Skip to content

Chapter 18

Chapter 18

Ladidin Kauye Book 1 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
Download Book

ba yanada bak'in gashi dakuma gashin baki wanda yafito da tsananin kyawunshi ,kallon Humaid yakeyi kallon a ina nata6a ganinka Humaid ne yace ”aslamu alaikum mutuminne ya mik'awa Humaid hannu cankuma mutumin yace”naso nasanka koba kaine Humaid Abdullahi ba ?gingina kai Humaid yayi yace ”nine nima kamar nata6a ganinka 'a lokacin da zamu bud'e hospital d'inmu ,tunani mutumin yayi cankuma yace”ai dadynka abokina ne sosai kuma yayimin bayanin komai toya jikinnaka dasauk'i Humaid yace ”daganan yafara yimai tambayoyi." Doctor d'inne yakai dubanshi ga Khadija yace” wanan iyalinka ce? a'a Humaid yace”. K'anwata ce OK doctor yace ” please zaki iya bamu guri akwai wata magana danakeso muyi maganar ta doki Khadija to kwai tace tafice daga office d'in ,tasami guri ta zauna tana zuba uban tagumi ✍️✍️✍️. Mom Islam ce *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 33_34 _____Zuciyarta na k'una tarasa maike yimata dad'i amma babu komai ,doctor ne yakai dubanshi ga Humaid yace” yakamata kasani akwai aikin dazamuyi maka kuma yana buk'atar nutsuwarka gaskiya ko kanada mata saidai tayi hak'uri har na tsawo one month kasancewar aikin 'na buk'atar kulawa ,cikin farinciki Humaid yace” doctor ashe zan warke daganan suka fito doctor yanunamai d'akin dazai shiga ,batare da yayiwa Khadija magana ba yashige d'akin yana murmushi 'itako Khadija dataga batada muhimmanci yasata komawa masaukin su zama tayi tadinga rusa kuka kamar wace akayiwa mutuwa ,had'a kayanta tashiga yi tana surutai da alamu ranta ya 6aci sosai ATM d'inshi ta d'auka ta d'auki jakarta tayi waje ,rasa ina zatayi tayi zuciyarta ce take cemata ki koma Nigeria kawai ,hakan ko akayi ta d'auki shawarar zuciyar ta ,mutumin dake jigila dasu wato Joseph shi ta kirawo a waya tacemai dan Allah yazo ya kaita airport ,cemata yayi aisu alhaji suna hanya mezatai a Nigeria ,cikin zak'uwa tace ” fils na maganin Humaid aka manta kuma dole saidasu za'ayimai aikin , cemata yayi to bari yakirawo y'an airport d'in yaji ko jirgin 'Nigeria ya tashi, to tacemai dan burinta taganta 'a k'asarta yana kira yacemata nanda 30 minutes sasu tashi ,cikin hanzari taje ta tarkato kayaanta tafito ta kullo d'akin ,barin keys d'in tayi a hotel d'in suka wuce filin jirgi 'itada Joseph ,lokacin da suka isa 'ana kiran Nigeria dagudu tashige kasancewar yanzu harkar Bank akeyi tabiya kud'in komai . Duba lokaci tayi a ’agogon dake d'aure a hannunta k'arfe 10:23am jin jirgin zai tashi yasata yin adu'a can kuma taji hawaye tafara cewa kuyi hak'uri momy ba'asan raina nadawo ba 'amma babu inda na iya saboda bak'incikin da Humaid ke k'unsamin bayan wasu mintuna ta jirgi ya sauka murna dakuma danasani fall cikin Khadija saboda tana ganin kamar batayiwa su momy adalci ba ,tana sauka tacire sim card d'inta tasai wani wanan kuma tasa 'a jakarta direct gidansu ta wuce wato gidan Humaid ganin mai gadi nanan yasata farinciki nocking tayi had'e da sallama cikin gaggawa mai gadin ya bud'e mata yana cewa hajiya sannunku da dawowa ywwa tace”tashige ciki mai gadin mamaki yafara to ina Humaid d'in??tabb 'bashida mai bashi amsa yasa shi yin shiru, da k'atuwar jaka tafito saboda ta d'ibo kayan abinci su katan d'in indomie dakuma su Maggi star da mangyad'a duka ta loda 'a jakar ,mai gadi naganinta da d'irmemiyar jaka yasashi zaro ido amma babu batun magana ,ficewa tayi batare datace ga inada zataje ba , bank taje taciro kud'i masu ywwa daganan ta dawo gida ,maida jakar tayi tana haki . *ACAN INDIA*? Tunda momy suka sauka take gwada number Khadija shiru a kashe ,dady ne yakira Joseph yace”yakaisu hotel d'in da Khadija suka kama d'aki acan ,Joseph da jikinshi yafara sanyi yacewa su dady wanan madam d'in yau tatafi Nigeria, what!!! Dady 'yace”cikin kid'ima ya 'akayi hakan tafaru maikuma yafaru momy da batada wuyar kuka tace”wallahi Humaid ne sanadi dama ba sonta yakeyi ba shine ko rayuwarta ta salwanta bashida matsala ko tana kuka tana magana ,dady ne yace” Joseph muwuce hospital d'in kawai ,mota suka shige suka nufi asibitin da isarsu sunyi sa'a wanan doctorn yanan office d'inshi suka wuce bayan sun gaisa ne sukace ya mara lafiyar yake dasauk'i doctor yabasu amma tare da shada musu d'azu akayi aikin kuma 'akwai alamun nasara masha Allah sukace yanzu ina yake?doctor ne yace” yana room 3 , amma naga bank'ara ganin sister nashi dasukazo d'azu ba ,lokacinne momy tace”matarshi ce doctor ne yace”amma shine yacemin ba iyalinshi ba ,dadyne ya mik'e suka fito dasu momy dakuma doctor room d'in aka nuna musu suka shige." Ganinshi kwance yana bacci yasa dady dka mai tsawa yace ”ina kakai Khadija?? "arazane ya tashi yace”dady 'yaushe kuka iso ?babu wanda ya kulashi dan haka yayi shiru ,can kuma yace”ai takoma hotel ,dady dayaga Humaid nason raina masa hankali yace ”hotel d'in ubanka !!!... Momy ce tace ”nidai yanzu damuwata number Khadija kuma gashi a kashe kiran number Jalal sukayi yana gurin aiki yace”bai gantaba rasa yazasuyi sukayi saboda halin marainiyar Allah, ... Haka sukayi kwana uku a daddafe duk a tunaninsu Khadija tana gidanta ,a kwana na biyar ne aka sallame su kasancewar Humaid yaji sauk'i sosai gobe zasu dawo Nigeria tunda suka koma hotel d'in Humaid yashiga damuwa dan yasan indai ba'aga Khadija ba to shima ya 6ata dan wallahi saisu momy suncimai mutunci fiyeda tunani, washe sukayi shrin zuwa Nigeria ,jirgin safe sukabi . *NIGERIA* Sun sauka lafiya daga saukarsu gidan Humaid suka wuce maigadi ne yace”hajiya fa jiya tabar gidannan saboda naga ta loda kaya 'a wata k'atuwar jaka tashiga motar ta ko magana batayiba ta shige ,momy ce tazaro ido tace”yanzu fargabar da Khadija take jefamu yayi kenan ?" Dady cikin k'unar 'rai yace”kai kuzo muwuce duk inda zataje taje zamatadawo da k'afarta momy na kuka tana kiran sunan Khadija gashi wayarta bata shiga ,Humaid kam yakasa magana dan yasan kad'an suke jira sufara balbaleshi da masifa 'a motar Humaid suka wuce can anguwarsu momy suna sauka Jalal na shigowa yana ganinsu yace”ina Khadija fa momy ce tashige ciki da 'alamu kukanne zai ku6ce mata shikuwa dady cewa yayi ta 6ata ,Jalal daya tsaya kamar gunki yarasa takamai man amsa yace ”to nikam yaya Humaid ina Khadija? "wani mugun kallo Humaid yayiwa Jalal daganan yashige ciki. Damuwa iya damuwa sun shiga sosai amma shi Humaid bai damu sosai ba kasancewar ba damuwarshi bace ,dady dayaga abin babba ne dan yau da dawowarsu kwana uku yacewa su momy su shirya suje k'auye ko tana can ,momy batayi wata kwaliya sosai ba ta fito suka wuce itada dady ... Da isarsu malam Adamu yafara yimusu lale marhabun shigewa gidan sukayi suka sami 'inna tana zaune tayi k'wad'on rama ,zubo musu tayi aka kawo musu ruwa mai sanyi na randar k'asa ,malam Adamu ne yace”ina zuwa can anjima saigashi yadawo da k'waryar fura da nono dakuma ludaya ,zuzubawa su momy akayi bayan sunci sun k'oshi sukace dama 'abinda yakawomu shine mund'auka Khadija tazo nanne?"inna dake cin rama tace”walhi rabona da ita tunda 'akayi bikinsu nikam mukuma bamu k'ara wai wayarku ba malam Adamu ne yace”to yar marainiyar Allah ina tashiga momy ce tace”har wayarta sun gwada amma 'a kashe ,shirin komawa

Table of Contents

Chapters

32 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32