Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Ladidin Kauye Book 1 Complete Hausa Novel 1,168 words 0 views Progress saved
Download Book

ne ya cire kud'in shi kana yabawa alhaji abdullahi ribar halak d'inshi ne yana juyawa yana karatun boko kan kace me arziki ya hau hawa . Daga nan yafara neman aure Alhajin da ya bud'e mai shago shine yazama uba a garezhi yabashi kyautar gida a ranar alhaji abdullahi yayi ,kuka sosai ,yana fad'in inama iyayenshi na raye da sunga gatan da wadatar dayake ciki . Bayan auran, ne malam adamu ya zo jos ganin ,gidan alhaji abdullahi gidane. Gidane me kyan gaske sedai ba shida girma sosai amaryar tashi me suna Aisha tayiwa malam adamu tar ba me kyau. Bayan y'an watanni Allah ya albar kace su ,da samun cikin Humaid cikin Aisha yasami gata sosai bayan wata ,tara da kwana goma Allah ya albar kacesu da samun k'aruwa kya'kyawan yaro me farin jini ya taso cikin gata da nuna kulawa ,kwatsam tana yaye Humaid se cikin jalal Allah yara bata da cikin lpy anyi hidima sosai tundaga lokacin aihuwa ta,tsaya mata . *_BACK TO STORY*_ Bafula tanin ne ya d'auko jar, kar ,ruwan shi ya shek'a mata duka a jiki ware idanu tayi kana tace ,wai shin idan mutum ya mutu yana dawowa ne bafula tanin ne ya dube ta kana yace tunda kinga yanzu kindawo ba. Shirin muguntar da zata yiwa bafula tanin takeyi sandar ,da ya buga mata ,ta d'auke ta ruga a guje . Shikuwa bafula tani basan gidan su Ladidi ba yaro ne yazo wu cewa kiran shi yayi kana yace kasan gidan su Ladidi¿" yaron ,ne ya d'aga kai ,kana yace babu nisa ai bafula cewa ya yi to don Allah zoka ,rakani . Barin shanun yayi suka nufi gidan su Ldidi yaron,ne ya shige cikin gidan ya diko ya samu tana shara gai sheta yayi kana yace ana sallama da Ladidi yadiko saboda jin dad'in yar tata zata fara zuwa hira ta ce kace gatanan fitowa . Yaron ,ne Yakoma ya gayawa bafula tanin wai gatanan zuwa . Ladidi ce ta fito daga d'akin yadiko tasha kwaliya in kagan,ta kace sabuwar aljana washe hak'ora tayi kana tace yadiko nayi kyau ¿" Yadiko ce ta jin ,jina mata ,kana tafara yimata kira ,ri. Kaga yar gidan yadiko ,washe bakin ta kumayi tana dariya. Lek'awa tayi dan taga me sallamar hango shi tayi ,yana ta dunk'ule hannu kamar me shirin kai naushi . K'ara mai da hanka linta tayi gurin sauraran abin dayake cewa jitayi ya na fad'in wlh tana fitowa zan ,zuba mata naushi . Itako Ladidi jin haka yasa ta koma gida yadiko ce ,tace har kin dawo ¿". A, a Ladidi tace kana ta shige d'an k'aramin d'akin ta ,,ta d'auko sandar bafula tanin ta dawo ta la6e kusa da inda yake zaune seda ta dede,ci ya juya baya ai kuwa ta d'aga sandar ta sheme shi fad'uwa k'asa yayi ita kwa Ladidi gaba ta k'ara ta barshi ,shida sandar shi a gurin yakasa tashi yana ta ihu. Tana cikin tafiya ta ci karo da wasu samari su biyu . Tana ganin su ta ,tuno inda ta, ta6a ganin su Humaid ne shi,da Jalal sun fito kewaye . *LADIDIN ƘAUYE.* _funny & love story._ *_Labari mai ban dariya haɗi da faɗa karwa_* *NA* *ZAINAB HABIB* _{MOM ISLAM}._ *MARUBUCIYAR* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode: 5_6.* ____Humaid yasa shadda fara shi kuma jalal k'ana nan kaya ne a jikin shi Ladidi ce ta rik'e baki shagon da take kusa dashi ta shiga kana tace "dan Allah me manja samin a hannuna me manja ne ya dubeta kana yace "ke baki da hankali ko¿ LADIDI ce ta dubi me manjan kana tace "zaka ga aikin masu hankali roba ta hango a can waje zuwa ta yi ta d'auko robar shidai me manja yana kallon ta be ankara ba ta dumbula robar cikin manja . Me manja da yaga barnar da LADIDI tayi mai mik'ewa yai kana ya nufo ta da niyar kai mata mari. Ya d'aga hanu ze mare ta yaji an wanke mai fuska da manja sakinta yai kana ya nemi gurin zama . LADIDI kuwa ganin haka ta kuma dum bular manjan tayi gaba . Hango su Humaid tayi a gindin wata bishiyar mangoro suna hutawa . A hankali ta tako kana ta zagaya ta bayan su inda bazasu ganta ba saboda bishiyar k'atuwa ce . Juye manjan tayi a rigar Humaid ta baya sunata hira basusan abinda ke faruwa ba a jiye robar tayi a gefe . Hango cinnaku tayi da yawa d'auko biyu tayi tasawa Humaid a dede gurin zaman shi kuma d'auko biyu tayi kana tasawa Jalal a daidai saitin da ya zauna. Tashi tayi taje wani shagon da ake siyarda yar bebi jitayi anata ihu Humaid ta hango yanata tsalle shima jallal d'in tsalle yakeyi a tak'ai ce dai babu me temakon d'an uwansa. Sun rasa inda za suyi aikuwa suka zuba a guje . Kamar mahaukata Jalal ne yace "Humaid wlh bayanka manja . Zaro ido Humaid yayi kana yace "kai k'yaleni bata manja nakeyi ba. Mutane sa kallon su suke ta famanyi, ita kuwa LADIDI barin gurin tayi dan karsu ganeta da k'yar suka gane hanyar gidan malam Adamu saboda zuwansu na biyu kenan . Da gudu su ka shige cikin gidan inna hauwa tanajin an shigo gidan da gudu bata tsaya ganin kosu waye ba itama ta ruga d'akinta da gudu. Su Humaid ne suka shige d'akin da malam ya basu wanan na ihu wancan na ihu se zuwa can anjima ya lafa musu . Humaid ne ya hau tattaro kayansu yana had'awa guri d'aya jalal ne yace "Humaid me zakayi da kayannan . Humaid ne ya kalli jalal kana yace "insha Allah gobe zamu bar wanan k'auyen . Jalal ne ya tuna da gudu da suka dinga kwasa ya kyalkyle da dariya . LADIDI ce ta fito d'auke da tiren tuwo da miya malam adamu ne da malam musa suna zaune suna hira kasa kunne tayi taji suna cewa ai bak'in gidana gobe zasu tafi . Tsalle LADIDI ta buga kana ta je gurin kayan wasan ta kusa da bishiyar kuka . Dakin YADIKKO ta nufa samun YADIKKON tayi tana sallahr isha I . Fitilar d'akin ta d'auko kana ta koma gurin kayan wasan . Farar k'asa ta d'auko taje kan dutse ta dan dak'ashi seda yayi laushi. Ta kwashe shi a leda d'akinta ta nufa mudubi ta samu . Ta lakato mai me yawa ta shafa a fuskarta ta d'auko farar k'asar da tadaka shima ta goga a fuskarta, tunawa tayi ai batasa kwallin ba d'auko kwalkin tayi ta zana baki a bakinta takuma zazzana a duka fuskarta kayanta da suka yayyage ta d'auko . Riga tasa me yagaggen hannu se wandon atamfa shima ta gwuiwa ya yage . Dan k'aramin gyalenta ta d'auko ta kuma nan nad'ashi a kanta . Duk wanda yaga Ladidi to ze d'auka aljana ce saboda ba lallai ka gane taba . YADIKKO ce keta k'wala mata kira amma tana ji taki kulata . Kuma lek'awa kofar gidan nasu ta yi hango su baban ta da malam adamu suna tsaye da alamu baban nata gida ze shigo shikuma malam adamu zashi masallaci ya kwana . Wurga sandar ta tayi kana ta dura ta

Table of Contents

Chapters

32 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32