Skip to content

Chapter 19

Chapter 19

Ladidin Kauye Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

sukayi dady 'yabawa malam Adamu dubu hamsin sukayi gaba,godiya su inna suka dinga jerowa suka yimusu rakiya,har zuwa gurinda sukayi parking d'in motarsu. Dady 'yana tuk'i yana tunani anya ba wani abin Humaid yayiwa Khadija ba dan sunsan halinta batada son zuciya ,momy ma 'a tata zuciyar tunani takeyi kodai Humaid ya cusa mata wani mugun abunne yasata guduwa ,har suka bar garin babu maiyiwa wani magana,da isarsu jos suka wuce gidan TV da gidan redio domin bada sanarwa ko 6ata tayi ...✍️✍️✍️. Mom Islam ce *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 35_36 _____Daganan sukayi gida jiki babu k'wari kowa ya sauka 6atan Khadija yazame musu tamakar mutuwa tayi ,dady ne yakira Humaid a waya yake cemai maza _maza yazo yanason ganinshi ,gaban Humaid na fad'uwa ya shigo gidan bayan yayi parking d'in motarshi ne ya shiga parlor ganin babu kowa yasashi wucewa d'akin dady ,samun dady 'yayi a kishingid'e kamar mai bacci, da sallama ya shiga yanemi guri ya zauna zaice ina wuni dady, _dady 'yace”bana buk'atar gaisuwar ka saboda yanzu batada 'amfani kuma wallahi kaje ka nemomin Khadija duk inda tashiga kokuwa kayi danasani a rayuwarka ,gumi ne yafar a keto mai tako ina yace”dady nimafa wallahi...wani azabbaben mari dayaji saida ya mik'e yana shirin bigewa da bango ,ficewa yayi daga gidan yana gunguni ,shima Humaid d'in gidan TV da gidan redio ya nufa yabada cigiya daganan yakoma gida yana 'adu'oi akan Allah ya baiyyana ta yafita daga masifar da iyayenshi suka kirari ,yaukam hankalinshi ya tashi sosai ganin fushin dady ba k'aramin tsorata yayi ba . Washe gari ko gigin zuwa gidansu baiyi ba kasancewar bayason jin kalmomin da zasu hargitsamai k'wak'walwa , gashi yau saura sati d'aya ciwon jikinshi ta warke ,kuma yanada burin yin aure domin 6arje sabon shafi ,amma baisan wazai tunkara da maganar ba tunda wanan muguwar ta gudu ai ta jazamai fitina ,kwata_kwata bashida kwanciyar hankali kamar shine marar gata 'a duniya 'amma yasan mafita k'auye ya nufa gidansu malam Adamu yana shiga yasamesu suna ,zaune shida inna bayan ya gaishesu ne yake yimusu jajen 6atan Khadija ,malam Adamu ne yace”yau kimanin sati uku kenan Allah yasa tana raye ,amen yace ”can kuma yace”dan Allah baba inaneman wata 'alfarma ne ,babane ya maida hankalinsa ga Humaid yace” inajinka yaron kirki maiya faru ?"sunkuyar da kai Humaid yayi yace” baba sonakeyi nayi aure kafin Allah ya baiyyana Khadija muci gaba dayi mata 'adu'a." Jinjina kai malam Adamu yayi saboda lamarin babu dad'i wato shi ta 'aure ma yakeyi ,cankuma yace” karka damu yarona yaushe iyayen ita yarinyar sukace ka turo ?"cikin rawar jiki Humaid yace” ranar juma'a ne ,malam Adamu ne yayi lissafi yace” saura kwana hud'u kenan to insha Allah zanzo kuma kafin inzo zankira mahaifinnaka muyi magana ta waya ,inna ko sai jinjina kai takeyi tana tuno Khadija, godiya Humaid yayi tsabar farinciki bandir d'in y'an dubu ya 'ajiye masa yana komawa mota ,yakira budurwar tashi saida sukayi hira sosai sanan sukayi sallama , ya mik'i hanya tafiya yakeyi cikin farinciki da nishad'i saboda yakusa zama 'ango hhhh... Tunda yakoma gida ya kirawo masu decorection d'in gida gyra 'aka yiwa gidan kasancewar yarinyar y'ar manya ce shiyasa yakeson shima 'asan d'an manya ne ,part d'inta na can gefe gaban d'akin Khadija kayan Khadija kuma 'yadawo dasu k'asa 'amarya takoma sama ,kwana uku da magana ,dama Humaid ko k'ok'arin dosar gidan baiyi ba ,momy dajin zancen auran Humaid batace uffan ba haka shima dady 'yace” babu hannunshi ,malam adamu ne sukaje gidan surukan shida Humaid shikuma Humaid ya wuce gurin budurwar sa mai suna khairat ,hira sukeyi cikin so da k'auna dama irinta ya dad'e yana nema wato mai budadd'en ido ,ruk'omai hannu tayi tace”zomuje zagayeshi tadingayi da girma dakuma shuke shuken gidan suna rik'e da hannun juna.... Malam Adamu na fitowa ya koma can gidansu dady baisami dady a d'akinshiba yasa ya danna number Humaid, yana d'agawa malam Adamu yace” to kazo anyanke magana ,cikin azama Humaid yabaro gidan yayo gidan su ,samun malam Adamu dayayi shi kad'ai yaji dad'i sosai ,malam adamu ne yace” sun yake dukiyar aure nabada cikin kud'in da kabani d'azu to ansa biki sati uku masu zuwa ,godiya Humaid yaketa yimai daganan malam Adamu yace” zai koma, wasu mahaukatan kud'i Humaid ya d'ibo yabawa baba ragewa yayi kana yace” Allah yasa 'albarka saganan sukafice ,Humaid da sauri yafice daga gidan kamar marar gaskiya hmm.. Da kanshi yaje ya had'o kayan akwati daganan ya zarce gidan mahaifiyar momy yabata labarin abinda yafaru da Khadija amma yad'an had'a da k'arya ,su hajiya lefinsu dady suka dinga gani kuma sukace insha Allah zasu tsayamai kan maganar auran ,godiya yayi musu yabar kayan a gidan yadawo gidanshi ... Yau saura sati biyu biki shirye²akeyi ta kowane 6angare amarya kuwa gyara takesha kamar ba gobe ,batun soyayya kuma sai abinda yayi gaba dan babu baya, ana biki saura 1 week ne dangin momy suka kai kayan akwati ,da shigarsu dangin maman khairat suka hau gulma suna cewa ji wanan banzan akwatin kamar na y'ar talaka ko besan wa ya 'aura bane?,sudai dangin momy haka suka kai kaya suka dawo jiki a sanyaye, dady ne yakira Humaid a waya yake cemai duk wasu takkaddu dayasani na hospital d'inshi to ya tarkato ya kawomai dan haka shima tuna 'aure zaiyi yafara neman 'nakanshi tashin hankali gamida rikicewa Humaid yashiga ko 6atan Khadija baisashi shiga damuwa irinta yauba ,hak'uri yake bawa dady amma ina dady 'yace” aina rantse ,daganan dady 'ya katse wayar .... Yau saura kwana biyu d'aurin aure Humaid yayi d'inkuna sunkai kalla goma saboda murnar khairat ,a yaune dady 'yabada saukar alkur'ani mai girma masallatai akan 6atan Khadija , Humaid ne ya tattarawa dady kayanshi ya kaimai ,dady ko kallonshi baiyiba shikuwa Humaid mamakin abinda dady 'yayimai yakeyi ,kiran Jalal yayi a waya yake fad'amai halinda yake ciki ,Jalal cikin k'unar'rai yace ”to Allah ya kayauta nikam ina goyon bayan dady kasancewar baka damu da Khadija ba,Humaid ne yaja waya ya kashe saboda 6acinran yafara isarsa." Washe gari akayi dinner anzubar da kud'i a bikinnan ,Humaid ko tunaninshi in kud'inshi suka k'are ina zaisami wasu ?amma bashida 'amsa gashi yarinyar sai k'irk'iro hidimomi takeyi kuma bayason yin harkar k'aranta hmm ,momy kam tamik'wa 'Allah komai ganin Khadija batada niyar dawowa gashi yau watanta biyu bata gida 'Allah yasa dai tanacikin k'oshin lafiya . *WEEDING💖💫* Yaune dubban jama'a suka shaida d'aurin auran Humaid ADAM da 'amaryarsa KHAIRAT USMAN DOLLARS akan sadaki dubu d'ari biyar hmm tofa riders kunjifa 😉,kowa mamakin kud'in auranan yakeyi amma babu mai bakin mgna kasancewar gaba da baya securitys ne kewaye da gurin ,y'ar manya kenan,misalin k'arfe 9pm aka wuce da ita gidanta ,duk iskancin su saida suka yaba da gidan saboda ba k'aramin kyau yayi ba misalin k'arfe 10pm kowa ya watse daga 'amarya sai ango ,bayan sunyi sallah ne ya dafa anta yayi mata 'adu'a daganan aka faracin kaji ,bayan sun kammalah ne Humaid yashige wanka 'a can toilet d'in shi itama 'amaryar wanka tashiga ta sanya sleeping dress.....✍️✍️✍️. Mom Islam ce *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya

Table of Contents

Chapters

32 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32