Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Ladidin Kauye Book 1 Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
Download Book

sark'a wow ba k'aramin kyau tayi ba ,zama tayi gurin tukunyar indomie tafara baiwa cikinta rabonsa saida taci ta k'oshi tayi gyatsa sanan ta mik'e tayi gurin madai daicin fridge d'inta taciro hollondia mai sanyi ta kkora." Daganan ta 6oye tukunyar . Yana fita direct kitchen yanufa ganin baiga tukunyar daya d'ora ba yasashi zaro ido had'e da dogon tunani ,komawa parlor yayi ya murd'a handle d'in k'ofar jin a kulle yafara tunanin kodai Khadija ce ta d'aukemai hanyar d'akinta ya nufa jin k'ofar ansa key 'yasashi cewa "wallahi koki bud'emin kokuma duk lokacin da kika fito sainayi maganinki , tanaji yana sababi amma fur tak'i fitowa ,gajiya yayi da tsayuwa , komawa d'akinshi yayi ya watsa ruwa daganan ya fito yayi shirin tafiya gurin cin abinci . Tanajin k'arar motarshi ta fito rik'e da gyale a hannunta dakuma takalmi mai tsini yiwa drivern gidan "magana tayi da saurinshi ya taho ya durk'usa 'a gabanta yace " hajiya Mota zakishiga ?"eh tace"daganan ta shige mota suka nufi 6ukur park wato anguwarsu momy ,murna take sosai kamar mai shirin tafiya hajji ,suna isowa kusada gate d'in drivern ta yafara horn mai gadi ne yaje ya bud'e mai daganan suka kutsa ciki ,suna sauka ta ruga ciki da gudu,turuss tayi ganin Humaid zaune yanacin farfesu ,zaro ido tayi tana jujuyasu shikwa yiyayi kamar bai ganta ,fakar shi tayi ta shige bedroom d'in momy da gudu ....✍️✍️✍️. ~MOM ISLAM CE~✍️. *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 25_26 _____Samun momy tayi ta fito daga wanka ,dagudu taje ta rungume momy saikuma ta fara kuka Momy datake murna saikuma 'annurin fuskarta ya disashe kasancewar taga Khadija na kuka ,janyota momy tayi zuwa bakin gado bayan sun zauna ne "momy take tambayarta tare sukazo da Humaid ne ?" saboda taga Humaid 'din bai dad'e da zuwa ba ,Khadija ce ta share hawayen ta tace"momy babu komai kawai farincikin ganinki ne ,badan momy ta yarda ba tace"to nima nayi farinciki da ganinki my daughter ,saidai naga kin rame sosai kodai da wata matsalar ne? a'a tace" Momy ce tace"to gyramin gaban mirror d'innan ,to Khadija tace" tafara 'abinda momy ta sata momy tayi hakane domin tasami damar zuwa gurin Humaid saboda shid'in ma ya rame sosai,bayan momy ta fita ne Khadija tace" na shiga uku gara da ban fad'awa momy komai ba da walhi zata iya fushi da Humaid. "Momy nazuwa parlor tasamu Humaid na danne _danne a waya yana ganin momy 'ya d'ago kai yace" barka da fitowa momyna dafatan kin fito lafiya ? Lafiya lau momy tace"Allah yayi albarka cike da kulawa yace amen momy _momy ce takai dubanta ga Humaid tace"amma dai kuna zaune k'alau ko?"cikin rawar baki yace"eeh eeh lafiya Lou ,momy ce tayi murmushin su na manya tace"bakwa zaune lafiya Humaid a zabure Humaid ya kalli momy 'yace ita Khadijan ce tagaya miki haka ? ko d'aya momy tace"daganan kuma duban Humaid a karo na biyu saboda 'akwai abinda take karanta "cewa tayi karka manta yarinyar nan marainiya ce bamu baka ita dan ka cutar da ita ba kuma na fuskanci ko a lokacin auran kayi farinciki amma metayima dahar zaku dinga cutar da rayuwar ku?" sunkuyar dakai yayi kana yace nikam 'momy saidai kiyi hak'uri dani dan wallahi bazan ta6a son Khadija ba kuma wlhi ko meye ya wanketa zaro ido momy tayi had'e da d'an gutun hawaye tace"ni Humaid kake gayawa wanan kalmar ni ko kukane ya kufcewa momy cikin k'araji tace tunda kazo.duniya bamu ta6a musu dakai ba 'amma zuwa yanzu ne zakace zamudinga musayar yawu dakai ,hak'uri ya shiga bata ganin bata kulashi ba yasa ya durk'usa kan guwaiwar shi yana bata hak'uri,ko kallon shi momy batayi ba ta mik'e cike da matsanancin 6acin rai tace "wallahi wallahi inhar ka cuci Khadija 'Allah ya isa tsakanina dakai!!!." Cikin firgici ya d'ago kanshi da yayimai nauyi yace "ni momy kike yiwa mugun baki " nafad'a nace nafad'a kozaka mareni ne tunda yanzu ka isa yiwa kanka komai "momy tace" cike da takaicin halin da takeciki, komawa tayi cikin bedroom ta sami Khadija ta zuba uban tagumi girgiza kai momy tayi daganan tace"kitashi kibi mijinki ,Kadija ce ta dubi fuskar momy tace"momy maiya faru naga kamar kuka kikayi ?cikin sasanyar murya momy tace "ba kuka nayi ba kwai raina ne ya 6aci ,adu'a Khadija tayiwa momy daganan ta d'auko mayafinta ta fice, bata sami kowa 'a parlorn ba hakan yabata damar wucewa parking spice da sauri jin anata kiraye _kirayen sallah magrib yasa ta k'walawa drivern daya kawota kira jin shiru bai zoba yasa fara jin haushi tafara cewa kodai'in kar6o keyn mota ta ne?komawa tayi tace" momy bani mukullin motar da dady 'yasiyamin 'nabaki ajiya ,momy ce tace"ina mijinnaki yayi ?"cewa tayi ya tafi wlh kuma driver ba banganshi ba ,d'auko mata momy tayi daganan tayiwa momy sallama ta wuce mota . Ganin motar a lulu6e yasata yayewa ta shige da bismillah ta fita daga cikin gidan tahau titi ,tafiya takeyi cike da kulawa har Allah yakawota gida lpy, da saukarta ne taga Humaid bai dawo ba hamdala tayi daganan ta wuce kitchen ta d'ebo kayan shayi duka har indomie kwali biyu ta d'ibo kwai kuma ciko kwali tayi kasancewar yafi k'arfin abin d'ora k'wan a cewarta tadena fita mancewa tayi bata d'auko abin girki ba zuwa tayi tana tunanin da gas da electri wane zata d'auka ,kinkimo gas tayi tana cikin tafiya ne taji alamun dawowar Humaid ,cikin azama ta ruga dashi d'aki tana nishi ,ta rufe k'ofar da key. Yana shigowa da sallama 'a bakinshi ya doshi k'ofar d'akin Khadija jin ta rufe k'ofar ne yasashi k'wafa yace"wallahi tunda kikaje kika had'ani da momy na wallahi saina miki jina jina ,tana daga d'aki tana yimai gwalo haka yagama sababin shi ya fice ,yayi d'akinshi". Bayan Khadija tayi sallah taji wata fitinanniyar yunwa na mata sallama mik'ewa tayi ta kuna gas duba tukunyar dazata d'ora ruwan zafi tayi bata gani ba zaro ido tayi tana salati tace yanzu ni mezanci d'anyan k'wai kokuma d'anyar indomie kokuma lifton zanci? babu madara babu sugar ?wayo Allah na nashiga uku ni LADIDI!!.tasa indomie a gaba tayi ta farke leda d'aya tanaci tanashan ruwa kasancewar lemu ya k'are a d'akinta bayan tagama cine tayi ,isha 'I daganan ta haye gado bayan tayi addu'oin dasuka zamemata wajibi ta kwanta badan ta k'oshi ba , asbha ta gari. Washe gari bayan tayi sallahi ta mik'e tanason fita tanajin tsoro ,shiko gogan tunda yadawo daga masallaci ya zauna ' a parlor ya kunna TV kuma yaune komawar shi gurin aiki wato hospital d'inshi dan tun dare ake ta yimai waya'akan anason ganinshi ,shi burin shi bai wuce yaga ya illata Khadija ba ,ita kuma Khadija tak'i fitowa saboda tsoron Humaid ,gajiya yayi da zama duba 'agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunshi yayi ,k'arfe goma da rabi 10:30 bai fita ba duk akan wanan shegiyar yarinyar?"yake tambayar kanshi tsaki yaja ya fice zuwa bedroom d'inshi wanka yayi yana fitowa yaga har sha d'aya tayi 11:am zaro ido yayi ,kamar maijin kashi ,shiri yakeyi jikin gaggawa kamar mai tashi sama da sauri yayi

Table of Contents

Chapters

32 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32