Chapter 4
Chapter 4
katanga . Tunda tafara tafiya bata had'u da kowa ba ta kusa isa gidan malam adamu ta had'u da wani mutumi me tallan tsire yana ganin ta . Ze ruga da gudu kenan Ladidi ta nunashi da sanda tace "wlh ko ka tsaya ko kuma yanzu inkaika gurin baba ifiritu me tsire yaji za,a kaishi gurin aljani ya dur k'usa har kasa ya ce ku kuke ganin mu ba mu muke ganin kuba dan girman Allah kuyi hakuri LADIDI ce ta zaro jajayen idanuwan ta kana tace "Zamu kyaleka amma da sharad'i me tsire ne yace "kome kukeso zan Baku indai zaku barni da raina da lpy . LADIDI jin hakan ta dubeshi kana tace "tashi ka bud'emin wannan kwanon . Me tsire na rawar jiki yaje ya bude kwanon ya mik'owa LADIDI tsire ne aciki tsinke biyar . Kwashewa ta yi duka ta had'esu guri guda tana tafiya tana ci shikuwa me tsire tunda yaga tayi nisa ya ruga da gudu yabar kwanon a gurin. Kafin ta k'arasa gidan su malam adamu k'arfe 9 tayi kowa ya kwanta suma su jalal sun gaji saboda gudun da suka kwasa d'azu. Taci sa,ar gidan a bud'e yake tunawa tayi da malam adamu a masallaci ze kwana kai tsaye d'akin nashi ta nufa lek'awa tayi ta windown d'akin suna kwnce suna danna waya. Basu ankara ba sukaji durowar mutum da farko hankalinsu be tashi ba seda suka hango farar fuska kamarta aljanu . Dakin nasu babu haske sosai . LADIDI ce taje bakin k'ofar d'akin tasa sak'ata tanata zaro jajayen idanuwan ta . Humaid tunda ya firgita ya koma kusada jakar kayan su ya 6uya shiko jalal dur k'usawa yayi yana bata hakuri . LADIDI ce ta dubi Humaid kana tace "kai bakan manya bako to yau karyarku ta kare . Rik'e hanun juna sukayi suna matsawa da baya da baya Humaid ganin abin yakeyi kamar a mafarki d'ago kan daza suyi suka hango nama a hanunta kurma ihu suka dingayi . Humaid tsabar tsorata fitsari yayi a wando shi kuma jalal yaje yin tusa ya had'o da kashi . Ladidi ce ta lura da abinda sukayi tace "kowannen ku ze kar6i wanan naman yaci Humaid ne yace "Ai Allah yayi kune dan Ku temaki mutane amma kunzo zaku cutar damu . LADIDI ce ta daka musu tsawa kana tace "tunda bazakuci naman ba to Ku cire wandunan Ku kai da kayi fitsari ka tsotse kai kuma me k'aton kai dakayi kashi kaci kad'an . Zaro ido sukayi kana suka fara "dan Allah kuyi hak'uri tsawa takuma daka musu tace Ku za6a yaji ta hango a gefen ta a kulle a leda ajiye musu a gaban su tayi ta finciko nama a tsinken tsiren tace to sekun shanye yajin nan duka . Humaid yana kuka yace Jalal gara musha yajin. Dukufa shan yajin da da d'an guntun naman sukayi idanunsu yayi jajur ga kuka ga shan yaji . Suna tsayawa zata daka musu tsawa inna hauwa ce tajiyo tsawar. Fitowa tsakar gidan tayi bata gane ta ina akeyin tsawar ba seda ta jiyo k'arar bud'e k'ofar d'akin malam adamu wanda su Humaid suke ciki . Kafin ta ankara taji an turo ta d'akin su Humaid juyowar da zatayi suka had'a ido da LADIDI . Inna hauwa ce ta kurma ihu tana salati tana fad'in dama ashe aljana ce tashigo mana gida shine bata k'arasa maganar ba taji LADIDI na rawa . LADIDI ce ta zaro musu ido kana tace rawa zakuyi ina hauwa ce ta zaro ido kana tace "kuyi hakuri kusan mu bil adama bamu da k'arfi . LADIDI ce ta d'aga sandar ta zata buga musu sukasa ihu rawa sukeyi kamar mahaukata inna hauwa ta dage se rawa take kwasa. LADIDI ce tace "jibeku dame k'aton kai dame k'aton hanci. Kekuma yar tsohuwa me k'aton goshi ki k'ara shiga abinda babu ruwanki . Inna hauwa ce ta had'a hanuwan ta biyu tace "kiyi hakuri bazan sake ba . LADIDI ce tace musu "kowa ya rife idanu kuma karku bud'e har senace inkuma ba haka ba to zaku tsinceku a duniyar aljanu . Kafin ta gama ,magana har sun rife ido . Ficewa tayi a d'akin ta nufi d'akin inna hauwa ......✍🏽✍🏽✍🏽. *Mom Islam✍🏽.* *LADIDIN K'AUYE* _Funny & love story._ *_Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa_* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB*. *MARUBUCIYR :* *ZAINABU ABU* *AND* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR _RAHIM* *Episode: 7_8* _____kwanuka tagani wanda akaci abinci wani kwano ta hango a rufe bud'ewa tayi abinda idanunta suka hango ya bata mamaki sosai. K'ara bude ido tayi nama ne soyayye cike a kwanon leda ta hango ta d'ibi iya san ranta ta fice a gidan . Tana fita suka bude ido sunata mamakin aljanar da suka gani . Inna hauwa ce tace "jalal zoka rakani d'aki jalal ne ya zaro ido ya dubi inna hauwa yace "walh inma zaki tafi ki tafi babu inda zani. Inna Hauwa ce tayi a uzubillahi ta ruga d'akinta da gudu . LADIDI ce ta koma gida duk mutanen gidan sunyi bacci lalla6awa tayi ta shige d'akinta ta kwanta babu maganar sallah . Washe gari bayan sallar asbah Humaid ya fito da jakar kayan su ko wanka basu yi ba malam Adamu ne ya dube su kana yace "badai tafiya zakuyi ba da wanan duku dukun safiyar gari be gama haske ba. Jalal ne yace "wlh mun shirya inna hauwa ce ta fito da carbi a hannun ta ,tana lazimi ta ce "malam ai dole suce zasu tafi, malam Adamu ne ya nemi guri ya zauna kana yace "meke faruwa.¿ Humaid ne ya nisa kana yace "wlh malam aljana ce tashigo gidannan jiya da daddare tadin ga yimana mugunta. malam Adamu ne ya jinjina lamarin ya ce to shine dalilin tafiyar Ku da wanan safiyar . Jalal yana gyara takal minshi yace "insha Allah yanzu zamu wuce jos . Ina hauwa ce taje d'auko kwanon da ta zuba soyayyen nama ganin naman ciki befi biyar ba yasa ta rafka salati har su jalal suna rugawa da gudu . Malam Adamu ne ya lek'a d'akin kana yace "meke faruwa ne¿ inna hauwa ce ta dubi malam da alamun damuwa tace "kaga naman da kasiyo wlh ragowarshi kenan malam be nuna dumuwar komai ba yace "karki damu kawo a kai musu . Barinje in siyo musu lemon kwalba ficewa yai . Ba dad'e ba se gashi ya dawo da lemon kwalba guda hud'u . Inna Hauwa ce ta kai musu d'aki suna zaune suna jiran lokacin tafiyar su yayi . Inna Hauwa ce ta mik'a musu had'e " da nama kar6a sukayi ci sukeyi da sauri sauri nan danan suka gama . Fitowa sukayi rataye da jaka a kafad'ar su inna Hauwa ce tayi musu Allah ya tsare. Humaid tsabar ya matsu su tafi harya shige mota Mallam Adamu ne ya fito d'auke da tsaraba a hannun shi bud'e bayan motar Jalal yayi ya shige motar suka d'auki hanya se jos. Washe gari Malam musa ya tashi babu lpy duk iya gigiwar LADIDI seda tayi sanyi ganin jikin mahaifin nata kwance yake se nishi yakeyi kamar me ciwon zuciya YADIKKO da jikinta yagama yin sanyi . Tanaji kamar Malam musa baze tashi ba tari ne
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32