Chapter 15
Chapter 15
zata sauko haka cikin sauri ba. Hakanan ya fahimci cewa halinta ne yin abinda tace zatayi. A fili yace, wannan ya zama dole in cika mata dukkan alqawuran dana daukar mata. Wata zuciyar tace, harda saki? Gabansa ya fadi, amma sai ya miqe ya nufi dakin. Tana kakka6e gado, ya shigo ciki. Yace, ina zan zauna? Ta nuna masa bakin gado, bayan ta gama gyarawa, ka zauna anan. Ya zauna, yana kallonta tare da ci gaba da tuno da gatan ta har ta gama. Aikin dai babu sauri, amma tsaf-tsaf. Ta kalleshi, in nace zanyi wanka zan 6ata maka lokaci ko? Yace, yi wankanki. Ta dauki hijabi ta saka sannan ta fita. Ta dauki ruwan wankanta da Ummi ta zuba mata, sbd bata iya jan ruwa a rijiya, tsoron rijiya gareta. Bayan fitarta ne yaga wani littafi akan Allon gadonta. Ya dauka ya Kalli bangon, INDA RAI, DA RABO. Haka yaga an rubuta ajikin littafin, sunan littafin shine yaja hankalinsa zuwa ga bude shafukan littafin yana dubawa jefi-jefi har ta fito. Lura da tayi baya kallonta, sai ta shafa manta a cikin hijabin, da tazo saka kaya ne ta kalleshi, a tunaninta hankalinsa yana kan littafin ne, sai ta faki idonsa ta saka kayan. Murmushi yayi, a ransa yace, khadija ke nan, domin tunda ta fito hankalinsa yana gurinta. Bayan ta gama tazo ta zauna a daya gefen gadon. Ya dubi littafin, menene ma'anar inda rai, da rabo? Ta danyi murmushi, bansan yaya zance maka ba, sbd ka san bansan kan hausa sosai ba. Kawai dai naji su yaya suna sauraron littafin ne a rediyo, shine nace, a siyomin. "wa ya siyo maki? Tace ban sani ba yaya ce tasa aka siyo. Yace, kin karanta? Ta daga kai, alamun eh. Kin qaru da wani abu? Tace, sosai ma, duk da cewa labarin soyayya ne. Yace, shikenan zaki bani labarin wani lokaci. [21/09 3:17 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 4⃣5⃣Ya aje littafin ya fuskance ta sosai, "ki bani hankalinki muyi magana mai muhimmanci. Ta sunkuyar da kai, "ina sauraronka" bata iya kallonshi, don sai taga yayi mata wani qwarjini, ya cika dakin, "zan fara da son sanin matsalarki, in kina da wata matsala. "tana wasa da hannunta, tace, ni banida wata matsala, domin duk abinda akaci, shi za'a babi daidai qarfinsu, kuma zuwa ynxun na iya cin komai. Kuma ba'a takura min, komai nakeso nayi, zanyi ba wulaqanci. In babu zan haqura kamar yadda kowa ya haqura, shine kawai. Yace, na fahimta, to kina son siyan wani abu, ko burin yin wani abu, ina nufin na kudi? Ta saci kallonsa, banison komai na kudi, don duk abinda nakeso na kudi, bakada qarfin saimin. Don haka kar ka damu, khadija ba mimin daka sani bace, Nayi haquri da iyayena ma bare wani abin duniya. Babu komai a raina. Babu abinda yake birgeni cikin duniya ynxun. Yace, har nayi zaton zaki koma makaranta, don ki kammala digiri dinki? Tace, baka zaton in na fita iyayena su samu labarina. Yace, har ynxun baki huce da fushi dasu ba? Tace, na huce tun bayan da bakanan yaya Amina tayi ta karantomin kurakuraina ta hanyar nasiha, har na fahimci irin sa6awar da nayiwa iyayena. Ynxun kam ina nesanta kaina dasu ne, sbd ganina kusa dasu zaita sakasu cikin 6acin rai, zasu dinga tuno abinda nayi musu. Shiyasa bana fita. Banida wani buri daya wuce cikawa da imani inje in tarar da khalil. Gaban Ismail yayi matuqar faduwa, domin bai zaci jin haka daga bakinta ba. Baisan lokacin daya ce, dama har ynxun baki manta da khalil ba? Da sauri ta kalleshi, ta yaya kk zaton zan manta da wanda yake matuqar sona? Wanda ke fadamin kalamai masu sani cikin farin ciki, da nishadi. Wanda ke kwadaita min wata irin rayuwa, amma kafin mukai gareta, sai mutuwa ta katse hakan. Ya barni cikin qunci da takaici! Kuka ya kufce mata. 4⃣6⃣Shiru yayi tamkar ruwa ya cinyeshi, nazarin zantukanta yakeyi. ya dan qara matsowa kusa da ita, ya tausasa muryarsa qwarai. "Yi haquri khadija, inda zaki bani labarin soyayyarku da khalil, zanso ji. Ta dubeshi, fuska cike da hawaye, ba zan iya ba. Banason in tuna da komai game da labarin. Abinda kawai ba zan manta ba shine tsananin son da khalil yayi min. Haka kuma ba zan manta da yadda nayi ta wulaqantashi ba. Salon son da khalil yake nunamin ta hanyar chatting dina a facebook, wtsapp, da sauran irin wadannan kafofin, tun bana bashi amsa, har dadin kalamansa suka sa na soma bashi amsa, duk da ni ba amsa mai dadi nake bashi ba. Ranar dana soma son khalil, yawun bakina na watsa masa fa a cikin mutane. Amma kasan me yayi? Ismail yace, a'a tace,, ga mamakina sai naga kurum yasa harshensa ya lashe yawuna daya sauka kan kafadarsa, sannan yayi murmushi, "komai naki inason sa. In na bari yawunki ya sauka a qasa nan, nayi muguwar asara. Ta soma sabon kuka, wannan kadan ne daga irin son da khalil yayi min. Ismail yace, shikenan kiyi haquri. Allah ya yafe masa tace Ameen. Yayi shiru. Yasan ynxun yaya Amina ta rage mashi hanya da tayi wannan jihadin, na yiwa mimi nasiha harta fahimci cewa tayiwa iyayenta laifi, ba zai wahalar shawo kanta don zuwa basu haquri ba. Amman wannan ba ynxun ba. Ya dubeta, har ynxun tana share hawaye. Nace kiyi haquri. Kuma zaki iya samun wanda yafi khalil sonki, kema kuma ki soshi fiye da son da kk yiwa khalil din. Ya girgiza kai, Da wuya hakan ta kasance, nina kulle babin so, koda na samu mai sona, ni kam na tabbata ba zan soshi ba. Ismail yayi murmushin yaqe, to yaya batun islamiyya fa? Mimi tace ina daukan karatuna a gurin yaya Amina. yayi dariya, shikenan Allah ya biyata da aljannarsa. [21/09 7:46 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 4⃣7⃣Ya miqe ya dauko jakar tsarabarsu, ya dawo ya zauna bakin gado, "zo ki za6i abinda kk so cikin tsarabata. Ta matso. Ya dauko jakar ya dora ta saman Gadon. Ya soma ciro jallabiya, pink mai ratsin baqi, sai jarta, itama mai ratsin baqi, sai takalma da riga da wando kala biyu, duk ire-iren wadanda take sawa. Ta tsaya tana kallonshi, sbd ta san tsadar kayan. Kafin tace wani abu, sai kurum taga ya ciro wani gwangwani a can qarshen jakar, ya miqo mata. Da sauri ta kar6a sbd irin turarenta ne. Ta soma karanta rubutun jiki a fili tace, "tabbas shine" ta dago ta dubeshi, "siyan turarennan kayi? Yace eh, siya miki nayi. Tace ina ka samu kudi haka? Na ga kai din dalibi ne, kuma duk kayan nan suna da tsada, musamman wannan turaren? Yayi murmushi, "munyi aikin raba abinci ne ga mabuqata aka biyamu. Ta soma hawaye, ban ta6a tunanin zan qara amfani da wannan turaren ba. Nagode sosai. Ya tausasa murya don jin dadin sake burgeta. Karki damu khadija, nayi miki alqawarin in Allah ya buda min, zanyi miki gatan da yafi wanda kk ta6a shiga a fannin jin dadi. Ta sa idanunta cikin nasa, "nasan zaka iya, domin duk abinda kayimin alqawari, ka cika. Ina ganin kimar ka sosai, ynxun saura abu daya ya rage. Ya zaro mata manyan idanunsa, me? Tayi shiru, gabanta yana faduwa. Yace karki damu ki fadamin, qila
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37