Skip to content

Chapter 25

Chapter 25

Ladidin Kauye Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

tayo kitchen d'in da sauri tana cewa kufa y'an gayu inzakuyi girki bakwa gayya dariya khadija tasa tace ”to a wanan girkin menene abin wahala ?Sahura ce tace ”walhi ku kula saboda ance yawan ciye _ciyen kayan dad'i nasa ka mance da lahira Khadija dai bata kulata ba sai aikinta takeyi ,Sahura ce taga bread a saman fridge tsalle tayi ta d'auko ta yaga tace ”oh sai natuna lokacin da kike cutar mutane ki gudu amma yanzu ana yimiki magana ma sai kinyi ra'ayi ,hmm kawai khadija tace ”sbda hankalinta na kan girkinta." Khadija ce ta dubi sahura tace ”to muje muyi sallah sai muci abinci ko ?Sahura ce ta yago bread tace ”tabb inma zaki zubo abinci ki zubo dan ni wata shegiyar yunwa nakeji yasin khadija ce tace ”zan zuba miki naki nikam zanyi sallah , tunda khadija ta zubo abinci Sahura ke had'iyar yawu tana lashe baki ,khadija ce ta mik'a mata tare da wani soyayyan nama a kai Sahura ce tace ”ke bakida wayo nikam kawo naman injishi a hannuna kar azo ba'a sawa inna ba tace saitaci ,khadija kam wucewa tayi tabarta a gurin tana tura nama cikin aljihun wando, bayan sun kammalah cin abincin khadija ta kwashe takai kitchen saida ta wanke sanan ta fito ,inna ce ta mik'o wa khadija wani k'ullin buhu tace ”lalle ne da barkono da kuma citta godiya khadija tayi sosai daganan inna tace ”zasu wuce Sahura da ido yai ja tace ”nifa inna kitafi walahi bazan koma k'auye ba kicewa babanmu sai yazo aurena ,dariya suka sa khadija ce tace ”to kizaune in kikayi sati biyu ko uku saiki koma ,tsalle sahura ta doka ta cakumi khadija tana murna ,inna ce tace ”to anta6a yanke hukunci babu mai gida khadija ce tace ai ya Humaid bashida matsala, haka inna ta tafi tabar Sahura ." Washe gari Sahura ce gaban TV tana kallo a MBC action wani film suke yi mai fad'a suna cikin fadanne wani ya kaiwa dan uwansa naushi Sahura ce ta doka tsalle ta kaiwa khadija naushi har tana neman k'ara mata ,a razane khadija ta dago tana kallon Sahura da hankalinta ya tafi ga TV nuno gurin kuka 'akayi aifa ta zauna tadinga kuka harda gumi ,khadija ce ta tashi ta kashe TV n sallamar humaid sukaji Sahura ce ta dubi humaid tace ”barka mijin ta jikin t b juyiwa yai yace ”to waye ta jikin t b ?kallon khadija data had'e rai tayi tace ”to ai naga yan gayu idan mijinsu ya dawo fara'a sukeyi kekuwa kin wani had'e rai kamar dillaliya anzo cin bahi lolz ,wani mugun kallo khadija ta jefeta dashi shikuma humaid na kallonta baice komai ba ya *LADIDIN KAUYE* funny & love story 47_48 Ganin abin zuba sharar gidan ya cika mai zuwa kwashewa bai zoba yasata d'auka ta nufi wani guri tafiya takeyi tana dube dube a uban kwandon zuba shara a kanta ,hango wani k'aton kare tayi yana shirin dosota jikinshi duk gashi cikin tsoro tafara gudu aikuwa kare yadinga binta duk inda ta shiga saiya bita gudu takeyi da kwandon shara a kanta ,tama manta layin dazata dosa gashi gidajen duk kusan kala d'aya wani mutumi ta hango yana gyra parking din motarshi k'arawa tayi da gudu tace ”dan Allah ka temakeni karya halakani ,mutumin ne ya kalli karen yace ”mai tayi ma kake binta ?itako Sahura ganin yana neman raina mata hankali tace ”shi mutumne dazaka tsaya tuhumarshi ko kaima mugune irin karen ,mutumin ne ya rike baki tana salati cewa karen yayi duk inda tashiga kabita karka raga mata." Aikuwa kare yafara bin Sahura gudu take ci babu mai temakon ta ,humaid ne tafe a cikin mota hango ta yai tana gudu ashe harta zo anguwar takuma juyawa yanzukuma ta dawo duk bata sani ba ,fitowa yai daga cikin motar yana cewa keee!!da k'arfi ziwa tayi ta cakumeshi tana ihu ,karen humaid yabawa hak'uri daganan yace ”to ga gidan nan amma ina zaki da kwandon shara cewa tayi naje zubar muku da shara shine kare ya biyoni wata shu'umar dariya humaid yasa yace to jeki gida maganin mai yawo kenan ,murgud'a mai baki tayi ta shige ciki , tana shiga tafara cewa Ladidi ki fito yau nakusa mutuwa ,da sauri Khadija ta fito tana cemata na k'arshe karki sake cemin ladidi ,to natuba dan kunga ku yan gayu ne shine kikeso kisa a maidani gida to ta Allah ba takiba ta shige d'akin da yake mazaunin nata." Washe gari salamar momy ce ta karad'e harabar gidan da gudu khadija ta fice tana oyoyo momy a tare suka shigo parlor rik'e da hannun juna ,Sahura na zaune tana kallo tace ”hajiya barka da zuwa momy ce tace ”yww daughter yar aiki kika samu ne ¿khadija ce tasa dariya tace ”tare sukazo da inna hauwa ,oh momy tace ”na tuna ai ta fad'a min amma bbu wani matsala kho eh momy komai normal , nan momy ta jata zuwa bedroom d'inta tanata bugar cikinta 'akan ko tana cikin wata damuwa ,juyin duniya khadija tak'i fad'awa momy komai,momy ce ta fiddo da wani turare tace ”yau d'inan 'nakeso kiyi using dashi ,to Khadija tace ba tare data musa ba ,nasihoyi momy tayi mata akan ladabi dakuma hak'urin zaman aure,momy ce ta d'au jakarta tana shirin tafiya narai _narai Khadija tayi da fuska zatayi kuka momy tace ”nazo kuma dan inganki inji dad'i shine zakiyi kuka kull kiyi hak'uri zaman aure ba wasa ba ,raka momy tayi har gurin motar da tazo sukayi sallama ,magrib nayi tayi wanka tasa riga da wando rigar dai _dai cinya wandon kuma dai _dai gwuaiwar k'afarta ,turaren da momy ta bata ta fito dashi shafawa tayi a fuska tana mai jin k'amshin yayi mata dad'i ,,jin sallamar Humaid yasata fitowa a kunyace tace ”barka da dawowa yaya uhm barka yace yana k'are mata kallo ,wani lamari yakeji mai wuyar fasarawa sabda inya kalli fuskarta ,cewa yai kaimin bag d'innan ciki ohk tace ”ta wuce taje kaiwa ,tana shirin fitowa taga an kashe light d'in d'akin anbar kadan zaro ido tayi lokaci guda kuma tsoro ya baiyana a fuskarta ,cikin zuciyar shi yana cewa da nace sai lokacin da kika amince to yau na soke wlhi ,nufota yakeyi tana ja da baya ,a haka har tasamu tayi d'akinta da gudu ,6acin rai ne ya dirarwa Humaid sabda yafara wani tunani daban akan Khadija yafara zarginta sosai sabda had'in kan datak'i bashi tana nufin Allah bazai kamata da laifi ba kenan?takoma kamar jahila wacce batayi karatun islama ba ,yau dai 6acin rai yasa Humaid maganganu marasa kan gado juyi yakeyi yana tunanin anya wani bai rigashi ba hmm ." Yaune Sahura zata koma gida sai kuka takeci kamar an aikota wai zatayi kewar burodi da shayi ga kayan dad'i harda bubuga k'afa ,a haka suka had'a mata goma ta arziki akwati sabo Humaid ya siya mata hardasu atamfofi driver akasa ya kaita. Khadija batada wal walah kwata ²komai cikin sanyin jiki takeyi gashi ta koma very silent abin haushi ma dariya tsada takeyi mata ,washe gari da safe kira ya shigo wa Humaid cewar wanan doctorn yanason suyi wani aiki tare urgent yaje ya sanar dasu momy fatan alkairi sukayimai sanan sukace to matarka fa

Table of Contents

Chapters

32 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32