Chapter 17
Chapter 17
dady yace”to inkun kammalah gamu nan a hanyar zuwa airport ku hanzarto angama komai tun jiya to tace”gamunan zuwa dady ,zuwa d'akin Humaid tayi tace ”kafito gasu dady can a hanyar airport mik'ewa yayi jiki babu k'wari yace ina kayana?cewa tayi gasunan a jaka bud'e gurin kayan 'nashi yayi yakuma lodar 'rigada wando kamar yasan bata d'ibarmai ba ,cemata yayi bar 'rawar jiki dan kona sami lafiya 'aure zan k'ara ,Khadija ce tace ”a hakan da babu k'arfin jikin kana tafiya kamar mace,zaro ido yayi yace"wlh zanci ubanki shigewa tayi tarabu dashi tasandai koba komai ta gasamai magana. Shigewa mota sukayi sun d'anyi tafiya sanan suka iso airport d'in samunsu momy sukayi a zaune suna jiransu k'arasawa gurinsu sukayi suka durk'usa suna gaisuwa Humaid dak'yar ya mik'e itako Khadija dariya takeyi k'asa k'asa jin lokacin tafiyarsu yayi yasa momy yimusu fatan 'nasara ta mik'awa Khadija wani babban jaka mai zurfi ,dady ne yace ”nayima transfer na kud'i bakada matsalar su godiya yayiwa dady daganan suka shige jirgi ,hawaye Khadija tafara shareware saboda tasan momy ma dauriya kwai takeyi ,jin tashin jirgin yasata rik'o Humaid ta matseshi tsaki yaja yace ”dalla ni karki sakamin k'azamin jikinki banza kawai ko kulashi batayi ba tacigaba da rik'eshi ,shikuwa bashida k'arfin kokawa yasa ya k'yaleta....✍️✍️✍️. Mom Islam ce *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 31_32 _____Suna sauka cikin ikon Allah saiga wani bature yazo yake cemusu ance yanuna musu masaukin su Humaid saboda rashin yarda yace "saiya kira dady aikuwa yana kira dady 'yace”nine na turoshi dafatan kun sauka lafiya ?lafiya Lou Humaid yace”daganan suka shige motar wanan bature ,itadai Khadija gajiyace ta buwaye ta dan burin ta bai wuce taganta tana hutawa ba ,wani katafaren hotel suka sauka Khadija ce tazaro ido tace"nifa tsoron jajayen fata nakeyi wallahi kar azo angama cinikinmu, Humaid ne ya gimtse dariyar sa shikuwa wanan Bature babu abinda baijiba wanada Khadija tafad'a kasancewar yana mu a mula musulmai sosai amma shi Christen ne saboda baya sallah ,door bell baturen ya danna k'ofar ta bud'e da kanta zaro ido Khadija tayi tace”to Allah gamu gareka tana tafiya tana sambatu shikuwa Humaid ko kallonta baiyi ba ,direct wani rantsatsen step naga sun hau d'aki mai number goma suka shiga ,Humaid ganin ba'ayi maganar komai ga shuwagabanin hotel d'inba yasashi cewa to sukuma masu hotel d'in anbiya sune?eh baturen yace”tun jiya dadynku yayi komai ,godiya Humaid yayimai mutumin 'ne yace”sunanan Joseph barin baka number ta musayar lamba sukayi daganan Joseph yace”suyi wanka su huta za'a kawo musu abinci . Tana shiga d'akin Humaid ma yashigo tunda tashigo take kallon d'akin kyau tsari gakuma nerorin da 'aka kashemai tabb tace ”lallai wasu basusan zafin kud'i ba ,Humaid da gajiya ta tarumai yace”to sannu 'uwarsu zaki 'iya fita ki sanar musu ,ko kallon inda yake batayi ba tashige bathroom wanka tafarayi kasancewar akwai sabon sabulun wanka da sabbin brush da man goge baki saida tayi wanka sanan ta d'auro alwalah tafito ganin har bacci yafara d'aukar Humaid yasata kurma uban ihu tace”wayoo nashiga uku ,a firgice Humaid ya farka yana salati ganin Khadija tayi shuru yasashi cewa komai aka had'a da jaki saiyyaci kara ,zaro ido tayi tace”waye jakin nikake kira da jaki, murmushin takaici tayi tace ”d'an adam mai mance hallacci babu komai kasan ba'acin bashina ,mamakinta yakeyi dahar take gayamai maganganu san ranta saboda taganshi a kwance bazai 'iya 'aikin k'arfi ba yasa takeyimai wulak'anci ,dariya yasa lokaci d'aya kuma yace”yaro baisan wutaba saiya taka." K'yaleshi tayi tafara sallah tana idarwa ta dubo al qur'anin data taho dashi tafara rera karatu , idon Humaid a lumshe kamar mai bacci ya bud'e ido yana saurarrar karatun Khadija jiyakeyi kamar karta dena ,bayan takammala karatunne ta mik'e tayi gurin kayansu bud'e jakarta tayi ta dubo atamfa rigada skirt mai adon flowers green zatasa kayan ta tuna 'aifa Humaid na d'akin juyawa tayi tace ”malam zaka iya juyawa saboda zansa kaya karkuma 'a kalleni ehe, juyowa Humaid yayi yace”wanan banzan jikin'naki mezan kallah jikinda kowa yagama ganinsa ,tanajin takaicin wanan kalmar amma 'akwai lokacin ramako, d'ibar kayan tayi takoma bathroom ta sanya sanan tazo tana shafa mai kasancewar garin da zafi kuma dukda sanyin AC mutum gumi yakeyi ,kwaliyarta tayi a nitse sanan wuce dining table d'inda 'aka kawomusu abinci ganin cimar kamar ba irin tata ba yasa ta had'e fuska tana rik'e ciki ,hango wayar tafida gidanka tayi ganin 'number su a calendar yasata d'auka cewa tayi nifa bazan iyacin wanan jagwal gwalon ba 'akawomin tuwo kokuma indomie mutumin da baigane maitake cewa ba yace ” give me one minute please am coming zaro ido tayi tace ”tabb 'banza shima turancin bai gama bakinsa bba." Humaid daketa dariya yana k'arawa yace”LADIDIN KAUYE y'an mata had'e rai tayi tace”wallahi kabari dan banhuce na d'azu ba, shiru yayi dan yasan komaiye ma zata rina 'aikatawa ,nocking aka farayi Humaid ne ya lala6a ya mik'e saikuma ya tsaya yace ”saikije kiyimai bayani,Khadija ce tace”bagane nawa turancin zaiyi ba dan 'naga shima koyo yakeyi yanzu hakama brain d'ina tafi tashi ,wucewa kawai Humaid yayi ya bud'e k'ofar mutumin 'ne d'auke da farantin abinci bud'ewa yayi yaga indomie ne aciki godiya yayiwa mutumin daganan yasauka k'asa da tiren abincin samun guri yayi yafara loda indomie saida ya cinye duka sanan ya tashi yabar plet d'in agurin yakoma sama. Samunta yayi ta rafka uban tagumi tana kuka ko kallon gunda take baiyi ba bare tasanma yaganta taji dad'in 'narkewa bathroom ya wuce yayi alwala yazo ya gabatar da sallah tunda yayi sallama yaketa jero adu'a 'akan Allah yabashi lafiya ,itadai Khadija tarasa meke yimata dad'i a duniya kasancewar bata ragawa ciki ko kad'an mik'ewa tayi taduba maid'an dama dama tafara tuturawa badan yayi mata ba tana gamaci ta d'auki waya takirawo momy cikin farinciki momy tace” daughter dafatan kuna lafiya dai ko?eh muna lafiya Lou "amma momy 'yaushe zakuzo?momy tana murmushi tace”gobe ne insha Allah muna zuwa zamu wuce hospital amma zaku rigamu wucewa,to kawai tace shikuwa Humaid dama can magana ba damunshi tayiba, daganan sukayi sallama da momy. Dare nayi basuci wani abinci mai nauyi ba ,Humaid na k'ok'arin hayewa gadon tarigashi ,hak'ura yayi ya koma k'asa ya shinfid'a bargo ya kwanta . Washe gari bayan sunyi sallahr ashba babu wanda ya koma shirin tafiya 'asibiti sukeyi bayan Humaid ya fito daga wanka yaduba jakarda Khadija, ta lodamai kaya 'acikin ganin gajerun wanduna yasashi salati yace”wato kinmaidani d'an iska kenan ko ?cigaba tayi da kwaliyarta daganan ta mik'e tana cewa to inka shirya nizan wuce ,Humaid ne yace”kin dad'e baki wuce ba banza kawai jibeta 'ahaka kamar saliha ,shiru tayi saboda batason wanan kalmomin da yake jifanta dashi amma burinta lokacin yazo . Yana gama shirin ya fice ko magana baiyi mataba jitayi yana kiran Joseph a waya dagudu ta fito tana tsaki ,ganin Humaid yashige mota yasata bud'ewa tashige da sauri wani katafaren hospital suka nufa suna sauka koshi Humaid ' d'in saida ya jinjina kyau irinna asibitin suna zuwa 'aka tarbesu office suka wuce domin ganin babban likitan suna shiga sukaci karo da wani mutumin farine dogo yanada jiki amma ba sosai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32