Chapter 2
Chapter 2
ta dubeshi kana tace "meyasa meka ne ɗan gayu¿ cikin su babu wanda ya kulata bare su waigo ta Humaid ne yace ja motar Jalal muyi sauri mu isa gidan . Sun zo dai dai k'ofar gidan LADIDI tace "to munzo seku fito Humaid dake ɗin gisa ƙafarsa yace "to ai seki koma tun da kin rako mu. Zaro ido waje tayi kana a zuciyarta tace lallai wannan besan ko wacece LADIDI ba . Duban ƙafar Humaid ɗin LADIDI tayi kana ta fashe da dariya Humaid da babu halin gudu ya dura mata zagi Jalal ne yace "tunda ta nuna mana ƙofar gidan to muje ka kyale yarinyar nan . Hango wata zabge giyar sanda tayi ta ɗauka kana ta gyara bakinta seda tabari Humaid yazo dede saitin shiga gidan ta zula mai a kafar da tayimai allura zubewa yayi a ƙasa yana ihu da gudu ta ƙasa... Malam adamu ne yaj ihu kuma na babban mutum da sauri ya ƙaraso Jalal ne yace "barka malam , malam adamu ne yace a,a wana ke gani kamar yan birni¿ Jalal ne yace "malam mune wata yarinya ce tara komu gidanka gashi ta bugawa Humaid sanda a ƙafa ta gudu ,malam yajin jina zancen kana yace "nasan ba wata bace illa LADIDI wannan aikin seita . Humaid ne yayi ƙarfin halin magana yace "Jalal kaje kane momin yarin yar nan senaga waye ubananta. Malam adamu ne yace "wlh gara ka hakura saboda wanan yarinyar ana tunanin tana da aljanu ......✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽. *_~MOM ISLAM CE✍🏽.~_* *LADIDIN ƘAUYE.* _funny & love story._ *Labari mai ban dariya haɗi da faɗa karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:ZAINABU ABU* *_AND NOW *_ *LADIDIN ƘAUYE.* *BIMILLAHEER RAHMANIR RAHEEM.* *EPISODE 3&4.* ___malam adamu ne yayi musu nuni dasu ƙarasa cikin gidan inna Hauwa matar malam Adamu ta na ganin su ta shiga yi musu sanu da zuwa d'akin malam Adamu suka wuce kai tsaye Humaid ne yayi rau rau da ido kamar me shirin yin kuka yace "Jalal please help me jalal da shima hanka linshi ya fara tashi yace "sorry brother anjima ka d'an zakaji jikin naka ya koma normal Humaid ne a ts,wace ,ya dubi Jalal kana yace "baka san azabar da nake ji bane shi yasa . Jalal ne ya mik'e jiki babu k'wari yanufi gurin da inna hauwa take tambayar ta yashiga yi akwai asibiti anan kusa¿ inna hauwa dake dama fura da nono ta ce "eh akwai amma fa akwai tafiya sosai Jalal ne yace indai akwai barin yiwa Humaid magana mutafi inna hauwa ce ta kwala wa malam adamu kira shigowa yayi d'auke da ledar lemu da ayaba da kankana ajiye ledar yayi ganin yanayin Jalal malam Adamu ne ya ce har yazu jikin humidun ne eh Jalal ya ce asibiti nakeso mu kaishi ko aliura ayi mai . Shiga d'akin sukayi suka temaka mai ya mike suka sa shi a mota seda suka yi tafiya me nisa kana suka shiga asbitin . Wani likita ne yazo gurin malam Adamu hannu ya mik'awa malam Adamu suka gaisa kana likitan yace "baba waye babu lpy ¿. malam Adamu ne ya nuna Humaid da zazza6i yarufeshi ri rik'eshi sukayi yanuna musu d'akin kwantar da marasa lpy ruwa aka fara samai kana aka yimai allurori bacci ne ya d'auke shi me nauyi Jalal ne yaji cikin shi na kukan yunwa mik'ewa tsaye ,yayi kana yace mala barin d'an fita yanzu zan dawo. Malam Adamu ne yace ina kuma zaka¿ Jalal ne ya ce wlh am feeling Hungary malam Adamu ne ya zaro ido kana yace naji kamar kace kwan giri Jalal ne ya tun tsure da ,dariya kana yace . "Cewa nayi ina jin yunwa malam Adamu ne ya ce au to ko in koma gida ne in taho muku da fura da nono ¿". Jalal ne yace a,a ai dazamu taho naga masu saida abinci malam Adamu ne yayi mai Allah ya tsare Humaid ne ya farka d'auke da salati a bakin shi. Malam Adamu ne yace sanu Humaidu,, humai ne ya dubi malam Adamu kana "yace yauwa sannu ina Jalal yayi ?". Malam Adamu ne yace Jalal yaje siyo abinci yanzu ze dawo . Likitan d'azu ne yashi go d'auke ta ,takaddar salama mik'awa malam Adamu yayi kana ya tambayi Humaid ya,,ya kejin jikin nashi Humaid ne ya ce wlh yanzu babu inda yake ciwo hamdala malam Adamu yayi . Jalal ne yashigo da ba bbar leda a hannun shi kifi yasiyo soyayye da kuma kaza guda biyu gasassu malam Adamu ne yace duk wanan kayan ina za,a kai su lemun kewalba ya mik'awa Humaid da kifi domin Humaid d'in ma,abocin son kifi ne jalal ne ya d'auke kaza guda daya ,ya mik'awa malam Adamu . Malam Adamu ne ya e a a ni bazan ci ba ,dole dai seda ya kar6a tukun ya d'an sha lemun ya barsu a gurin ya nufi masalaci. Suma bayan sun gama sallah sukayi kana suka biya likita kud'in shi ,suka hau mota suna cikin tafiya suka hango Ladidi tana jifan mangoro abishiya Humaid ne ya dubi jalal yace tsaya ga mahau kaciyar ,yarin yar nan . Malam adamu ne yace kufa kiyayi Ladidi kotayi lefi babu me d'aukar mataki Humaid ne a zuciye ,yace wai malam wanan yar gidan waye ¿malam adamu ne ya ce yar gidan amini na ne malam musa. Humaid ne ya ce dan Allah malam kabari ,inkoya mata hankali malam adamu ne ya ce jalal kawuce mutafi na gaya maka kar katsaya . Humaid ne ya lek'a ta window yace ke Ladidi wlh kinci bashi zanga uban daya tsaya miki a fad'in a kurkin k'auyen nan . Ladidi ,da kamar jira takeyi ta sami abokin fad'a dagudu tayi ,yo gurin motar amma ina jalal ya k'ara gudun motar duwatsu tasamu tanata kai jifa amma babu sa,a jifan data kai na k'arshe se a bayan wani bafula tani yana tsugune a wata gona yana kashi yaji ,jifa a bayan sa dasauri yaja wandon sa ya rik'e yana ihu Ladidi data lura tayi mugunta tazo guduwa bafula tani yace yau k'aryar ki takare kamota yayi kana ya dunga dukan ta . Yana saketa ,ta mul mulo zagi shikuwa bafula tani dayaga Ladidi tafi k'ar fin shi ya shemeta da sanda ko motsi bata yi . *_FARKON LABARI*_ Malam musa shine ma haifin Ladidi ita kad'ai Allah ya basu tun tana k'arama bata ji ko,kad'an bare duka shima be dame taba abota ce me k'arfi ta shiga tsakanin malam musa da malam adamu mutanen kirki . Malam Adamu shine k'anin mahaifin su Humaid da jalal ma haifin su Humaid wato alhaji abdullahi tun bayan rasuwar mahai finsu wato kakan su Humaid kenan da mahai fiyar shi. ya had'a kayan shi yatafi neman ilimi shi kuwa malam adamu be bi d'an uwan ,nasa ba ya zauna ,yana koyar da almajirai . Shigar dadyn su Humaid garin jos ya had'u da wani bawon Allah ya d'aukeshi zaman shagon atamfofi suna samun alkairi sosai saboda alhaji abdullahi akwai amana baya cin kayan da bana shiba shiyasa yake zaune lpy da mutane. K'watsam wata rana uban gidan shi yabashi kyautar wani katafaren shagon da yagina had'i da bashi kaya masu yawa acikin lokaci k'alilan kud'i suka bunk'asa uban gidan nashi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32