Skip to content

Chapter 21

Chapter 21

Ladidin Kauye Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

bai 'isheta ba tacigaba da kwasar kayanta ,tana gamawa tace ”saura takadda ta ,humaid da yad'auki lamarin k'arami saiyaga 'abin ya zarce gona da iri ,yana rok'arta itako tana tafiya ,ficewa tayi daga gidan da k'atoton akwati tayi bakin titi ,napep ta tara ya kaita har k'ofar gidansu , tana sauka ta mik'a mai kud'inshi tayi nocking mai gadi ya bud'e mata da sauri ta shige cikin gidan ,samun momynta tayi a parlor tana kallo a tashar MBC 2 ,kwanciya tayi tafara rera kuka ,momyn ce tace ”kiyimin bayani mana maiyafaru daga biki yau kwananki biyar amma kice kin taho da k'aton akwati ?"ko wata matsalar ce kinfi k'arfin ki kiarani a waya? Momy tadinga jero mata tambayoyi a jere, Khairat ce ta dubi momy tana hawaye tace ”momy ki fahimceni please karkiyimin mumunanr fahimta ,momy ce tace” tashi mu shiga ciki kinsan gidan baya rabo da mutane, rufawa momy baya tayi tare da 'akwatinta ,suna shiga momy tace ”ina jinki daughter ya 'akayi wani sabon kukan tafara tace ”momy wallahi mutuminnan bashida lafiya , momy bazan iya zama dashiba wallahi ,momy da bata fuskanci 'inda y'ar tata _ta dosa ba yasata cewa rashin lpy kuma ?eh Khairat tace”daganan ta bata labarin hirar dasu humaid sukayi a hospital dakuma 'yanayin zamansu .... Momy cikin jinjina, lamarin tace ”gaskiya zama bazaiyyi ba za'a cuci d'aya dama yasan bashida lafiya ya auro ki tabb, amma bari yau dadynki yana hanya sai muyi maganar aji inda lamarin zai kaya, to tace” daganan ta kwanta momy kuma tayi waje.. Gidan su Humaid momy ce tacewa”dady anya baka zargin wanan yaron Ammar shine ya sace Khadija?",dady shiru yayi nad'an wani lokaci cankuma yace ”eh to gaskiya ban zargesa ba kasancewar baya gari ,kinsan iyayensa ba Nigeria suke ba ,amma zansa 'a bincika min ko da wata mak'ark'ashiyar ,momy ce tashare wasu zafafan hawayen dasuka kwaranyo mata ,dady cikin tausayawa yace ”dole sai hak'uri uhm 'momy tace ”Jalal ne yashigo cikin sallama , bayan su momy sun amsa ne Jalal yace ”dady kunji abinda yafaru ?" Momy ce ta dubi Jalal tace ”menene yafaru ”gyara zama Jalal yayi yace ”momy wlh matar yaya Humaid ce tace ”wai saidai ya saketa ,cikin ko inkula dady 'yace ”to saime ni banga dalilin da kowa zai tada hankali ba ,inace aurene ?to tinda yariga yayi shikenan yaje yaci aure ,momy uffan batace ba, ta mik'e tayi cikin bedroom d'inta.... *AFTER 1 MONTH* Kwance yake a parlour ,kallo ya kunna 'amma hankalinshi baya gurin ,tunani ne suka taru sukayimai yawa yarasa tudun dafawa ,jin nocking yasashi mik'ewa ,handle d'in k'ofar ya murd'a ganin Khairat yasashi mamaki ,cikin fushi tace ”karkayi zaton ko nazo ne ,dama nazo in gayamaka ciki ne dani kuma kuma three3 weeks kenan ,hamdala Humaid yayi yace ”kinga munada rabon samun baby's ko ,murmishin da baikai zuci tayi ,tace ”a cikin wa? cemaka 'akayi zanyi shayarwa tabb, to kasani aihuwar ma bazanyi ba dan yaron daba 'a gidan ubanshi nake ba mezan haifa? Humaid jiyayi damuwar tashi takuma nunkuwa over ,cewa yayi please khairat ki fahimceni mana ,nifa bani na koreki ba cox kekika tafi da kanki bansan lefin danayimiki ba, bud'e baki tayi tace ”au bakamasan lefin dakayimin ba to bari 'in tuna maka koka manta dakaida mace banbancin ku kad'anne?." Dafa kai Humaid yayi yace ”kibar ganin ina lalla6aki wallahi zanyi miki dukan tsiya kuma inga mai tsaya miki, kallon up and down tayimai kana tace” turr tayi gaba ,tana fita Humaid yamaida k'ofa ya rufe yafara kuka kamar k'aramin yaro ,yana tambayar kanshi wai shi meyayine a rayuwa bashida sa'a yanzu yayi aure dan yaji dad'i amma sai tozarci dayaketa biyo baya ,ga wanan shegiyar yarinyar tayi sanadiyar had'ashi da iyayenshi ,wayoo Allah na yafad'a cikin k'unar'rai dazanga Khadija saina kusa kasheta ,domin ita masiface..... Momy ce zane rik'e da carbi tana lazimi jin sallama yasata d'ago kai ,ganin Khadija ce take shirin shigowa parlor yasa wani matsanancin kuka ya ku6cewa momy ,tana cewa daughter ashe zanganki ? three months kenan bakya gida ,itama Khadijan wani kukane ya su6uce mata tana momy kiyi hak'uri nasan nayimuku lefi ,amma kafin in zauna kuyafemin ,ta had'a hannuwanta biyu ,tana rok'arsu momy ,rungumeta momy tayi tace ”bakiyi mana komai ba daughter amma kinsamu fargaba ,rik'o hannunta momy tayi tace ”zonan kije kiyi wanka sai kizo kici abinci ,babu musu tabi momy ,bayan momy ta rakata d'akinta nada kafin tayi aure ta fice , wanka tashiga tayi alwalah ta tada sallah tana idarwa ta zauna gaban dressing mirror tafara tsara kwaliya ,wata doguwar 'riga tagani bak'a mai adon stone ajiki dakuma flawoyi masu kyau ,farinciki ne ya lulu6eta tafara magana cikin zuciyar ta tanacewa 'anya nayiwa momy hallacci dahar natafi nabarta ? gashi duk da haka bata ganin lefina kuma bata fifita y'ay'anta 'a kaina ,share guntun hawayen daya kwaranyo mata tayi tasa rigar dakuma bra da pants tasanya rigar ,rolling d'in d'ankwalinta tayi tafito ,ganin bataga momy a parlor ba yasata wucewa bedroom d'inta ,canma batanan ,k'ara fitowa tayi ta zuwa kitchen.... Rungume momy tayi ta baya tace”momy da kanki kike girkin ?"ina ummi fa ?momy ce tace ”ah ai yau dole nayi miki girki daughter na guda tadawo ,daganan suka shiga hirar duniya ,amma momy batace ina taje ba , itama bata ce komai ba ,bayan sungama girkin 'ne suka wuce dining ,cikin so da k'auna suke cin abinci momy nata janta da hira,Jalal ne yayi sallama 'amsawa sukayi da Khadija da momy Jalal jin muryar Khadija yace ”tabb yaushe a gari ?kodai Makkah kikaje ne ?bud'e baki Khadija tayi tana dariya tace ”yaya Jalal nasiyoma kalo kalo ,bashiba har momy saida tayi dariya ,zama yayi shima yace ”to momy ina 'abinci na ?Khadija ce tace”kaga zomuci anan inbamu k'oshi ba ma k'aro ,zaro ido Jalal yayi yace ”tabb kinaso yaya Humaid yazo ya ganni 'inacin abinci da matarsa kenan ko ?"d'aure fuska tayi tace"barin zuboma naka to ,momy na kallon yanayinta 'amma bata nuna mataba ,tana fita Jalal yace ”ina tajene wai” cikin rad'a ,momy ce tace”wlhi bata gayamin ba nikuma ban tambayeta ba...... Tana dawowa rik'e da plet na 'abinci Jalal yace ”to sannu a yawo ,dariya tasa tace” yaya nifa ba yawo naje ba ,to ina kikaje inji Jalal ?to garinmu naje ,momy ce ta 'ajiye cokalinta ta tsaya kallon Khadija wacce magana takeyi ko a jikinta kuma babu alamun damuwa 'a fuskarta ,wallahi yaya Jalal ina gidanmu ganin babu wanda yake shiga gidan ,yasani yin saukar dare na bud'e gidan na zauna 'aciki kuma ko inna da malam Adamu basusan inanan ba dan babu Wanda na gayawa.....✍️✍️✍️. Mom Islam ce🤙 *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 41_42 _____Shiyasa ba'asan inanan ba ,kuma koda na koma banida matsalar abinci kasancewar komai na d'iba ,momy sai lokacin tayi magana tace ”to me ya had'aku da Humaid?? "nisawa tayi tace ”tunda mukaje India yake wulak'antani nikuma yasa na gudo kawai nakoma can gidan ,kuka momy tasa tana cewa dama,cin mutunci da tozarcin da Humaid zaiyi mana kenan hamm ya kyauta , Jalal ne yace ”to momy ai tunda tadawo farinciki zamuyi

Table of Contents

Chapters

32 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32