Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

Ladidin Kauye Book 1 Complete Hausa Novel 1,192 words 0 views Progress saved
Download Book

?"sosa kai Humaid yai yace ”tace batason yawo lolz tunkafin ka tambaya hh,a tunanin su momy cikine da ita dan yau bikinsu 1 month kenan ,ficewa yai sunata sanya mai albarka komawa gidansa yai yasami gimbiyar na goge TV k'arasawa yai ya rungumeta yana cewa lovely munsami cigaba fa kitayani murna ,murmishinta tayi mai tsada tace ”Allah ya tabbatar da alkairi ,wanan adu'ar tasa yaji dad'i sosai ,yace to kishirya muje tare a'a tace ”a tak'aice shiru yai bai sake magana ba ,yanason cewa ki shiryamin kayana a jaka yakasa ,hakadai ya shirya da sauri sauri ,Jalal ya kira akan yazo ya kaishi airport sai ya dawo da motar ,yayi yayi Khadija ta rakashi koda airport d'inne amma ttak'i." Haka tayimai Allah ya tsare ,yana tafiya ta fashe da wani matsanancin kuka ,ring d'in wayarta taji mik'ewa tayi ta d'auko wayar ganin number babu suna yasata kallon number, dauka tayi had'e da sallama dagacan 6angaren akace ya kike kwalli lpy Lou Khadija tace ”dan bata gane mai maganar ba Fati ce kokin manta da mukayi school tare oh na tuna yakk hope kina lpy eh ya amarci dariya Khadija tasa tace ”amarci nan sai wanda ya k'aru daganan sukayi sallama ,zaman shirunne ya isheta ta zari hijab ta shiga mak'otan su gidane tangameme kuma tsararre da yafi nasu komai ma nocking takeyi amma shiru , can mai gadi ya bud'e yana kallon Khadija yace ”daga ina ne ?cewa tayi ga gidnmu nan wanan na jikin nakun ,Allah sarki yace dagan an yabata hanya ta shige ,da isaera k'ofar parlorn wata k'ofa ce ta glass tana haske kala kala sallama tayi jitayi an amsa ,matar dai batasan Khadija ba amma dayake batada girman kai yasa tace toshigo mana sister." Shiga tayi matar da a shekaru zatayi 27 tace ”saidai ban ganeki ba wlhi tana murmishi ,Khadija ce tace ”ga gidanmu nan jikin naku ,oh ko kece amryar da aka kawo kwanaki 8 months da suka wuce ,jinjina maganar Khadija tayi tace ”wata takwas kina nufin Humaid yayi aure kenan ?matar ce ta dubi Khadija tace ”oh su6utar baki please karki tada hankalinki ita wacan ba zaman aure ya kawo ta ba ,kinga ni sunan na Rahma yarana biyu kin gansu nan a photo yarane kyawawa masu kamada uwarsu sunsha kyau sosai Khadija ce ta dubi Rahma tace ”ni kuma sunana Khadija danan hira ta 6arke kamar sun dad'e da sanin juna horn sukaji Rhma ce ta mik'e tana lek'awa ta window ,oh kinga sweety ya dawo please ina zuwa , Khadija ce ta mik'e window da Rahma ta lek'a nanta fara lek'awa wani kya kyawan magidanci ta gani fari sol kamar bature ,hango Rahma tayi ta bud'e masa mota ta kar6i jakar ta rataya ta kuma ruk'o masa hannu shikuma ya rungumota suna tafiya suna dariya ,Khadija ce tace ”danasan iskancin da zan gani kenan da banzo gidannan ba wlhi ni nazo domin d'ebe kewa amma naga abinda yafi k'arfina nifa bazan iya k'arewa a yiwa namiji bauta ba hmm ,ita kad'ai taketa maganarta ,can kuma taji gabanta na fad'uwa sosai ,yarinya tagani wacce zatayi shakara hud'u a duniya tace ”jeki cewa momynki bakuwar ta tafi ,da gudu ta shige tana cewa momy bakuwa zata wuce ,OK kice ganinan Rahma ce tace ”sweety zani yiwa bakuwata sai gobe ,janyota yai yace ”daga ina tazo a mak'otanmu take ,Rahma ta fice tana dariya ,samun Khadija tayi a bakin get a tsaye ,Khadija ce tace ”to aunty Rahma sai wani lokaci godiya Rahma tayi mata ,Khadija ta fice.shige ciki....✍️.*LADIDIN KAUYE* funny & love story 49_50 Jin fad'uwar gaban ya tsananta sosai yasata k'ara saurin tafiyar ta ,tana dosowa bakin get abinda taganine yasata kurma uban ihu ta fad'i sumammiya . Sahura ce zaune tana cin tuwo tana turo baki ,inna Hauwa ce tace ”nifa banasan kinibibi garama abincin gidanmu naku da ko kafi zabo babu ,kuka Sahura ta fashe dashi tace ”ni walahi sonakeyi in koma jos gurin Ladidi ,zaro ido inna tayi tace ”to ga hanya nan kitafi k'wad'ayayya sunmayi namijin k'ok'ari da har kikayi musu sati biyu batare da sun koroki ba ,wani kallo tayiwa inna harda murgud'a baki tace ”to dan kiji ma yasin ni bazanyi aure a nanba saboda talauci yayi muku kanta ,salati inna keta jerowa ita ko sahura surutunta take jerowa ,jin salamar yaro yana tallar alele hhh fans means allale ,tace ” kai d'an hanse kawo dan uwarka ,inna ce tace ”walhi ki kiyayi zagi saikace baki zuwa islamiya ,mugud'a inna baki tayi hakan yabawa inna damar yin shiru ,Sahura ce tace ”wa yaron biyar biyar ko¿" a'a yaron yace wake ya k'ara tsada goma goma ne , cewa tayi to sako na wazobiya inna mik'omin kwanon kusa dake ,mik'o mata inna tayi duban yaron tayi tace ”kasamin manja da yaji sosai ,bayan yasa ne tace ”inna bismillah kawo kwanonki ,inna da bata wuce tayi ta mik'a kwano aka samata guda d'aya ,Sahura ce taga yaronna kallonta cewa tayi d'an hanse zakaci alelen ne eh yace aikuwa tace to ci d'aya da rabi ninikuma inci biyu inna ga wanan rabin ki kara ,inna na rawar jiki ta kar6i alale tanaci tana lashe rroba." Saida suka gama ci yaron yace ”Sahura bani kud'in ?" cewa tayi kai na nawa kaci ?" yace ”to ai kece kika bani kyauta ,juyawa tayi gurin inna tace inna kinci na sha biyar ko ? eh inna tace tana zaro ido to talatin kenan ungo murtala sauran kuma sai kubiya ,yaronne yafara kuka yana ihu ,shigowar malam Adamu yasa Sahura zamewa ba tare da kowa ya ankare ba ." 6angaren su Jalal kuwa soyayya suke zubawa wacce babu algus kowa bayason yaji 6acin ran d'an uwansa shiri takeyi zatace hospital gaishe da Khadija da ake yimata k'arin ruwa Jalal ne yace ”Honey inkin gama kizo mutafi ,shagwa6e fuska tayi tace ”anya babyn ma zaibari na fita kuwa ,k'arasowa Jalal yai dai _dai saitin cikin nata da zaiyi wata hudu ya kasa kunenshi yana dariya ,girgiza kai yayi yace ”to baby's sunce ko America zaki saikin dawo ,dukan wasa ta kaimai tana cewa tabb barinzodai mu tafi dan naji ance jikinata yayi tsanani ." Emergency room aka kwantar da ita saboda lokacin da ta yanke jiki ta fad'i Allah yasa da mutane a gefe ,kwance take ansa mata oxygen wato abin nunfashi ,nunfashinta baya fita sosai kowa ya cire rai da khadija momy kuwa sarkin kuka kullum cikinsa take tanacewa kukuma jarabawarku kenan wayo rayuwa, Saudat ce tayi sallama ita da Jalal amsawa su momy sukayi itada k'anwarta durk'usawa har kasa sukayi suka gaidasu momy dagan an ya ajiye food folks a gefe yace "ya jikin Khadijan da sauki momy tace ”had'a baki sukayi gurin cewa Allah yabata lafiya amen momy tace ”bayan Jalal ya zauna ne yace ”momy number ya Humaid bata shiga yau 3 days kenan ina gwadawa amma a kashe ,momy ce ta share hawayen da suka zubo mata tace ”shima dajin wanan lamarin da yafaru a gidannasu ya kwanta rashin lpy dan naji ance jikin ya tsananta sosai ,Jalal ne ya tausayawa yayan nashi yace ” momy insha Allah jibi zantafi dubo shi to Allah ya kaimu tace ”daganan shiru ya biyo baya." Momy ce ta shiga room d'inda

Table of Contents

Chapters

32 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32