Chapter 22
Chapter 22
,shikuma yaya Humaid d'in ku yafemai ,momy batace komai ba ta share hayenta tace ” daughter Allah yayimiki albarka mu mun had'aku ke baki bijire mana ba 'amma shi ya bijire mana ,hak'uri Khadija tashiga bawa momy .... Washe gari dady 'yadawo daga tafiyar dayayi ,ganin Khadija 'a parlour yasashi dad'a wara iadanu tace” Khadija saukar yaushe?cikin ladabi ta gaida dady tace ”jiya kanta 'a sunkuye masha Allah dady 'yace daganan ya wuce ciki ,Jalal ne yashigo da y'ar dariyarsa yace ”albishirinki ?goro Khadija tace fari ko ja Khadija ce tace ”fari k'al ma ,zama yayi kujera mai kallon tata yace” nakusa yin aure ,tsalle ta buga saida su momy suka fito suna cewa ,maiyafaru ne hayaniya tayi over ¿" Khadija ce tace ”yaya Jalal ne zaiyi aure zaro ido momy tayi tace ”to yaushene mukam bamu sani ba?Khadija ce tayi shiru cankuma tace ”yaya Jalal gayamin in sanar dasu ,dukkansu tabasu dariya har dady sanda ya dara ,shiyasa tafiyarta kokwa yai missing d'in dariya..... Dady ne tace ”ai bikin da saura tunda saura 3 weeks ,Khadija cikin murna tace ”tabb nikam wazaiyimin anko?tazuba tagumi momy ce tace ”da kinada saurayi da saiya yimiki ,dariya tasa tace ”tabb aikuwa momy ke zakiyimin atamfa da material dakuma gwagwaro tunda naji d'azu yaya Jalal suna waya da 'antyn tamu ,momy ce tazaro ido tace ”to wanan kayan da kika kirawo sunkai 50k Khadija ce tace ”hh momy karki damu inbasu isaba zan k'ara miki dady dayaketa dariya yace ”momy and daughter anfansu a rana,dariya Jalal yayi ,momy ce tace ”to naji karsujimu , juyawa Khadija tayi tace ”ywa dady kai kuma gyale da takalmi da jaka da sark'a da d'an kunne ,dady shima ganin abin yazo kanshi yasashi cewa kekuwa bakida samari ne ?dariya tasa tace ”dady nadena samari ,kowa yazo yagansu zaiyi sha'awarsu kasancewar dady da momy suna wasa da y'a y'ansu ... Dady ne yace ”to naji shikuma Jalal mai zai siya miki ,shima juyawa tayi tana kallonshi tace ”yaya ango turare da kayan makeup ,dariya yayi yace ”karki damu autar momy ,daganan suka mik'e kowa ya shige nasa dakin , dare nayi tazo yiwa momy sallama saiga wani yaro nan ya shigo wai ana sallama da Khadija ,zaro ido tayi tace ”to koma waye ya makaro ,momy da take jinta tace ”kaje kace yayi hak'uri gobe yadawo ,to yace ”yaron ... Washe gari momy da dady da Jalal da Khadija sun taru a palory ,dady ne ya dubo number Humaid ya danna kira ,Ring daya kamar mai jira ya d'auka yace ”aslamu alaikum dady ,dady cikin kakkausar murya yace ” ba doguwar sallama mukeso ba kazo yanzu kuma banason 6ata lokaci ,insha 'Allah ganin zuwa , gaban Khadija ne fara fad'uwa tana zaro ido ,had'a ido da Jalal sukayi yayi mata gwalo ... Cikin mintuna kad'an saiga Humaid nan ya rame sosai yayi bak' ,duk tsanar da momy tayimai saida ta tausaya mai sosai saboda ko shima dady bai nuna'a fuska ba ,sallama yai yashigo ,ganin Khadija takuma k'iba da kyau yasashi tsayawa kallonta ,wani mugun kallo ta watsamai ,saida yasami guri ya zauna ,yana zama dady 'yace ”dama ba komai yasa na kirawoka ba saidan inason kabawa Khadija takardar saki kuma ba saki biyu ba saki uku nakeso ,cikin bada umarni dady 'yayi maganar ,kid'emiwa gamida k'arewa Khadija kallo yakuma duban momy kozatace wani abu ,ko kallon inda 'akeyin magana batayi ba , wasu zafafan hawaye ne suke fitowa daga fuskarshi ,ya durk'usa gaban su momy 'yace ”mom da dady dan darajar fiyayyen halitta dan darajar al qur ani ku yafemin wlh na gane kuskurena ,dan Allah ,kuka Jalal yafara 'abinka da d'an uwa yace ”momy da dady maizai hana ku yafewa yaya Humaid tunda har yagane kurensa kutuna fa 'Allah munayimai laifi a kullum kuma mu rok'eshi ya yafe mana wasuma bazasu rok'eshi ba kuma baya fushi dasu to dan hasken annabi Muhammad kowa yace”sallalahu alaihi wa sallam ,mun yafe maka, momy tace ”idanunta na tsiyayar k'wallah dady ma cire farin gilass d'insa yayi yace ”mun yafe maka Humaid .... Wani farinciki da nishad'i suka ziyarci zuciyarshi d'a hannu yayi samma yana godewa 'Allah ,dady ne yace ”to saura maganar takardar saki ,Humaid ne yaji k'irjinsa na dukan uku uku yace”dady ai na d'auka shikenan ,momy ce tace”yanzu dai za6i yarage ga mai zaman gidan ,Khadija dai an d'aure mata kai dan tarasa yazatayi kawai tafara kuka tana cewa walhi bazan komaba , Ran momy yad'an 6aci kad'an to kunsan tsakanin d'a da uwa sai Allah haka 'aka tashi taro abin babu dad'i . Washe gari har k'arfe goma bata ko lek'o parlor ba ,momy da bata iya daure rashin ganinta yasata nufar d'akin Khadija , zaune tasameta tanata gurshek'en kuka ,momy ce ta dafata tace ”au akan maganar Humaid ne kike wanan kukan ?to sha kuruminki saikin yarda zaki koma, amma inason baki shawara inhar kina sinsa to walhi karki zurfafa jamasa rai 'inkuwa bakya sansa kiyi magana tun wuri ,shiru ne yabiyo baya ,momy jin Khadija tak'i magana yasata mik'ewa ta fice, kukane ya kuma ku6cewa Khadija jitakeyi dama mutuwa tayi ta huta da duniyar nan saboda k'uncin da take ciki... Gobe juma'a gobe ne d'aurin auran Humaid duk da bak'in cikin da Khadija take ciki bai hanata murna ba ,kar6o kayanta tayi a gurin momy tanata yimata godiya dady ko tun kafin bikin agama tashi siyayyar haka ma Jalal... *WEEDING*💍🥰. Kowa na gidan shirin zuwa d'aurin aure yakeyi Humaid kuwa shine kan gaba ,misalin k'arfe biyu dubban jama'a suka shaida d'aurin auran JALAL ADAM DA AMARYARSA SAUDAT KABIR akan sadaki dubu d'ari ,kowa kagani yana cikin farinciki ango kuwa inkaga bakinan kamar gonar auduga sai gaggaisawa yakeyi da mutane sunata yimasa Allah ya sanya 'albarka ,shirin komawa gida sukayi ,saboda zasuyi shirin zuwa reception gurin rawa ... Humaid na shigowa da fara'arsa kamar shine angon yacewa momy an d'aura fa ,cikin farinciki momy ta kwararo adu'oi tana murna cikin zuciyarta kuwa saitaji tausayin Humaid sosai ,amma 'a kullum tana adu'ar Allah yasa Khadija tasoshi, motoci ne zasu wuce itako Khadija batasan lokacin tafiya ba domin tatafi gurin kwaliya ,basu jima da wucewa ba saigatanan ta dawo ,momy na ganinta tace”kai kai kai ko amarya albarka dariya Khadija tasa tana cewa momy barinje in shirya kar masu moto suzo ,rik'e baki momy tayi tace ”tabb aikuwa sun wuce ,ida nunta sunyi rau rau alamun zatayi kuka tace ” nashiga uku nikam wazai kaini ,momy ce tace ”barin kira Humaid ina tunanin k'ila basu fara d'aukar y'an matan ba ,wani kishi ne yataso mata amma bata nuna inda momy zata gani ba ,ring d'aya biyu akayi sa'a ya d'auka Aslamu alaikum yace ”momy ce tace ” walaikumusalam kazo ka d'auki matarka tarasa mota ,cikin zumud'i yace ”ganinan zuwa momy ,Khadija ko harta shige gida sa kaya saboda kafin ta tafi tayi wanka , wow tana sanya kayan suka fito da ainihin kyawun ta inka ganta zaka rantse itace amaryar dukda nima banga amaryar ba ,da k'yar tasa skirt d'in domin ya matseta sosai gakuma takalmi mai tsini sosai ga nad'in gwagwaro da 'akayi mata ,d'ankunne da sark'a tasa ta d'ibi kud'ad'en datakai akayimata canji aka bata sababi ,mayafin kayan ta yafa a kafad'a ....✍️🤙. Mom Islam
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32