa akan nata. Sai da ta koma tamkar ba tada rai sannan ya barta, don in yace, zai wuce gona da iri ma ya lura ba zata hana ba. Amma yanason koya mata komai daki-daki. Don sai ya raina wayewar da take iqirarin tayi. Domin ya lura batasan komai ba a wannan karatun. Rana ta uku ne ta soma biya karatun daya koya mata. Don haka a dare na hudu, sai yace, suyi wata sallah raka'a biyu. Bayan sun idar ne, ya dubeta, "kin san sallar nan da mukayi ta mecece?" ta girgiza kai, yace ta ma'aurata ce. Yau karatunmu zai canza salo. Kije kisa turare a duk ga6o6in jikinki kizo. Sam bata iya yi masa gardama ynxun, ko menene dalili? Oho! Tabbas yau sabon darasi ne, sai da karatun yayi nisa, sannan ya rada mata a kunne, "in barki haka ko? Tace, da wuya? Yace ba zan bari kisha wuya ba, sbd naga ke budurwa ce har ynxu. Idanuna ba zasu iya kallonsu ba. Don haka na tura qofa a hankali na fita don barin ma'aurata da sirrinsu. Saidai daga bakin qofa nake jiyo ismail yana karanta addu'ar da mazaje na qwarai sukeyi lokacin kusantar iyalinsu. A fili nace, "an kashe Boss kenan." ban koma dakin ba saida na kusan awa biyu. Lokacin dana leqa ban gansu ba . A raina nace, suna bandaki. Ina nan la6e suka fito. Ya kwantar da ita, shi kuma ya shimfida sallaya. Nace su mimi Amaren asali, kin kai masa mutunci. Shi kuwa sallar godia ce ga Allah yayi. Da asubahi mimi batayi ragwanta ba, tashi tayi ta nufi dakinta don yin sallah. Bayan ta idar, ta kwanta a gadonta, tana tuna abinda ya faru jiya. Gsky Malam ya wuce da tunaninta. Mamakin sa kawai takeyi, dama zata iya tambayarsa, da tace, ina ya koyi salon sa mace ta manta da duniyar da take? Sai dai kashh, tanajin kunyarsa. Barci yayi gaba da ita. 9⃣8⃣Ismail daga masallaci dakinta ya nufa ya kwanta bayanta ya rufesu. Barci sukeyi tamkar wasu taurari. Naso in musu hoto. Sai tara saura ya tashi. Shine ya hada musu abin kari. Lokacin daya dawo saman tana wanka. Ya tsaya jikin bayin, "inzo in taya ki? Tace na gama. Ta fito ta kasa kallonsa. Yana zaune ta gama shiri, harda taya ta gyara gashin kanta. Suka nufi qasa don yin karin kumallo. Cikin sati dai ismail baya nisa, launukan karatun da yake koya ma amaryar tashi kam babu dama. Itama batason yayi nisa, shiyasa ma ta yanke a ranta in zai koma Abuja ba zai barta ba. Haka kuwa hutunsa yana qarewa, tace, Malami na zaka dani? Yace dama izininki zan nema. In kinji zuwa daya kenan. Da ma kema ki soma karatunki. Tace amma zan canza layi. Islamic zan karanta, don sai ynxu na fahimci Musulunci yazo da komai na wayewa. Sam ismail ya manta da wata zainabu, khadija ce a gabansa, wadda yake kira my Dija. Kafin wani lokaci, mimi tayi kyau, ta goge. Da kanta tace, ismail ashe na jima ina cutarmu. Kuma ka san na dade ina sonka? Yace, na gano haka tun ranar dana saci wayarki na bincika sai naga ashe kece matar dake ta damuna a wtsapp. Tayi dariya, shine baka fadamin ba? Yace gashi ynxun na fada. Yaya Amina kuwa tunda taga Mimi, tasan an kashe boss, domin ta ciko masha Allahu. Sam Na'ima basu ta6a haduwa da mimi ba, ko don ba department daya suke ba, oho. Lokacin da Alhaji ya dawo daga ingila, sai ya samu labarin Mimi suna Abuja kuma tana karatu. Yaji dadin haka, kuma ya jinjina wa malam ismail. Shima ismail ynxun abu daya ya rage masa, shine ya sada Mimi da iyayenta. Amma ya bari sai sunje katsina. Cikin haka, Mimi ta soma laulayi. Ta ga gata ganin idonta. Har da kanta ta darsa a ranta cewa data bar ismail, da ta tafka asarar da ba zata iya maida ta ba. Kullum tayi sallah, sai ta godewa Allah, ta kuma godewa mahaifinta daya za6a mata ismail, ta samu CANJIN RAYUWA. 9⃣9⃣Cikinta wata bakwai sukazo katsina, domin za'a bude makarantarsa, kuma zaya kai Mimi gidansu. Bayan an gama kai kawon bude makaranta, da sati daya, tuni ma an soma karantarwa. Ya danqa komai gurin wani bawan Allah dake nan unguwarsu malam Aminu. Shine ma ya kawo shi, yace tunda Ismail baya zama. Sai ismail ya amince, don yasan malam ba zai kawo musu bara gurbi ba. Kuma ya zuba qwararrun malamai a makarantar. Safiyar juma'a, Mimi tana kwance kan cinyar ismail, yace muje in taimaka miki kiyi wanka , zamu fita. Tace zuwa ina malamina? Yace inda muka kwana biyu bamuje ba. Kinsan falalar zumunci. Gashi ke nake jira ki haihu, zamu tafi Madina don neman digiri dina na biyu. Bayan ta fito tana zaune, ya shafa mata mai, sannan yace, wane kaya zamu sa? Tace ka san dai yau juma'a, kuma kamar yadda muka tsara ma kanmu rana ce ta saka kayanmu na al'ada. Dubamin shadda ko atamfa. Sabbin riga da zani ya fito mata dasu na super mai kalar popple, sai ratsin baqi, har da sarqa da dan kunne masu kyau yasa mata. Shima ya shirya tsaf, cikin shadda sabuwa. Tasha hijabi da niqabi, suka shiga sabuwar motar da yayi kakara, ya canza. Saida sukayi tsarabar kayan sha, dana zaqi, sannan ya tuqa su zuwa unguwar. Sam Mimi bata fahimci inda suka dosa ba, sakamakon an samu canje-canjen gine-gine. Wani gurin ma babu gini da. Ko gidansu, saida suka shiga ta ganeshi, sakamakon an canza gaban. Ta kalli ismail, "yaya zaka yi min haka? Gsky mu juya, tunda ba wanda ya ganmu. Yace ni ba wannan ya dameni ba. Baki lura da yawan motocin da ke harabar gidannan ba? Sannan ga mutane can ansa rumfa. Da alamun anayin wani abu agidannan. Kai tsaye tace, Allah dai yasa ba daddynh bane ya rasu. Sai kuma ta bude qofar da sauri, ta fito. Shima ya fito, ya riqeta. Yi sannu My Dija. Babu abinda ya faru, sai alheri. Alhajin ne suka fito daga falonsa tare da qaninsa kawu shafi'u da kuma su Alh kabiru, da Alh isah. [29/09 8:26 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 1⃣0⃣0⃣Ismail yace, to ga Alhajin nan ma. Da sauri ta nufesu tana fadin daddynah! Cak ya tsaya domin ko cikin mjrya dubu zai fidda ta Miminsa, ko da zai shekara dubu bai ganta

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37