Chapter 5
Chapter 5
ya sark'e mai wuya . Yafara k'ok'arin magana sunan YADIKKO ya kirawo wato Aisha amsawa tayi da na,am Malam yunk'urawa yayi . Kana yace dan Allah ki kula da LADIDI kinga y'a mace ce tunda Malam musa yafara magana YADIKKO ta fara hawaye . Tari ne yakuma sark'eshi YADIKKO ce ta umarci LADIDI ta kawowa mahaifin ta ruwa bayan ta kawo yasha . Yak'ara da cewa na bawa Malam Adamu LADIDI YADIKKO ce ta rushe da kuka ta aika LADIDI ta kirawo Malam Adamu ba,a jima ba se gashi sun dawo tare da gudu Malam Adamu ya k'araso ya rik'e hannun Malam musa jiki a sanyaye yace "sannu Malam . Amsawa yayi da yauwa ga amanar LADIDI nan nabaka jikin Malam Adamu yakuma yin sanyi sosai ya daure yace "insha Allah zakaji sauki . Murmushin yak'e Malam musa yayi daga nan ya kirawo LADIDI matsowa tayi kusa dashi ya kamo hannunta ya rik'e gam daganan yafara shak'uwa . Kulli nafsin za,ikatul mauti .. Allah yayiwa Malam musa rasuwa kowa ya jimama mutuwar Malam musa . YADIKKO inta kalli k'ofar Malam musa setaji hawaye ya zubo mata . LADIDI kuwa takoma kamar mutuniyar kirki bata fad'a bare neman tsokana duk wanda ya tsokaneta bata kulashi. Bayan anyi sadakar bakwai kowa ya watse YADIKKO ta kwanta rashin lafiya har asibiti Malam Adamu ya kaita amma an rasa gane ciwon dake damun YADIKKO . Kulum cikin ciwo take LADIDI kuwa tunda taga YADIKKO na ciwo shikenan ta karaya tana ganin kamar itama zatabi mahaifinta ne a kulum YADIKKO in suka zauna da LADIDI basayin wata magana kamar tadinga cemata ki rik'e mutuncinki a matsayinki na y'a mace, LADIDI na kuka tana jin YADIKKO. Ciwon YADIKKO ne yatashi sosai da gudu Ladidi ta tafi domin kiran Malam Adamu YADIKKO na d'agawa LADIDI hannu akan tadawo ina LADIDI ta kid'ime bata ankara ba tafice da gudu Malam Adamu tasamu a zaune shida inna Hauwa suna hira ganin ta cikin wanan yanayin yasa su mik'ewa a zabure LADIDI tana kuka tana cewa su Malam Adamu YADIKKO na zata mutu kuzo duk wanda yaga LADIDI a lokacin komi rashin imanin shi seya tausaya mata . Kafin inna Hauwa ta d'auko gyale ta fito har Malam Adamu ya isa gidan su LADIDI salati yahau yi ganin YADIKKO rai yayi halinsa . Inna Hauwa ce suka k'araso itada LADIDI Malam Adamu na ganin su ya juya fuska yana sharar kwallah . Tunda LADIDI taga haka itama ta zauna ta rafka uban ihu tareda birgima a k'asa babu wanda yayi yunk'urin hanata kukan mutane ne suka fara shigowa masu kuka nayi masu salati nayi masu adu,a nayi hak'ik'a mutuwar YADIKKO ta girgiza mutane sosai . Tsakaninsu da mijinta Malam musa wata d'aya bayan anyi sadakar uku inna Hauwa tasa LADIDI ta kwaso kayanta ta dawo gidanta da zama duniya tayiwa LADIDI kunci kwata,kwata batajin dad'in zaman duniyar. Bayan sadakar bakwai aka rufo gidan da kwad'o tunda LADIDI ta dawo gidan inna Hauwa takoma shiru shiru ko abinci takeso bata magana sedai in and'auko anbata. JOS tunda su Humaid da Jalal suka koma garinsu kowa ya koma bakin aikin shi Humaid aiki yakeyi a hospital d'in dadynshi daya bud'e mai , shikuma Jalal aiki yakeyi a ma,aikatar mahai finshi. Wato saida kayayyakin mata na sawa dana maza da sauransu sun maida hankali akan sana,ar sosai . Dady ne zaune a dining suna breakfast shida su momy da Humaid da Jalal kirane ya shigo wayar dady d'auka yayi kana ya kara a kunnenshi jinayi yace innalilahi yaushe ¿"dady ne ya ajiye wayar yana jimama rasuwar Malam musa da Aisha wato YADIKKO. Jalal ne yakalli dadyn nashi kana yace "badai iyayen LADIDI bane suka rasu¿ daday ne ya amsa da cewa dama sunada y'a LADIDI ne ? Jalal ne yace inadai kauyen da muka jene to tabbas iyayenta ne abokin Malam ne dadyne yace tabbas sune momy ce ta fara tambayar dady kwatance yayi mata inda zata gane adu,a sukayi musu daganan kowa ya wuce gurin aikin shi. ★ ★★ ★ ★ ★ Bayan shekara uku LADIDI tana da shekara 14 years tayi tsayi tayi k'iba farinta ya k'ara fitowa ga k'irjinta yafara cika tafiya takeyi tana waka ta hango me tallar k'uli,k'ulli tana zaune a gindin bishiyar kukar dake k'ofar gidan Malam Adamu da tazamo gurin zamanta tun ana hanata har anzo ana barinta. Me k'uli _k'uli ne ya kawowa Ladidi ,'d'agawa tahauyi tana cewa nawa nawa yaro me tallan k'uli yace "ashirin,ne Ladidi ce tace "za6omin d'auri d'aya kuma k'atoto mik'o mata yaron yayi kunce ledar tayi tanaci tana jefa k'afa yaro ne yagaji da zama yace ba bani kud'in kafin ya k'arasa Ladidi ta buge bakin yaron tace tunda har katambayeni wlh bazan bada kud'in ba kuka ya hauyi yaron tasowa tayi ta kama kunnenshi ta murd'a seda ya kwala k'ara ta sakeshi kana tace daga yau ka karayimin rashin kunya kagani.....✍🏽✍🏽✍🏽 *MOM ISLAM✍🏽✍🏽✍🏽.* *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 9_10 ______malam Adamu ne yakira dadyn su Humaid a waya akan cewar Ladidi zata dawo gurinshi saboda tasami ,ilimi sosai"beyi musuba yace ranar lahadi se su Humaid suzo su d'auketa malam adamu ne yace da muna shirin kawota gobe nida Hauwa dady ne yace to ai babu damuwa duk d'aya ne sekun so Allah yakawoku lpy daganan sukayi sallama". Inna hauwa ce ta ,tattaro wa Ladidi kayanta had'i da bata kud'in sabulu akan tayi wanki gobe zasu wuce birni aikuwa Ladidi jin haka ta fara murna tana tsalle ta kar6i kudin tafice siyo sabulu tana cikin tafiya ,ta had'u da k'awarta tana siyarda d'anwake gashi Ladidi najin yunwa k'awar ce tace Ladidi barin zuba miki d'an waken saboda tasan inta wuce Ladidi zata iya 6aro da robar d'an waken". Fara zubawa tayi Ladidi tace ke barshi haka yarinya gobe zamu tafi birni mushi kayan d'ad'i kawar Ladidi ce ,tace nima inason zuwa birni sedai bamuda y'an uwa a birni . Bayan ta siyo sabulun tafara wanki seda tagama duka sannan ta zauna tana jira su bushe ta ninke ". Washe gari bayan sunyi sallahr asbh malam adamu yashigo yace su shirya da wuri saboda wuyar mota. K'arfe goma suka tafi tasha sunyi sa,a wata mota bata cikaba suka shige malam adamu yabiya kud'in motar suka d'auki hanya zuwa jos". Tunda suka shiga mota Ladidi ta hango wani k'aton arne yana cin Apple lek'enshi takeyi tana lashe baki had'a ido sukayi ta sunkuyar da kai a karo na biyu takuma d'ago kai tayi sa,a shima yad'go suka had'a ido ita kuma Ladidi ganin yanata kallon ta mugud'a mai baki shikuwa yana ganin haka ya bige bakin inna Hauwa ce ta ce kaikuma metayi maka dazaka bigi yar marainiyar Allah . Da hausar da bata game bakinshi ba yace wanna yariya batada hakali Ladidi ce ta ,tuntsire da ,dariya shikuwa yaji haushin wanan dariya ana zuwa gurin sojoji ya bawa Ladidi 6awon gyad'a yace tazubar mai Ladidi bata ta6a shiga motar da zatayi tafiya me nisaba aikuwa ta watsa 6awon gyd'ar kusada wani k'aton soja suna ganin haka suka tare motar su Ladidi suka ce kowa ya fito
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32