Chapter 23
Chapter 23
ce *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 43_44 _____D'akin momy ta nufa ,momy na ganinta ta rangad'a gud'a mutane sai kallonta sukeyi wasu na gulma wasuna cewa tabasu sha'awa ,momy ce tajata gefe tace ”please daughter karkiyiwa mijinki rashin kunya kinga can jama'a suna kallonku dan Allah badan niba ,sunkuyar da kai Khadija tayi tace ”momy wallahi bazan yimai rashin kunyaba ,cikin jin dad'i momy ta mik'o mata dubu biyar sabbi tace ”tayi manni ,godiya tayiwa momy ,suna cikin magana saiga Humaid nan yashigo cikin shadda mai ruwan coffee shimafa ba k'aramin kyau yayi ba kai kace shine angon ,durk'usawa yayi har k'asa ya gaida momy ,bayan ta 'amasa ne yashiga ya gaida jama 'ar dasuka taru ,daganan yafito ,ya yiwa Khadija magana ,cikin yanga tace ”inzo mutafi ? wani kalo yake yimata mai kamada na so hhh masoya kenan 😘,momy ko ganin hakan yasata shigewa ciki ,Humaid cikin wani salo maijan hankali yace”muje lokaci na tafiya ,ohk tace ”daganan suka wuce ,gidan gaba ya bud'e mata ,shigewa tayi shima yashiga hmm riders duk wanan ladabin da khady take yiwa humaid duk a cikin umarnin momy ne hhh🤣 driving yafarayi cikin k'warewa rik'o hannunta yayi da d'ayan hannunshi d'ayan kuma yana driving dashi ,ko k'ala batace ba .... Da isarsu yayi parking gurinda kowa ya parka motarshi ,fitowa yayi yana jiran Khadija tafito ,hhh abinku da gimbiyar mata saida ta jima yana tsaye sanan tafito ,a yangace take tafiya ,Humaid ne ya hango wasu samari suna k'arewa shigar Khadija kallo, cikin zafin nama ya rik'o mata hannu suka wuce ,da shigarsu Hall din kalo yakoma gunsu ,sai tafi ake yimusu ,kusada ,amarya Khadija ta zauna shikuma Humaid friends d'insu nacemai ga guri yana cemusu shifa kusada gimbiyar zai zauna ,dole aka mik'o wata ha d'ad'iyar chair ya zauna ,kammo hannunta yayi yana mata rad'a 'a kunne ,nimafa banji meyace ba nadaiga suna dariya ,duk abinda sukeyi doctor Umar yana yimusu photo ... Kiran Amarya akayi dakuma k'awayenta ,mik'ewa amaryar tayi Jalal kuwa yana rik'e da 'amarya dan haka suka mik'e a tare yana cemata wananfa matar yayana ce ,cikin fara'a 'amaryar ta rik'o hannun Khadija tace" kitaso muyi rawa dayake Saudat tasan rigimar Humaid ko kallonshi batayi ba 'amma tana jan hannun Khadija ,saboda daga ganinta saudat taji tashiga ranta sosai da sosai ,humaid kuma damk'e hannun Khadija yayi wai adole bazatayi rawa ba ,fakar idonshi Khadija tayi ta mik'e aka fara cashe rawa ,ganin bai hangota ba yasashi tashi yana lek'e ,hangota yayi kusada mai d'aukar photo ,zuwa yayi ya janyota yana mata kallon soo💖 ammafa 'akwai kishi over, ahaka dai akayi abubuwa kamarsu yanka cake dakuma bada tarihin amarya da sauransu ,ana shirin tashi ne aka sake kid'a mata da maza suna rawa ,Humaid na waya Khadija ta mik'e taje tafara rawa ,cikin zafin nama ya figota yana cewa kinada hankali kuwa ?ko kulashi batayi ba ya rik'e mata hannu suka fice..... Direct wani katafaren hotel sukaje kayan dad'i yasa 'aka kawo musu ,sunci sun k'oshi daganan ya wuce gurin mai saida kaza tofa🤦♀️, Guda biyu yasiya saboda yasan mutuniyar akwai son cin dad'i ,daganan ya wuce da ita wani katafaren shago kayane na Makkah su dogayen riguna da etc.. cemata yayi kiza6i wanda ranki yakeso cikin zumid'i ta hango wata riga da tun tana budurwa take burin sata 'amma saboda tsananin tsadar 'rigar yasata hak'ura ,yaukam zata gwada d'auka ko zai siya mata ,nuna rigar tayi tace ”nidai wanan rigar nakeso ,Humaid ne yace ”to ita kad'ai ta isheki ?eh tace ” saboda tana tunanin inyaji kud'in rigar cewa zeyi ya fasa ,mik'a rigar yayi ,mai lissafin kud'in kayanne yace”50k take ,cikin ko d'ar yace ”ok yabada ATM aka cire suka wuce,mamaki ne yacikata ,amma babu bakin mgna tayi shiru ,hanyar gidanshi ya nufa da ita ,zaro ido tayi tana kallon ikon Allah ,momy ce take kiranshi a waya ,ganin kiran yasashi cewa osh momyyy ,d'auka yayi ,yace ”momy mundawo fa momy bata yardaba tace ”to yanzu kuna ina? Munje kasuwa yace”a tak'aice hmm momy tace ”to maza _maza kudawo gida ,farinciki ne ya lulu6e khadija ta fara murkishi tana cewa hhh kaza zanciki ina komawa gida ,shiko humaid haushine ya cikashi ganin yaufa momy ta takura masa ,yanzu yasiyo kajin a bati kenan ya tambayi kanshi ,juya kan motar yayi zuwa unguwar su momy .... Suna isa yayi Horn mai gadi ya bud'e mai ya shige da motar ,khadija ce ta juya ta hango ledar kazar a back side ,saida tafara bud'e k'ofa tukun ta janyo ledar ta ,arce da gudu tana dariya ,wata muguwar yaunwa humaid yakeji gashi Khadija ta d'auke kajin ,kaii yace yana mai d'ora kanshi a booth d'in motar , Cikin sanyin jiki ya shige parlor yana mai sallama wucewa part d'inshi yayi ya kwanta idanunshi a rufe amma ba baccin yakeyi ba,yanason su zauna da khadija yaji ko tana sonsa kokuma zata sauya ra'ayi ,amma yana tsoron yimata magana ta taso da 'abinda yariga ya wuce , bacci ne ya d'aukeshi yana cikin tunanin khadija ,wani mumunan mafarki yayi wai ga khadija nan wani mutumi ya rik'e mata hannu sunata gudu, a tsorace ya farka yana salati ,çikin azama yayi part d'in khadija ,samunta yayi tayi bacci akan sallahya gakuma plet d'inda taci kaza ga ragowar kazar a gefe,zama yayi shima ya cika cikinshi sosai sanan yashiga toilet d'inta yayi alwalah yazo ya tada sallah ,yana idarwa ya kwnta ta bayanta ,khadija jin mutum a kusada ita yasata kurma uban ihu tana salati ,lokacin dare yayi sosai dan 11pm na dare ,dady ne yafito shida momy cikin razana ,kai tsaye d'akin khadijan suka nufa ,humaid najin alamun zasu shigo ya shige toilet yana rawar jiki ,ganin harta koma bacci yasasu komawa bayan momy tayi mata 'adu'a ta fice ..... humaid ganin khadija zata iya tona masa 'asiri yasashi komawa d'akinshi babu shiri ... Dady ne yata humaid da khadija akan maganar komawarta hhh jiyafa humaid kwana yayi yana sallah akan Allah yasa khadija ta yarda ,dady ne yace ”to gareki khadija zaki koma gidan humaid 'd'inne kokuwa ,dogon 'nazari tayi akan hallacin da su momy sukayi mata ko d'an cikinsu albarka gaskiya koda batason humaid bazata iya duban idanunsu tace ”bazata komaba ,sunkuyar da kai k'asa tayi tace ”na 'amince wow kuzofa kuga rawar jiki ko kunyar dady baiyi ba ,ba humaid ba har dady 'yaji dad'i sosai ,albarka yadinga samusu dakuma fatan alkairi da zuri'a d'aiyyiba ,momy ce tafito itama tana tsaye tanajin duk abinda 'ake cewa ba k'aramin murna tayi ba..... Washe gari wani gyara momy tafara yiwa khadija su dilka ne su tsumi ne dasu garin sha magani dai kala_kala gasu humra da ta jiki data kaya gakuma kayayyakin d'aki da dady 'yasa 'akawo daga kamfani a fitar da na gidan......✍️. Kwanaki k'alilan khadija ta sauya tayi kyau sosai ,humaid kuwa jira yakeyi ace yatafi da ita 'amma shiru ,hhh yadai fara shawarar ya gudu da ita , saida 'kayi one month da magar sanan momy ta amince yake zuwa gurin khadija washe gari kuwa dady 'yace ”ya tattara matarshi su wuce ,aikuwa kamar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32