Skip to content

Chapter 11

Chapter 11

Ladidin Kauye Book 1 Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

Momy da takejin farinciki tashigo da turare a hannunta ta fesawa Ladidi takuma fesawa Humaid sega y'an uwan momy nan sun shigo suna gud'a.....✍️✍️ Mom Islam ce✍️✍️✍️ *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 19_20 _____wata kakar su Humaid ce ta shigo tana sanye da wata tsaleliyar atamfa, daka ganta kasan nera tayi kuka sawa tayi aka kirawo Ladidi ,Ladidi tana kuka 'aka shigo da ita ,lokacin ta canza kaya 'atamfa ce Holland me tsadar gaske ,riga da skirt ne mai adon stone a jiki ,tunda 'aka fito da ita take kuka mai cin rai y'an uwan momy ne suka rik'ota suka wuce da ita part d'in momy, lulu6eta naga 'anyi daganan kuma 'aka d'auko turaruka masu k'amshi aka fara fesa mata sosai take jin zafin rabuwar ta da iyayen ta gashi kuma yanzu wanda sha'awar ta yakeyi shi za'a 'aura mata kuma tsanan ta kukan tayi saboda zuciyar ta d'aci take yimata , jiyo muryar mutane suna rangad'a gud'a yasata dawowa daga duniyar tunanin da ta tafi, momy ce ta janyo ta jikin ta kana tace" Khadija duk abinda zance na fad'a miki tun jiya , sai dai zan kuma yimiki tuni da ki rik'e mijinki da 'amana kuma kiyi biyayya 'a gareshi kibi duk wani abu da yakeso inhar bai sa6awa shari'a ba ,wani kukan 'ne yakuma ku6uce mata saboda wanan nasihar ba k'aramin shigar ta sukayi ba ." Bayan momy ta share hawayen da suka zubo mata tace"wa wasu mata da 'alamu k'annen ta ne tace"musu su raka Khadija d'akin dadyn su , k'afar momy Ladidi ta rik'e tana kuka mai tsuma zuciya ,kowa na gurin saida ya zubda hawaye saboda tausayi, bayan sun kaita d'akin dady ne yafara yimata nasiha bayan wa inda suka rakota sun kauce yafara sanya mata 'albarka daganan yafara da ina 'alfahari dake Khadija kibi mijinki karkiyi k'ok'arin sa6a mai kuma yakamata kisani karki kasance mai d'aga murya 'akan ta mijinki kibi umarnin mijinki , karki sa6a masa indai umarnin bai sa6awa addinin musulunci ba ,kanta 'a k'asa tace Dady nagode ,wani small box Dady 'ya d'auko wasu keys ne na mota ,mik'awa Khadija yayi duk da 6acin ran datake ciki saida ta dara saboda tsabar farinciki har k'yal k'yalewa da dariya take,hak'ik'a dady 'yaji matuk'ar farinciki tare dakuma sanya mata 'albarka,kira yayi akan azo a tafi da Khadija ba'adau wani long time ba saiga wasu mata nan suka d'agota kiran sunan dady takeyi amma inna shima baiyi magana ba ,hawayen da suka zubo mai yashere batare da kowa yagani ba ." Humaid ne zaune a d'akin abokanan shi yana hutawa ,wani abokin shine yace "abokina wallahi ka huta saboda wanan babyn taka tagama had'a maka komai ,Humaid ne ya gyara zama yana kallon abokin 'nashi yace" banason irin wanan wasan, daga nan ya gyara zama ,jiyo k'arar wayar shi ne yasa shi duba gurin da ya 'ajiye wayar ,ganin 'number babu suna yasa shi jinkirta d'aukar wayar ,saida 'akayi 6 miss call sanan ya d'auka ,jin muryar wani yasa shi gyara zama k'irjinshi na dukan uku_ uku,ji nayi yace"what!!!. " Wata razana nniyar k'ara yasa yana cewa no_no wlh ba ita bace kana ya mik'e yana layi ,abokin 'nashi yace "Humaid akwai problem ne ?" idan Humaid da ya sauya launi ya juyo yace"babu komai zan dawo anjima,abokin baiji dad'in jin hakan ba 'amma sanin halin Humaid yasa shi yin shiru da bakinshi. Bayan Humaid ya isa gida ne ya hango Khadija ita da k'anwar momy suna magana ,wata muguwar tsanar ta yakeji acikin ranshi, wucewa part d'inshi yayi ba tare da k'ara kallon gurin da 'amaryar tashi take ba?"direct parlorn dady 'ya nufa kafin ya shiga saida ya tsaya sosai yana tunanin kalmar dazai fad'awa dady ,ganin bashiga mafita yasa shi, shigrwa kai tsaye ,bayan yayi sallama ne yasami dady zaune da laptop a hannun shi ,dady ne ya cire farin glass d'in da yake manne a idonshi kana ya juya ya kalli d'an 'nashi ,kan Humaid na k'asa saboda bayason su had'a ido da dady ,bayan sun gaisa ne dady 'yake cemai lafiya ko naga kayi shiru ?"dady ne ya d'ago kai ganin mood d'in Humaid ya sauya sosai yasashi cewa to me kuma ya faru ?idanun Humaid sunk'ara kad'awa ya d'ago kai yana duban dady 'yace"dady dan Allah dan darajar manzon Allah ka fahimceni ,dady dai baisan inda Humaid ya dosa ba saboda babu abinda ya fahimta ,Humaid ne yace"dady nafasa auran Khadija!!!,sauran kalmar ta mak'ale a bakin shi ganin wani mugun kallo da ,dady ke jifanshi dashi." Dady da yakejin ranshi yana yimai d'aci ya dubi Humaid 'da jikin shi ke rawa yace"wallahi wallahi ko bayan raina ban yarda 'ace ka fasa 'auran Khadija ba ,da ubanwa yasa kace" kana sonta, kodan kanaso ka wulak'anta mu ?"girgiza kai Humaid yayi saboda yana ganin dady bazai fahimceshi ba ,dady ne yace"tashi ka ficemin marar kunya da bakasan mutunci ba ni zakazo kacewa wai kafasa 'auran Khadija to dama gobe juma'a 'aure babu fashi wallahi sai anyi ,Humaid ne yayi saurin ficewa daga part d'in dady saboda kar momy tasan halin da 'ake ciki ,komawa bedroom d'inshi yayi ya hau makeken gadonshi juyi yakeyi saboda zuciyar shi ji yakeyi kamar zata fashe , yafara tuno kalar tanadin da yace"zai yiwa Khadija 'amma yanzu gashi komai ya rushe ,yafara kuka kamar k'aramin yaro ,sai kuma ya tuno cewa gobe nefa d'aurin aure dafe kanshi da yake faman ciwo yayi yana salati ,akwatin shi da yacika shi da d'inkuna ya kalla saboda kayak shiki zasukai kala talatin amma gashi komai ya rruguje." Khadija ce zaune kusa da umma tana k'ara tunatar da ita 'akan zaman lafiya dakuma ibada da hak'uri ,wata gora babba momy ta d'auko tabawa Khadija tace"kinga wanan daga saudiya 'aka kawo min kuma dan ke nasa'aka taho dashi saboda ba ,a ko ina 'ake samunshi ba , ita dai Ladidi ta kasa gane me momy take nufi ,momy ce ta dubi Ladidi kana tace"zuma ce ta mata kullum zakidinga sha 'amma fa yanada k'arfi,2 small spoon zaki dinga sha ,Ladidi ce take mamakin momy da take zayyane mata maganin mata." 💍 *WEEDING*💍 Yau juma'a yaune dubban jama'a suka shaida daura auran *KHADIJA MUSA DA HUMAID ADAM* Akan sadaki dubu d'ari lakadan ba 'ajalan ba 'abokanan su Humaid basu ji dad'in ganin yanayin angon ba kasan cewar baya cikin 'nutsuwar shi saboda 'a inda yake basu labarin shagalin da zasuyi a gun bikin dakuma garar daze kwasa 'amma sunga yanzu ko sunan amaryar baya son ji ." Kowa ka gan yana cikin farinciki a yau saboda biki yayi biki amma banda mutum biyu wato Khadija da Humaid , wata k'awar Khadija ce tace yakamata mu tambayi Humaid saboda musan a inda za 'ayi dinner Khadija ce tace"hmm kuna iya zuwa bazan hanaku ba ,babbar k'awar ce mai suna ramsy ta d'aga waya tana lalubar number Humaid 'dan kab k'awayen sunfi shiri sosai ,jin takira wayar tanata ringing ba'a d'aga ba yasata dad'a gwa dawa cikin k'araji yace" wai waye ne please banason takura ,Ramsy ce tace"Humaid baka ganin 'number tane nice fa ,Humaid ne yace"to inna

Table of Contents

Chapters

32 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32