Chapter 30
Chapter 30
tsaye ga wasu kuma dake ririke da last speaker suna yimasa tambayoyi to maiya kaika aikatawa y'ar minista fiyad'e ? tsautsayine yace ”a takaice ,wasu tambayoyin aka kuma jeromasa akan cewar kwanaki ankashe mai gadi agidan yaron Alhaji ABDULL... ko zaka iya bamu cikakkiyar amsa eh ninne na kashe shi ,kuma ba shi naso kashewa ba tsohuwar budurwata naso kashewa kokuma mijin da ta aura ,bayan nan ko akwai wani kisan daka ta6ayi babu nasani tawa ta k'are k'arfin arzik'in mahaifina bazai fitar dani daga hannun hukuma ba_. Daganan aka wuce gurin . Kukane ya kufcewa Khadija sbda tayi dana sani akan sanin Ammar datayi amma Alhamdulilh tunda gashi a hanun hukuma . Suna cikin alhinin Ammar sukaji sallama ,Humaid ne ya mik'e jiki a sanyaye bud'e k'ofar yayi yana k'are mata kallo yace Khairat!!!! momy dake baya ta shigo sanye da hijab tace ” daughter kinga yarinyar da tayi sanadin ciwonki nan ,mik'ewa Khadija tayi ta fad'a jikin momy ta saki kuka mai tsuma zuciya d'ago kanta tayi tace ”momy wanan wacece ?"tsohuwar matar Humaid ce ,momy ce tabata kaff labarin auran Humaid 'dakuma abubuwanda suka faru bayan barinta gida da halin da momy ta shiga ,kuka Khadija takuma sawa ta durk'usa ta rik'e k'afar momy tace ”momy dan Allah ki yafemin,dana zauna da baki dinga zubar da hawayenki ba natuba momy ,d'agota momy tayi tace ” daughter na yafe miki karki damu kowane bawa da tashi jarabawar ,Khairat ce ta durk'usa 'a gabansu momy tace ”dan Allah nima ku yafemin ,nasan na cutar daku gashi ta sanadiyar bin bokaye fuskata ta k'one kowa guduna yakeyi kuma iyayena ma sun tsune min ta had'a hanunwanta biyu tace ”dan Allah Ku yafemin kodan guduna da duniya takeyi ,Khadija ce ta d'agota tace ”na yafe miki Allah ya yafemana ,Humaid da ko kallonta bayason yi sabda fuskarta tayi abin k'yama yace ”indai zaki ficemin a gida to na yafe miki jekiii ya daka mata tsawa momy ma cewa tai ta yafe mata daganan ta fice ,tana fita suka rufo k'ofar d'akin ,jin wani k'ara da wata mota tayi yasasu bud'e get suka fito da gudu ,motace ta kad'e Khairat jini ta baki jini ta hanci ,drivern kuma ya gudu ,cikin azama Humaid yazo ya jijigata jin alamun babu rai a tare da ita yasashi salati momy ma salatin takeyi Khadija kuwa na kuka gidansu ya nufa da ita inda da shigarsu suka tarar da mahaifinta da mahaifiyarta a parlor." Bayan ya gaishesu ne yake fad'a musu tare da Khairat yazo ,a fusace mahaifin nata ya mik'e yana nuna Humaid yana cewa karta sake ta shigomin gida da k'azamin jikinta mai za'ayi da mazinaciya !!! Kuka Humaid yafara yana cewa dady ku yafe mata motace ta kad'eta kuma babu alamun nunfashi a tare da ita momy a razane tayi waje dady ko ciki ya shige irin ko a jikinshi ,momyn Khairat na ganin ta tafad'i ta suma dady ne ya fito da gudu shima ganin gawar Khairat yasashi nadamar tsa tsauran hukuncin da ya yanke akanta yafa cewa nayafe miki Khairat Allah kayafewa Khairat . Wayo Allah mutuwa fa ta kori komai a rayuwa kana yawo da gangar jiki baka saniba to y'an uwa mudinga nufar kowa da alkairi mubi umarnin iyayenmu muzamo masu neman za6in Allah. Gida Khadija suka koma ita da momy sai kuka Allah sarki rayuwa . ********************* Kamar inda kuka sani ne ikon Allah yafi gaban wasa rayuwa tana juyi kala kala wani abin a zahiri wani ko a bad'ini farinciki ko akasin hakan . AFTER 5 MONTHS momy na kwance tana bacci aka kirata a waya cewar matar Jalal ta aihu murna bakin momy baya rufuwa ranar suna yaro yaci sunan Baban Khadija wato Musa yaro yasami gata ta kowane 6angare Khadija kuwa tayi rawar gani sosai dan ba'a barta a baya ba ,lokacin cikin Khadija yana 8 months dak'yar take tafiya y'an uwan momy ma sunyi wa yaron shatara ta arzik'i. Farinciki arzik'i kwanciyar hankali duk familyn sun samu kwanci tashi asarar mai rai cikin Khadija yakai aihuwa zaune take bayanta ya rik'e gakuma mara datasata gaba salati takeyi Humaid dayake kwance yana bacci ya jiyo salatinta ya fito da sauri ganin halin da take cikine yasashi cewa zomutafi hospital ,girgiza kai Khadija tayi tace ”insha Allah a gida zan aihu ,nishi takeyi iya k'arfinta Humaid ne yace ”kid'an k'ara nishi please kidaure rik'eshi tayi kam kam tasaki wani nishi sai ga yaro ya fad'o tana shirin kwanciya taji wata sabuwar nak'udar Humaid yace ”baby gyara na dubaki ,kafin yakai ga dubata sai ga wani yaron yakuma fad'owa ,kuka tafara sosai dan walhi tunda tazo duniya bata ta6a shan zafi kamar haka ba ,Humaid ne ya mutsike yaran da kwa6a6en lalle sbda yana fitarda datti gakuma k'arawa yara lpy bayan mintuna kad'an ya nannad'e yaran ya kwantar dasu kitchen yaje ya juyowa Khadija ruwan zafi ya taimaka mata ya rakata toilet,wanka yayi mata tana cewa da zafi hakadai ya gasa mata jiki ,dawowa yai kan yaran ya tattauna dabino yabasu ya juyo da kunnesu yayi musu kabbara alhamdulih farinciki baiyyane a fuskar Humaid sai da yayiwa yaran wanka ya sanya musu kaya masu kyau sosai dasu safa ,yaga Khadija ta shirya kamar ba mai aihuwa ba sai dai rashin k'arfin jiki ruwan shayi ya had'a mata mai kauri tasha sanan ya kira momy a waya, yake sanar mata ai Khadija ta 'aihu momy ce tace ”wanne hospital kokuma kuna nakune ,Humaid ne yace ”momy a gida ta 'aihu ,da sauri momy ta d'auko hijab tasa driver ya kaita gidan Khadija ,da isarta gidan d'akin Khadija ta nufa ganin babu kowa yasata komawa parlor ta zauna." Tace ”idan kagama kar6ar aihuwar kafito cikin d'aga murya momy take maganar ,Humaid 'dake kwance ya rungume twins d'inshi ya zaro ido yace ”kiyi baccin k'arya please Khady ,rufe idanuwa tayi alamun tana bacci shikuma ya fice parlor gurin momy ,sunkuyar da kai yayi yana sosa keya alakun jin kunya ,momy ce tace ”ina daughter tana ciki yace ”a tak'aice da shigar momy tasamu Khadija tayi baccin gaske hhh mata anji jiki ☹️ rungume yaran momy tayi tana wani farinciki ,number dady momy ta lalubo ring d'aya ya d'auka ,bayan sun gaisa ne take bashi labarin aihuwar khadija murna fall zuciyar dady barinma dayaji momy tace ”yan biyu, Humaid ne ya shigo bayan ya gaida momy tana cemai ya kar6i aihuwar lafiya ? dariya yasa yace ”momy babu wani abu da 'ake buk'ata eh bbu zaka fitane ,cewar momy Humaid ne yace ”yanzu Doctor Umar yakirani a hospital zanje duba wata bbu lpy OK tom Allah yayi albarka ,amma gobe khadija zata koma gidan mu ba hakan yaso ba 'amma babu inda ya iya yace ”Allah ya kaimu. Washe gari momy tazo aka shirya kayan Khady dana boys suka nufi gidansu momy ,tana sauka farfesu yayi mata sallama tana zama momy tasa Ummi wato y'ar aikin gidan ta kawo mata citakeyi bakinta babu dad'i bayan tad'anci kad'anne tacewa Ummi tazo ta d'age ,*LADIDIN KAUYE* funny & love story 57_58 Washe gari Humaid ne yazo cikin wani lallausan yadi blue my kyau fuskar shi sai fitar da tsananin murmishi yakeyi ,kai tsaye d'akin matarshi ya nufa ,sanin yanzu za'a fara yimai katanga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32