Skip to content

Chapter 24

Chapter 24

Ladidin Kauye Book 1 Complete Hausa Novel 1,191 words 0 views Progress saved
Download Book

yana jira yace ”tafito ,momy ce tace ”ya kara mata one week 'komawa d'aki yayi yana kuka hhh manya, washe gari kuwa ko sallama baiyi musu ba Yakoma can gidan ganin Sabin gyaran da dady 'yasa 'ayi yasashi farinciki.... Yana 'alfahari da iyayenshi sosai da sosai adu'oi yadiga kwararo musu ,yana cikin hakanne yaji ana nocking zuwa yayi bud'e k'ofar yana budewa yaga khairat ce ,tsaki yaja ,cikin k'ufula yace ”mekuma kikazoyi gidana ?"tsaki taja tace ”naje na zubar da cikin kuma yanzu takarda ta nake jira ,cikin sauri yayo kanta ,kome ya tuna ya fasa ,cikin azama tace ”wallahi daka doka hmm kabani takaddata in ficema daga gida ,domin wanan ai bak'inciki ne ace mutane na sonka insunji da igiyar aure a tsakani saisu gudu mtsw ,humaid ne yaje ya d'auko takadda ya rubuta mata 'abinda ta buk'ata ,godiya tayiwa 'Allah daganan ta fice ,shikam ko damuwa baiyi ba tunda Khadijanshi zata haifamai y'ay'a ... Sati ya cika yaune ake shirye shiryen komawar khadija ,humaid ne yakoma gun doctor Umar akan ak'ara dubashi ,congrat yayimai yana dariya yace ”aci amarci lafiya yanzu kazama normal fa ,dariya humaid yayi yace ”nikam tun yau na d'auki hutu sai wata biyar dariya sukasa ,daganan yawuce gida zuwa d'auko gimbiya khadija ,tana kukan rabuwa da momy ,yashigo momy ce tace ”ka kula min da yarinya dan Allah ,insha humaid yace ”daganan momy ta rakata zuwa mota ,tuk'i yakeyi a hankali ,har Allah ya kawosu gida lafiya tana sauka zata fito ya ,sunkuceta ya goyata ya direta 'a k'ayataccen d'akinta ,ammafa d'akin yayi kyau ,tafad'a cikin zuciyarta ,humaid ne yace ”lovely dan zaki biyoni shine harda kuka ?"murmishi tayi ta nemi gefen gado ta zauna ,soyayya 'kuwa humaid ba bayaba dan jin k hadija yakeyi inta k'ara guduwa bazata dawoba*LADIDIN KAUYE* Funny & love story 45 _46 Zai iya rasa rayuwar shi lalla6ata yakeyi akan taci kaza 'amma sai wani sharewa takeyi murmishi ne ya su6ucewa Humaid cikin zuciyar shi yace ”kamar ba ita bace kwad'a yayyar kaza ba ,haka yadinga bata 'a baki tana ci tana yanga suna gama ci yace ”taso muje muyi sallah dan nuna godiya ga Allah ,a gajiye take amma batada za6i dole ta mik'e sukaje yin alwalah ,suna idarwa ne yazo yaja musu sallah raka'a biyu sukayi yai sallama bayan sunyi adu'oi masu yawa , ya d'ora hannu a kanta yana yimata 'adu'a ,suna kammalawa ya mik'e ya nufi bedroom d'inshi sleeping dress yaje ya sako ita kuma lokacin tsabar gajiya kwanciya tayi da kayan jikinta ,Humaid bai kulata ba yaja filo ya kwanta 'acan gefe ." Washe gari bayan tayi sallah ta duba bataga Humaid ba ,jin alamun shigowarshi yasata durk'usawa har k'asa tace ”barka da safiya yaya ,yww barka dai amaryar yaya ,da 'alamu baki damu da yayan naki ba ko ¿sunkuyar da kai k'asa tayi tana wasa da fingers d'inta surarta yai yace ”zomuje mu kwanta bacci nakeji please ya marai raice kamar yaro ,dariya yaso bata tace ”gaskiya not ni yanzu bazan kwanta ba buh wlh wanka zanyi tana magana kamar zatayi kuka Humaid ne ya shige ya barta 'a gurin ,juyi yakeyi baccin ma yak'i d'aukarshi tunani ya fara ,ina murna farinciki na ta dawo ashe akwai problems a gaba oh god Allah kadawo min da Khady kan hanya ." Breakfast ta had'a musu mai rai da lafiya chips ne na dankalin turawa sau wainar k'wai dakuma tea mai kauri wanda yaji kayan kamshi ,dining room ta wuce dashi kasancewar ankuma gyara gidan ,tana fitowa ta koma kitchen kayan data 6ata ta wanke ta rufo kitchen d'in ,tsintsiya ta d'auko tafara share parlorn tanayi tana hutawa 'a haka ta gama mopping d'in tayi daganan ta kuna turaren wuta ,wani sihirtaccen k'amshi ke tashi a gidan ,bedroom d'inta ta shige ta cire kaya ta d'aura towel ta shiga wanka ,ta dad'e tana wanka da sabulun da momy ta bata mai kamshi tana fitowa ta ciro kayanta , gaban dressing mirror ta zauna simple makeup tayi ammafa ta had'u atamfar ta d'auko mai ratsin wait and black tayi d'auri mai kyau ,kin shiga bedroom d'in Humaid tayi can kuma ta shige da sallama tana cewa yaya Humaid katashi breakfast is ready ohk yace ”dagan ya mirgino yana yimata wani kallo cikin sigar wasa yace ”ke bakisan inda ake tashin miji daga bacci bane ¿" am sorry tace "daganan ta fice, brush yaje yayi daganan yai wanka ya shafa manshi man kamshi ya fito sanye da shadda pink sai d'aukar ido takeyi ,murmishi ya sakarwa Khadyja yace ”lovely mai yasa baki kirani nazo na tayaki ba ¿cikin sanyi murya tace ”nagama ai ,janyo gwangwanin madara da ragowar kayan tea yayi saida ya k'ara komai bacin wanda tasa dagan yace ”to bud'e baki naga 'alamun bakison cin abinci sosai ko ¿shiru tayi daganan tafara cin abincin ,kad'an taci tace ta k'oshi." Kallonta Humaid yakeyi yarasa mai yasa yarinyar nan yanz bata sakewa dashi ,duk rashin kunyarta da neman tsokana yanz duk sunyi sanyi ,tunani ya shigayi to aure babu hira ina labari ,duk inda naso naga ta fahimceni amma lamarin ya citura ,mik'ewa yai yace ”lovely biyoni ki kar6i wani abu ,cikin sanyin murya tace ”ya Humaid banajin dad'i ynz kaina nayimin ciwo ,subhanallah to zomuje hospital a'a kabarshi inada maganin a d'aki please zani in kwanta ohk yace ”yarasa mai yaiwa khady take wanan slow d'in ,kodai har yanzun bata sonshi ne kwai tabi umarnin Momy da dady ne ,iska ya fesar mai zafi ya bugi bango yana dogon nazari itako tun tuni ta shige part d'inta." Kwance take tana kallon sama tana tunanin rayuwarta tada 'a cikin gidan hmm da yace ”baya sona yanz kuma yace ”yana sona kai da 'ayar tambaya wlh but naji masoya na cewa in mutum ya k'ika daga frko to karshe koyace yana sonka yai karya , haka ta dinga juyi a bed d'inta tarasa maiyake damunta . Washe gari ai yuka ta gabatar inda tasaba ko ina ta gyareshi gidan sai zuba k'amshi yakeyi ,yau 7 days da auransu ,nocking taji batayi azamar tashi ba saboda Humaid na nan ,ganin gimbiyar bata tashiba yasashi mik'ewa ya bud'e k'ofar ,su inna Hauwa ya gani ita da wata yarinya zatakai 13yrs a duniya sanye take da rigar banba lasta rigada wando sai hijab da yaji jiki ,inna ce tace ”munsha hanya fa khadija najin muryar inna ta mik'e da gudu tana oyoyo ,Humaid ne ya kar6i kayansu ya shige dashi d'akin bak'i yadawo suka gaisa ya fice sbda ana kiran sallah ,khadija ce tace ”inna kunsha hanya ya su baba ,lafiya Lou inna tace ”tana kalle² khadija ce ta dubi wanan yarinya tace ”inna naso in ganeta amma ta 6acemin ,yarinyar ce tace ”uhm ai wanan daular haka dole bazaki ganeni ba to inkin manta nice sahura waro ido khadija tayi tana duban sahura tace ”wai kece kika girma haka ? Sahura ce ta dubi khadija tace ”to ke kinga inda kika koma ne walahi kamar matan turawannan da muke gani a shagon mai shayi na anguwarmu ,dariya sukasa dukansu ,khadija ce ta shige kitchen sbda yimusu girkin lokacin 11am shinkafa jollof mai kifi da carrot dakuma green bean's dataji alaiyahu lokaci k'alilan gidan ya kaure da kamshi sosai ,Sahura ce

Table of Contents

Chapters

32 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32