Skip to content

Chapter 25

Chapter 25

Canjin Rayuwa Book Four Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
Download Book

ni bari in tafi. Tace zuwa gurin cin abincin fa? Yace mu barshi sai zuwa wani lokaci, zan sha tea in naje gida. Hankalin Mimi yayi qololuwar tashi, tace, ynxun fa kazo amma har zaka tafi? Yace inada wani uzuri ne, karki damu zan dawo da safe. Bata iya amsa shi ba ya fice. Kai kawo ta dinga yi a dakin. Ta gama yarda cewa tanayi ma ismail wani mugun so, shi yanason wata kenan. Ta fita zuwa dakin yaya Amina ta zauna. Yaya tace yau naga malam ya fita da wuri. Mimi tace, yaya in tambayeki mana? Yaya tace ina jinki. Mimi ta tsura ma yaya ido, wai wacece Zainabu? Yaya tace Zainabu? Kinsan tane? Mimi ta sake tambaya. Tace umm, wata yarinya ce da ismail yayi mata wani mahaukacin So, shine iyayenta suka yaudareshi, suka bada ta ga wani mai kudi. Zufa ta karyo wa Mimi, ta miqe. Yaya tace, yayi miki zancenta ne? Mimi tace kawunsu ummi ne naji suna waya, ta fada masa aurenta ya mutu shine fa ya fita jiki yana 6ari. 7⃣7⃣Yaya Amina ta miqe tsaye tabdi! Ai ko duk nacinsa ba zai aureta ba! Shegiya, ko wa ya bata lambarsa? Tuni nasan aurenta ga mutu, amma na share ban fada masa ba. Saboda kar ya koma mata. Mimi cikin fargaba ta miqe tare da fadin saida safe. Yadda yaya taga hankalin Mimi ya tashi ne ya bata mamaki. Har ta miqe da nufin zuwa ta bawa Mimi shawara, sai kuma ta fasa, tace bari in barta ta fara yin shawara da kanta tukunna. Yarinya kinada miji tun tsawon lokaci, amma me kin dage sai an rabu dake. Daga ganin ta kasan kishi ne can qasan ranga. Ta koma ta zauna. Mimi kuwa tana shiga dakinta ana kawo wuta. Sam bata damu da wutarba, duk da cewa fankar data soma kadawa tana kai mata iska. Sitiri kawai takeyi tsakar daki. Ta rasa wane irin tunani zatayi, ta rasa wa zai bata shawara. Ta zauna bakin gado. Na shiga uku na, ni khadija wa zai bani shawara ynxun? Kalaman yaya Amina ke mata yawo cikin kai, "wata yarinya ce da ismail yayi wa mahaukacin so. Ta maimaita sunan wai Zainabu. Ta tuna yadda ya miqe zumbur lokacin da ta ambaci sunanta. Ta tuna yadda ya manta da ita a dakin sbd zainabu. A fili tace, lallai za'ayi tan kuwa. Wani tuquqi ne ke taso mata daga qirji, tace, qila ma suna can tare. Ranar dai su Mimi ba'a runtsa ba, sannan bata qulla ma kanta mafita ba. Barci sama-sama tayi shi har asubahi. Sai da tayi sallah sannan varci ya dauketa. Ta kai kusan tara na safe sannan ta farka. Ta fito da nufin gaida yaya, sannan tayi wanka, sai kuma taga yayar sanye da hijabi zata fita. Tace ina kuma zakije yaya? Tace nan maqota zan shiga aikin biki, wannan gidan da sukace muje muga lefe. Kinsan yau ne daurin auren. Mimi tace, wai dole ne jn mutum yananan garin sai ya shiga aiki kenan? Ban saba ganin haka ba. Mu in zamuyi biki, ko suna sai akai gurin yin abincj ayi a kawo. Yaya tace, sha'anin masu kudi kenan. Mu nan in baka zuwa, wa zaizo maka? Bakiga sunan Aishatu ba, gidannan cika yayi? Kinsan dai in bana zuwa ba za'a zomin don tsorona ba. Mimi tace, sai kin dawo. Ni dai bana ra'ayin haka. Tayi 'yar dariya. Aishatu tananan tana varci a uwar daki. Mimi tace to. Ta dauki ruwan wankanta wanda ummi ta zuba mata, kamar kullum tunda bata iya jan ruwa. 7⃣8⃣Tana wanka taji shigowar ismail, yana ta sallama ba a amsa. Tana jinshi yana cewa, inma dai yaya Amina batanan, yasan babu inda Mimi zataje, qila tana bandaki. Saida Mimi ta gama ta fito, sannan ta dauki Hijabin Ummi dake kan igiya ta saka. Ta shiga dakin. Yi tayi tamkar bata ganshi ba. Ta wuce, kan madubi ta zauna tana shafa mai. Ta zame hijabin, ya sauka a wuyanta, dogon gashinta ya bayyana. Ta dauki mataji tana tajeshi. Baqi sidik. Ta lakuto manta na gashi tana kallon gashin cikin madubi. A ranta tana cewa, inda nagode ma Allah, duk lalacewar da nayi gashina bai zube ba. Ta kalli fuskarta a madubin, tace wai wane irin kyau mutuminnan yake buqata wanda yafi nawa? Sai dai ko in balarabiya yake son ya aura. A fili tace, zan so ni kuwa inga zainabun nan wace iri ce ita? Kyanta yaya yake? Yace me kk ce? Cikin sauri ta waiwaya, ta dubesbi. Yace yau 'yan miskilancin ne ko? Kin shigo kinyi kamar baki ganni ba. Shiru tayi, sam ta manta yana dakin, tayi zancen zucinta a fili, fatanta Allah yasa baiji taba. Tace kaji abinda nace ne? Yace a'a me kk ce? Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta maida hankali gurin abinda takeyi. Yace, ki fada min me kk ce mana? Sai naji kamar dai kin ambaci zainabu. Ta danyi dim, sannan tace, wai kai ka damu da wata zainabu, tunda ta kiraka jiya, ka fita hankalinka, harma takai ynxun kunnenka yanayi maka gizo ko? Magana mutane sukayi, sai ka zata sunce zainabu ko? Yace ni bance ba ranki ya dade. Ta zauna tana shafa hoda. Ta gama, taja durowar madubi, ta ciro abin daure gashin ta kamashi a tsakiya. Ta fesa turare sanna ta ciro daguwar rigarta leshi ta saka. Ba tare da ta daura dankwali ba ta nufi kicin. Shi dai yana binta da kallo. Tayi masa kyau a idanunsa. Ta dauko biredinta da ruwan shayi mara madara ta zauna, amma sai damuwa ta hanata cin biredin, sai ruwan shayin take kur6a. Yace nima zansha. Ta miqa masa na hannunta, kar6a. Yace, ki hadamin wani mana. Ta kalleshi, munin nawa har ya kai cikin kofin shayin ne, shiyasa ba zaka iya sha ba? Yace bance ba naga kamar baki qoshi bane, tunda ko biredin bakici ba. Ta daure fuska, nina qoshi. Yace shikenan bani. Ta miqa masa. Kan gado ta koma ta kwanta, fuskarta tana kallon gefe, tana tunanin nafita. Ya kalleta, baisan me take yiwa fushi ba. Sai ya samu kansa da shiga damuwa. [26/09 9:16 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 7⃣9⃣Yace ki tashi khadija, magana zamuyi, duk da naga yau kina fushi dani.Ta tashi amma taqi kallonsa, kanta yana qasa, tana wasa da yatsun hannunta, fuskarta a daure tam. Yace, to inason zan tare a gidana. Kina ganin ya kamata mu koma tare ne ko kuwa zaki zauna anan? Mimi tayi shiru cikin nazari, sai taga ya kamata ta gwadashi. Tace, kai me ka gani yafi? Ni ko ina daya ne a gurina. Ya dago yana kallonta cikin ido, sannan yace, banason in takura miki ne, kamar yadda nayi fa fada miki a tun baya. Abin da kikeso shi zan miki. Ta tura baki cikin jin haushi tace ni banida za6i. Ranshi ya sosu, cikin fushi ya miqe, shikenan, ni zan tafi. Duk lokacin da kk za6a, saiki fada min. Ni dai zan tare, kuma zanyi aure. Batasan lokacin da ta miqe tsaye a tsakiyar gadonba. Me kk fada? Yace nasan kinji. Tace ka auri dubu, amma kafin nan ka warware nawa auren dake kanka. Yace, nufina kenan don nasan bakida burin daya wuce wannan. Amma sai kina ta shirmenki.

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37