Skip to content

Chapter 27

Chapter 27

Ladidin Kauye Book 1 Complete Hausa Novel 1,188 words 0 views Progress saved
Download Book

aka kwantar da Khadija samunta tayi ido a kakkafe tana kuka momy tsabar firgici tayi gurin doctor tana kuka ,da sauri doctor Umar ya shigo yafara gawaje gwaje ,cikin sa'a nunfashin ta ya dawo normal can tafara bud'e ido ruk'o hanunta momy tayi tace ”alhamdulilh daughter Allah yakara miki lafiya ,Khadija babu bakin magana sai kalle kalle takeyi.. Tabarmai nagani da mutane a k'ofar gidansu dady kowa kaganin fuskarsa bbu dad'i zaman makoki akeyi dakuma adu'oi , dady ne keta kar6ar gaisuwa gurin jama'a suna yimasa ya karin hakuri ,washe gari jikin Khadija yayi kyau sosai dan har tana cin abinci sosai ,sallama aka basu suka wuce gida ,Khadija na ganin yan zaman makoki tafara tambayar waye ya rasu ,momy ce ta tuno da sharud'an da doctor ya gaya mata akan ta kiyayen 6acin ranta kokuma shiga damuwa ko gani ko jin fargaba ,momy ce tace ”suna hutawa ne kinsan wanan watan dolle sai anyi meeting da ma'ai kata ta gamsu da baya nin momy shiyasa ma bata k'ara d'aga hankalinta ba.... Kai nimafa mom Islam abin ya d'auremin kai 😢meya faru a gidansu Khadija ??waye ya rasu ??? tabb todai kubiyoni danjin inda muka dosa👏. Kwance take tana wani matsanancin kuka rabonta da abincin kirki tun da wanan abin ya faru ,tarasa ina zatasa kanta gashi Allah ya jarabeta da abubuwa duka biyu ,alwalah ta d'auro tazo tafara nafilfili tana gayawa Allah damuwarta ,washe gari yaune akayi sadakar uku mutane sun ragu sosai ba kamar daba ." Kale ² takeyi a d'akin tarasa meyafaru bazata iya tunowa ba ihu tafarayi dan razana take koda wane lokaci ,momy da tatashi akan darduma tayo d'akin da gudu ta sami Khadija nata juya kai tana ihu ,wasu zafafan hawayene suka zubowa momy tayi waje da sauri ,driver ta k'walawa kira cikin azama yazo ya drk'usa a gaban momy _momy ce tace ”maza ka fito da mota mu koma hospital ,komawa tayi ta ruk'o Khadija tafito da ita hijab d'inta ta Sanya mata daganan sukayi mota ,dak'ayar momy ta sata a mota suka wuce hospital, sunyi sa'ar ganin doctor ,inda yake sanar musu cewar su dage da adu'a kuma akwai abinda take tunawa yake tsorata ta magunguna ya kuma basu yace ”ku kulla sosai da ganin tasha magani." Haka driver ya dawo dasu gida ,matane keta shigowa gidan momy suna yimata ya karin hakuri ,wanan su shigo wanan su fita dayake momyn ta mutane ce . *KAUYE* Sahura ce ta shigo gidan inna da gudu tana shewa ,had'e fuska inna tayi tace ”fitarmin a gida nace kifice ko ,dariya Sahura tasa tace ” inna ya alelen ranan waya biya kud'in ¿"ubanki ne ya biya kinji ,sahura ce ta zaro ido tace ” ubana fa sirikinki ne ,inna ce ta d'auko sanda tana shirin buga mata wani yaro yai sallama yace ” Aslamu alaikum zakusi kai da kafar kaza ?" tsalle Sahura ta doka tace ”kai yaro kawo nan shigowa yaron yayi ya nemi guri ya zauna ,Sahura ce ta dubi inna tace ” hmm sai na tuna lokacin da mukaje gidansu Ladidi kullum sai naci kaza ,amma yauma Allah yasa inada ragowar kud'in da Humaidu ya bani d'ari biyu na siya ,dajin haka inna ta washe hak'ora tana dariya tace ”yoo ai siyama zakiyi koda na d'ari ne Sahura ce ta tambayi yaron nawa nawa ashirin ashirin yaron yace ”kasiyar uku hamsin ¿"eh kawo . Kai ta d'iba guda biyu k'afa kuma d'aya duban inna tayi data zuba tagumi tace ”toke bazaki d'auka bane ?inna ce tace ”to masu abin basuce in d'auka ba ni na isa ,dariya Sahura tasa tace ”laaa ina ki d'auki na hamsin ,inna na sid'ar hannu ta d'auka harda zubo romo ,yaron yana zaune har suka gama ci Sahura tace ”ga hamsin d'inka kajira wanan tsohuwar ta baka kud'inta inna na sud'e hannu tace ”kan uban ke kin biya naki hakafa kikayimin ranar sai malam ne ya biya yana fad'a Sahura dake taunar k'ashi tace ” maganin mai kwad'ayi komai mutum saiyyaci ,inna ce ta kunto zaninta gudar d'ari biyar ce a jiki mik'a wa mai kai da k'afa tayi tace ”k'aromin na hamsin ,dan ubanta ni zata rainawa hankali*LADIDIN KAUYE* funny & love story 51_52 Yaro dai na ganin ikon Allah ya je ya samo canji ya kawowa Inna ,Sahura ce tace ”au kewai inna kina gadarar zaki bani haushi ne aikin 6urr saidai inbaki haushi ta ja gyalena ta d'aura a kwankwaso ta fizge kwanon da inna tasa a dad'o mata naman ta ruga da gudu ,kuka inna tasa tana tsinewa Sahura tana cewa ,shegiya ga kashe d'ari danayi tashi d'aya gashi iya romo na tsaya sud'a ta wafce kwanon ,shidai mai talla gaba yai yabar inna tanata surutunta." _JOS_ da sallama ya shigo yana cewa momy yau akayi sadakar bkwai to Allah ya gafarta masa kuka momy takeyi sbda inta tuno abinda yafaru amma aikin gama ya gama rayuwar batajin dad'in yinta sbda Khadija har yanzu sai sauk'in Allah yanzu ciwon 'nata ya koma kamar na mai aljanu in ciwon ya tashi to guduwa take burin yi dady abubuwa sunyi mai ywwa sosai duka dai familyn gidan basuda wal wala ,kwance take tana bacci sai kuka takeyi kuma da k'arfi ,momy ce ta shigo d'akin ta sameta tana bacci kuma tana kuka ,adu'oi tashiga yimata tana tofa mata ,yunk'urowa tayi tana gurnani zata hankad'e momy ,cin sallamar Jalal yasa momy k'wala masa kira ,da sauri ya shigo yana cewa momy lafiya kuwa ¿inafa lafiya Jalal ?narasa yaza’ayi da ciwon Khadija kullum abin baya lafawa kullum cikin fad'a muke gashi banda kunu batacin komai y'an aikin gidan suntafi garinsu ,sai kuma tasa wani kuka mai ban tausayi ,hak'ik'a momy mace ce wace batada zalunci batada mugunta kuma bata fifita wani akan wani ,Jalal shima abin yafara damunshi kukan da momy keyi ya kuma tayarmai da hankali ,sukan sunga jarabawa Allah yasa su cinyeta duka." Washe gari antashi da wani sanyi mai shiga mai shiga jiki tunda gari ya waye khadija keta ihu tana k'ok'arin fitowa wani girgiza d'akin yakeyi ga wasu k'ara dake baiyyana a cikin d'akin ihu takeyi iya k'arfinta ,dady daya shigo yanzu yai d'akin da sauri ,ganin inda jikin khadija keta 6ari yana makyar kyata yasashi cire hular kanshi adu'oi yaketa karanto mata amma sauki sai lokacin da Allah ya nufa ,gefenta wasu abubuwa take gani masu ban tsoro sai nuni take yiwa dady ina shikam bai gani ba ,ihu take kuma yi tana ruk'o hannunshi amma dady babu abinda yagani yarasa wane ciwo ne ke damun khadija , adu oin da yai mata yasamu jikin ya lafa dan har bacci ya d'auketa." D'akin momy ya nufa zaune ya sameta kan sallahya tana azkar shigowar sa ne yasata shafa adu'a tace ” barka da dawowa mijin kirki ,dady ne ya fitar da wata zazzafar iska daga bakinshi ya d'aga hannu sama yana cewa Allah mun gode da jarabawar da kayi mana Allah ka kawo mana mafita ba yawan arzik'inmu ba bakuma yawan ibadunmu ba Allah ka dubemu ,suka shafa tare da cewa amen. Wata girgiza sukaji mai firgitarwa momy zata tashi dan taga meke faruwa dady ya tsayar da ita yana cewa kibari in lek'a ,momy na shirin kuka tace ”gaskiya sai dai

Table of Contents

Chapters

32 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32